Bayanin Saduwar Aure Da Yadda Ake Daukar Ciki (Conception)

Gabatarwa:

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta Æ™iyasta cewa, duk bayan minti É—aya aÆ™alla mata goma sha biyu (12) suna daukar ciki a Æ™asar Nigeria. Kwanciyar aure ko kuma saduwar aure abu ne mai matuÆ™ar muhimmanci a rayuwar É—an adam domin ta wannan hanyar ne jinsin É—an Adam zai ci gaba da wanzuwa a doron kasa. 

Duk da cewa, a kimiyyance ana iya samun haihuwa ba tare da namiji da mace sun haÉ—u sun sadu da juna ba, watau ta hanyar da bature yake kira "assisted reproductive techniques", toh amma hanyar saduwar aure itace hanya ta asali kuma hanya mafi sauÆ™i da É—an adam zai bi domin cigaba da samar da jinsin sa a doron Æ™asa[¹].

Ba É—orewar jinsi kaÉ—ai ba, saduwa tana da amfani ga jikin É—an adam kamar rage Æ™ishirwar sha'awa da ke damun samari da 'yan mata, inganta lafiyar Æ™waÆ™walwa, Æ™ara Æ™arfafa garkuwan jiki da kuma taimakawa wajen daidaita wasu sinadaran hormones a jikin mutum[¹].


Sassan jima'i a jikin É—an adam

Sassan jima'i wasu gaÉ“oÉ“i ne a jikin dan adam da ake amfani da su ko kuma suke taimakawa wajen saduwa ko yiwa mace ciki. WaÉ—annan gaÉ“É“ai sun bambanta tsakanin mace da namiji[¹].

Sassan jima'in namiji:

  • Penis : Azzakari
  • Testes :ƳaÆ´an marina
  • Scrotum : Fatar da ke É—auke da Æ´aÆ´an marina
  • Urethra : Bututun da ke fitar da fitsari da ruwan maniyyi
  • Prostate : Gland ne mai samar da wasu ruwa masu yauÆ™i
  • Seminal vesicles : Gland ne mai samar da wasu ruwa masu kauri
  • Epididymis: Wani bututu ne dake manne a bayan ya'yan marina, yana ajiye tantanin halittun haihuwa (ya'yan maniyyi) kafin lokacin inzali.
  • Vas deference : Wani bututu ne da ke É—auko tantanin halittun haihuwa daga epididymis zuwa tushen azzakari a yayin inzali.


Sassan jima'in mace

  • Vagina : Farji
  • Uterus : Mahaifa
  • Ovaries : Gland ne dake samar da Æ™wan haihuwa a duk wata(month)
  • Fallopian tubes: Bututun Fallopian wani bututu ne dake É—aukar Æ™wai daga ovaries zuwa cikin mahaifa
  • Clitoris : Dan tsele ko kuma beli
  • Labia majora : LaÉ“É“an farji manya
  • Labia minora : LaÉ“É“an farji Æ™anana
  • Hymen : Tantanin budurci, yana fashewa da zarar aka fara saduwa da mace.


Yadda ake tsokano sha'awa budurwa ko saurayi

Sha'awar É—an adam tana motsawa ne a lokacin da Æ™waÆ™walwar sa ta karÉ“i wasu saÆ™onnin da zasu iya motsa masa sha'awa daga jakadun Æ™waÆ™walwar sa dake gangar jiki (idanu, kunne, hanci, baki da kuma jakadun Æ™waÆ™walwa dake kan fata)[²]. Misali:

  • 1. Idanu - mutum ya kalli wani abin da zai motsa masa da sha'awa, kamar kallon matarsa, irin kallon sha'awa.
  • 2. Kunne - mutum ya saurari wani abin da zai motsa masa sha'awa, kamar kalaman soyayya ko kalaman batsa.
  • 3. Hanci - mutum ya shinshina wani abin da zai motsa masa sha'awa, kamar turaren matar sa, ko wani Æ™amshi da ya saba ji a lokacin da yake jima'i ko yake cikin sha'awa.
  • 4. TaÉ“i - mutum ya taÉ“a ko a taÉ“a masa wani wurin da sha'awar sa zata motsa. Jakadun fata zasu É—auki saÆ™on zuwa Æ™waÆ™walwar sa. Misali, sumbata, runguma, massaj da shafar jiki.
  • 5. Baki - mutum yaci wani abinda ke motsa masa sha'awa. Ko kuma yaci abincin da matarsa ke yawan kawo masa kamin suyi jima'i. A duk lokacin da yaci irin abincin zai iya jin sha'awar sa ta motsa.
  • 6. Tunani - mutum ya kama tunanin saduwa ko tunanin matar sa ko tunanin batsa. Shima wannan yakan motsa sha'awar É—an adam.

Me ke sa azzakarin namiji ya miƙe a lokacin sha'awa?

Da farko a duk lokacin da sha'awar É—a namiji ta motsa Æ™waÆ™walwar sa za ta karkatar da samar da isasshen jini zuwa ga azzakarin sa. Azzakari yana É—auke da jijiyoyin jini da wasu tsokoki na musamman waÉ—anda za su iya Æ™ara tsawo kuma zasu iya ragewa. 

Cikar waÉ—annan jijiyoyin jini a lokacin da zuciya ta karkatar da samar da jini zuwa azzakari shi zai sanya azzakari ya miÆ™e kuma tsokar jikin sa tayi tauri[²].

Yadda namiji yake kawowa a lokacin jima'i

A lokacin da ake saduwa tsakanin namiji da mace, namiji yana shige-da-fice da azzakari a cikin gaban mace, wasu jakadu dake jikin fatar azzakari zasu É—auki taÉ“i da kuma shafar da fatar azzakari ke yiwa fatar farji a matsayin saÆ™on jindadi na musamman sannan su aikawa Æ™waÆ™walwa.

ƘwaÆ™walwar É—an adam za ta fassara wannan saÆ™o a matsayin wani jin dadi na musamman sannan ta fara fitar da wasu sindaran hormones. 

A yayin sha'awar namiji yayi nisa, jindadin ya kai Æ™ololuwa, Æ™waÆ™walwar namiji za tayi umurni ga tantanin halittun haihuwa (sperm cells) da ke cikin kwararon epididymis da su kama hanya zuwa cikin azzakari. 

Daga nan zasu kama hanyar su ta cikin vas deference har zuwa tushen azzakari, a yayin da suka zo tushen azzakari daga nan zasu haÉ—u da wani ruwa da prostate gland ke fitarwa mai yauÆ™i da kuma wani ruwa mai kauri wanda seminal vesicles ke samarwa. 

WaÉ—annan ruwan guda uku (tantanin halittun haihuwa da suka taso daga epididymiys zuwa tushen azzakari, ruwan da prostate gland ke fitarwa da kuma ruwan da seminal vesicles ke fitarwa) su ne zasu gauraya su fito ta hanyar azzakari a matsayin ruwan maniyyi lokacin da namiji yake kawowa ko kuma yin inzali.

WaÉ—annan ruwan maniyyin da namiji yake kawowa a lokacin saduwar aure suna É—auke da tantanin halittun haihuwa da zasu kai kimanin miliyan talatin da tara zuwa miliyan É—ari biyu(39 - 200 millions) ga lafiyayyen namiji. 

Ko wane É—aya daga cikin waÉ—annan miliyoyin tantanin halittun zai iya yiwa mace ciki (juna biyu) idan ya haÉ—u da Æ™wan tantanin halitta É—aya da macce ke kawowa a duk wata.[²][³].

A lura cewa, a lokacin da namiji yake cikin Æ™aramar sha'awa kamin ya fara saduwar aure ko lokacin da ya ke tunanin saduwa, ko yayin wasa da matar sa yakan iya samun wasu ruwa marar kauri suna fito masa daga azzakari (ruwan da ake kira maziyyi da Hausa), waÉ—annan ruwan gland É—in prostate ne kawai ba tare da maniyyi ba, su ruwan maniyyi basa fitowa sai a lokacin babbar sha'awar lokacin da namiji yake kawowa, kuma da sun gama fita sha'awar namiji za ta dauke[³].

Yadda ake tsokano sha'awa budurwa ko duk wata mace

Yadda ake tsokano sha'awar budurwa ko duk wata mace shi ne, ta hanyar yin wasa da ita da kuma shafa mata sassan jima'inta waÉ—anda mun ka ambata a baya. A lokacin da sha'awar mace ta motsa Æ™waÆ™walwar ta zatayi umurni ga zuciyarta domin ta samar da isasshen jini zuwa ga al'aurar ta. Samar da wannan isasshen jini zuwa al'aura zai sa al'aurar mace ta kumbura kuma tayi jaa sosai. 

Haka zalika Æ™waÆ™walwarta za ta yi umurni ga wasu glands da ke cikin mahaifarta su fara samar da wasu ruwa masu yauÆ™i, waÉ—annan ruwan sune zasu gangara zuwa a gabanta domin su samar da ni'ima, da santsi a lokacin da fatar azzakari ke shafar fatar farji. WaÉ—annan ruwan suna Æ™aruwa sosai a duk lokacin da sha'awa da kuma jin daÉ—in jima'in da mace keyi ya Æ™aru[¹][²].


Yadda mace ke kawowa idan taji dadin saduwa 

A lokacin da mace ta kai ƙololuwar jindadin jima'i, ƙwaƙwalwar ta takan yi umurni da fitar da waɗancan ruwan da muka ambata a sama dayawa, fitar da wadannan ruwan da yawa shi ake kira da kawowar mace ko inzalin mata ko fitar ruwan maniyyin mata. Haka kuma fitar wannan ruwan yana kai maƙura ne a lokacin da mace ta kai maƙurar jindadin saduwa.

Amma a lura cewa, waÉ—annan ruwan da mace ke kawowa a lokacin da ake jima'i da ita har yanzu suna wani babi na mahawara ga masana ilimin kimiyyar É—an adam. Amma bisa ga magana mafi inganci ruwan da mace ke kawowa basu da wata alaÆ™a da tantanin halittun haihuwar da take bada gudunmawa domin daukar ciki. 

SaÉ“anin ruwan maniyyin da namiji ke kawowa daga azzakarin sa a lokacin jima'i, su ruwan maniyyin da mace ke kawowa daga farjinta aikinsu kawai shi ne samar da ni'ima da santsi da kuma inganta jindaÉ—in saduwa. 

Tunda abin ya zama haka, nasan mai karatu zai so yasan yanda mace ke bada gudunmawa domin samun ciki[²][³].

Yadda ake daukar ciki 

Mace tana daukar ciki ne ta hanyar samar da wani Æ™wai dake fitowa daga ovaries dinta, watau yin ovulation. A duk kowane wata (month) mace tana yin Æ™wai a cikin ovaries nata wanda yana samuwa ne a tsakiyar watan ta na al'ada, akwai alamomin ovulation da mace ke iya gani a wannan lokaci. 

Hakan zai yi dai dai da rana ta goma ko ta sha É—aya zuwa ta sha huÉ—u bayan tayi tsarki daga jinin al'ada. A lura cewa fitar da wannan Æ™wai baya da alaÆ™a da yin jima'i. Har matan da ba'a taÉ“a yin jima'i dasu ba duk wata sai sunyi wannan Æ™wai in dai sun balaga sun fara jinin al'ada[¹][³].

Yadda ake yiwa mace ciki (shigar ciki a jikin mace)

A duk lokacin da mace tayi Æ™wai ta fitar dashi ya kan fito daga ovaries dinta zuwa mahaifarta. Idan ta samu nasarar yin saduwar aure a lokacin da Æ™wan yake da rayuwa (Æ™wan ya kan dauki kwana biyu zuwa uku kamin ya mutu) har ruwan maniyyin namiji ya zuba a cikin farjin ta, toh tantanin halittun haihuwar da ke cikin ruwan maniyyin namiji za suyi tsera domin su je cikin mahaifarta su sadu da Æ™wan da ta sake domin a samu ciki. 

Daga zarar tantanin maniyyin namiji É—aya ya haÉ—u da Æ™wan mace shikenan sauran zasuyi haÆ™uri, shikenan mace ta dauki ciki. Daga nan kuma maniyyin namiji da kuma Æ™wan mace zasu haÉ—u su zama Æ™yanÆ™yasasshen Æ™wai sannan su ci gaba da girma a cikin mahaifa har zuwa haihuwa[³].

Illolin yawan saduwa a jikin namiji 

Duk da cewa saduwar aure yana da amfani a jikin mutum amma yawan yin saduwa barkatai kuma yakan haifar da wasu illoli a jiki. Manyan illolin sun haÉ—a da;
1. Kamuwa daga cututtukan da ake iya samu ta hanyar saduwa 
2. Yawan mantuwa
3. Jin ciwo yayin jima'i
4. Raguwar ruwan maniyyi
5. Rashin maida hankali akan muhimman abubuwa 

Bayanin rufewa

Saduwar aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a jikin ɗan adam, a cikin wannan rubutu munyi tsokaci sosai game da falsafar saduwa tsakanin mace da namiji a kimiyyance. Munyi bayanai tun daga yanda sha'awa take motsawa har zuwa yadda ake daukar ciki. Duk mai tambaya sai yayi ta a cikin akwatin sharhi dake ƙasan wannan rubutu. Insha'Allah zamu karɓa masa.

Nassoshi



3. Shtarkshall RA, Carmel S, Jaffe-Hirschfield D, Woloski-Wruble A. Sexual milestones and factors associated with coitus initiation among Israeli high school students. Arch Sex Behav. 2009 Aug;38(4):591-604. doi: 10.1007/s10508-008-9418-x. Epub 2008 Dec 18. PMID: 19093197.

Post a Comment

0 Comments