Gabatarwa:
Ciwon mara ga budurwa a lokacin jinin al'ada abu ne da ke yawan damuwar mata musamman matasa 'yan shekara sha huÉ—u (14) zuwa ashirin da biyar (25). Yana da kyau a gane cewa ciwon mara ga budurwa wanda ke zuwa daf da za ta fara jinin al'ada ko bayan ta fara, mafi akasari ba abu ne wanda wata cuta ko rashin lafiya yake kawowa ba.
Wane irin ciwon mara ne ke da alaƙa da jinin al'ada?
Ciwon mara ga budurwa da ke da alaƙa da jinin al'ada shi ne wanda ke zuwa daf da mace za ta fara ganin jinin haila ko da zarar ta fara. Yana zuwa cikin kwana ɗaya ko biyu kamin farawa ko bayan farawa, haka kuma zai daina kamin ta gama ko kuma daga zarar ta gama.
Yana sanya budurwa ko mata rashin walwala da É“acin rai wata rana har su ji kamar sun shiga Æ™unci (mood swings). Haka zalika yana iya zuwa tare da amai ko gudawa ko tashin zuciya ko kasala. Yanayin wannan ciwon mara idan ya fara, yakan taso ya kwanta kamin ya Æ™ara sake sake tasowa[¹].
Abubuwan da ke kawo ciwon mara ga budurwa a lokacin jinin al'ada?
Muhimman abubuwan da ke cikin marar mace su ne mahaifar ta da sauran sassan al'aurar ta. Ciwon mara a lokacin jinin al'ada ko haila yana faruwa ne saboda takura da mahaifa ke yi a lokacin da naman jikin mahaifa yake mammatsewa domin tilasta jijiyoyin jinin dake cikin maihafa su fashe su fara zubo da wannan jinin na haila[¹].
Wannan takurar da mahaifa ke sha a lokacin da namanta ya fara mammatsewa yakan hana ta samun isasshen jini da iska, rashin isashen jini da iska shi ne zai sa mahaifa ta fara fitar da wasu sinadarai na frostaglandins (prostaglandins and bradykinins) wanda su ne musabbabin jin ciwon mara.
Dangane da abubuwan da ke sa ciwon mara a lokacin jinin haila likitoci masu ƙwarewa ta musamman a fannin kula da mata masu ciki da ɗaukacin al'aurar mata (Obstetricians and gynecologists) sun raba ciwon mara a lokacin jinin haila gida biyu (2) kamar haka(2);
1. Ciwon mara ga budurwa a lokacin jinin al'ada kashi na farko - Primary Dysmenorrhoea
Wannan kalan ciwon mara ba abin da ke kawo shi face abin da muka ambata a baya. Shi wannan ciwon baya da alaƙar komai da wata cuta ko rashin lafiya. Kusan ko wace mace za ta ɗanɗane shi a rayuwar ta, sai dai na wasu matan ya fi na wasu.
Irin wannan ciwon mara ya fi tsanani ga mata matasa sababbin fara al'ada 'yan kasa da shekaru ashirin, kuma tsananin shi yana ragewa kaÉ—an-kaÉ—an lokacin da mace take Æ™ara shekaru. Wasu matan ciwon yakan daina baki É—aya bayan sunyi haihuwar farko[²].
2. Ciwon mara ga budurwa a lokacin jinin al'ada kashi na biyu - Secondary Dysmenorrhoea
Wannan ciwon mara shi ne ake alaƙanta shi da wasu cututtuka ko rashin lafiya. Cututtuka da ke kawo irin wannan ciwon sun haɗa da:
1. Endometriosis: Wannan shi ne samun ƙwayar tantanin halittun bangon mahaifa na ciki (endometrium) a wani guri da ba mahaifa ba, musamman cikin kugun mace ko kwankwaso.
2. Adenomyosis: Samun ƙwayar tantanin halittun bangon mahaifa na ciki, a cikin naman mahaifa (bangon mahaifa na tsakiya).Sanyin mara na mata
3. Cutar sanyin mara na mata (PID)
4. Matsewar bakin mahaifa
5. Ciwon dajin mahaifa
Yadda ake maganin ciwon mara a lokacin jinin al'ada
Da farko likita zai yi bincike mai zurfi akan marar lafiyar domin ya tabbatar da wani irin ciwon mara ne. Sannan zai iya aika marar lafiya É—akin gwaji ayi wasu gwaje-gwaje da zasu tabbatar da ce akwai ko babu wata cuta da ta haddasa wannan ciwon(2).
Hanyoyin samun sauki daga ciwon mara a lokacin jinin haila sun haÉ—a da:
1. Gashi da robar ruwan zafi: Gashi da robar ruwan zafi hanya ce mai aiki sosai domin rage raÉ—aÉ—in ciwon da ke zuwa tare da jinin haila. Ita wannan roba ana chika ta ne da ruwa masu É—imi sai a É—ora ta akan mara na É—an wani lokaci.
Akwai roba da ake sa ruwan zafi wadda turawa suka ƙirƙira ta musamman domin wannan aiki ana kiranta hot water bottle, kamar yadda muka gani a wannan hoto dake sama👆.
Amma idan mace ba ta da irinta takan iya samun karamin galan ɗin da babu komai acikinsa (empty gallon) ko gorar roba sai a cika da ruwan zafi a dunƙule shi a towel ko tsumma sannan a ɗora akan mara kamar yanda zamu gani akan wannan hoto da ke a ƙasa👇
3. Rage cin kayan chocolate: Masana sun gano cewa kayan zaki na chocolate musamman masu launin ruwan hanta (brown chocolate) suna tsananta ciwon mara ga budurwa a lokacin jinin al'ada. Saboda haka kiyaye cin wadannan kayan zaki yana taimakawa mata masu fuskantar matsanancin ciwon mara a lokacin jinin al'ada.
A lura cewa, ciwon mara a lokacin jinin al'ada kashi na biyu (wanda ke faruwa sanadiyar wasu cututtuka, kamar yadda muka yi bayani a sama) sai an fara maganin cutar da ta kawo ciwon sannan a haÉ—a da magungunan kashe ciwo. Magungunan da ake amfani dasu sun haÉ—a[³]:
Maimakon wadancan magungunan dake sama, idan mace tanada ulcer zata iya shan waÉ—annan:
Hanyoyin da mace zata kare kanta da ciwon mara a lokacin jinin al'ada.
Duk da haka wasu masana sun É—an yi tsokaci akan wasu abubuwan da kan iya kare mace daga ciwon mara a lokacin jinin al'ada. Abubuwan sune kamar haka(3):
Bayanin rufewa
A taƙaice mun ga cewa ciwon mara abu ne mai damuwar yan mata sosai a cikin al'umma. Kuma mun ga yadda ya rabu gida biyu, kashi na farko shi ne wanda ba a alaƙanta shi da wata cuta, kashi na biyu shi ne wasu cutuka ke haifar wa.
Kana munga cewa ana amfani da magungunan kashe jiki da kuma maganin mefenamic acid, buscopan da kuma cocp wajen kawar da ciwon.
4 Comments
Mekesa jini ya dawo period after 10 days please
ReplyDeleteAkwai abubuwa dadama masu kawo rikicewar jinin period. Mun yi bayanin su dallah dallah da kuma yadda ake maganinsu a cikin wannan post din. https://www.lafiyata.com.ng/2023/01/rikicewar-alada-jinin-haila-da-kuma.html
DeleteMeyasa idan nafara jinin al'adah ina rashin lafiya sosai
ReplyDeleteWannan duk yana cikin canje-canjen yanayin da mata ke samu a lokacin jinin al'ada. Ko wace mace da irin yadda abubuwan suke mata. Munyi bayanin wadannan canje-canjen dallah-dallah da Kuma yadda ake maganinsu acikin wannan rubutu https://www.lafiyata.com.ng/2023/08/canje-canjen-da-ke-faruwa-ga-mata.html?m=1 ki shiga ki amfana
Delete