Gabatarwa:
Mene ne cutar sanyin mara na mata (PID)?
Cutar sanyin mara na mata wata cuta ce dake shafuwar al'aurar mata, mahaifa, bututun Fallopian, ovary da kuma sauran sassan al'auran su da ke cikin kunkumin su (their pelvic organs.
Cutar takan iya yaɗuwa daga cikin kunkumi (kwankwaso) zuwa cikin ciki a inda za ta iya shafar kitsen peritoneum da kuma kitsen da yake lulluɓe da hanta wanda hakan yana iya haifar da cutar da ake kira Fitz-Hugh-Curtis syndrome ko kuma ya haifar da cutar peritonitis ko kuma acute abdomen.
Me ke kawo cutar sanyin mara na mata (PID)?
Cutar sanyin mara na mata tana faruwa ne a lokacin da cututtukan bacteria waÉ—anda ke yaÉ—uwa ta hanayar jima'i suka yaÉ—u daga farjin mace zuwa cikin mahaifarta, bututun Fallopian, watarana har zuwa cikin kwankwasonta da kuma cikin ciki.
Idan mace ta kamu da cututtukan bacteria da ke yaɗuwa ta hanyar jima'i ba kai tsaye cutar kan iya shiga cikin mahaifarta ba saboda akwai wata kariya a ƙofar bakin mahaifa.
Ƙwayoyin bakteriya masu kawo cutar sanyin mara na mata suna iya shiga ne a lokacin da cutar ta yawaita a jikin mace ko kuma ta daɗe ba tare da an magance ta ba, toh wannan shi zai ba cutar dama ta shiga cikin mahaifa har ta kawo cutar sanyin mara.
Farjin mace wuri ne mai matuƙar adana ƙwayoyin cutar bacteria, wannan shi yasa ya zama wajibi ga kowace mace ta kula da tsaftace farjin ta saboda kaucewa miyagun cututtuka.
Duk da cewa farjin mace yana tara ƙwayoyin bacteria masu yawa, amma ba kowace ƙwayar bakteriya ce kan iya yaɗuwa daga farji zuwa cikin mahaifa har ta kawo cutar sanyin mara na mata ba.
Ƙwayoyin cututtukan bacteria waɗanda ke haifar da cutar sanyin mara na mata ko kuma sanyin PID dukan su ana samun su ne ta hanyar jima'i, manya daga cikinsu sun haɗa da;
- Ƙwayar cutar Neisseria gonorrhoeae
- Ƙwayar cutar Chlamydia trachomatis
- Ƙwayar cutar Gadnerella vaginalis
- Ƙwayar cutar Trichomonas vaginalis
- Ƙwayar cutar Mycoplasma hominis
- Ƙwayar cutar Ureaplasma urealyticum
- Ƙwayar cutar Streptococcus agalactiae
- Ƙwayar cutar Haemophilus influenzae
- Ƙwayar cutar Mycoplasma genitalium
Alamomin cutar sanyin mara na mata ko sanyin (PID)
- Yawan zazzaɓi ko zafin jiki
- Fitar farin ruwa mai yawa, mai kauri, mai yauƙi da wari daga farjin mace (wata rana kalan ruwan yakan chanja zuwa kore ko kamar ruwan ƙwai).
- Ciwon mara
- Warin gaba
- Kaikayin gaban mace
- Jin zafi yayin saduwa
- Zubar da jini yayin jima'i ko bayan an gama
- Jinin haila mai wasa
- Jin zafi yayin fitsari
- Rashin haihuwa
- Amai.
Wa zai iya kamuwa da cutar sanyin mara (PID)?
Amma duk da haka akwai cututtukan da kan iya sa mace zubar farin ruwa da ake iya samu bayan amfani da kazamin ban daki, amma ba cututtukan sanyin mara ba ne.
Shin namiji zai iya kamuwa da cutar sanyin mara na mata (PID)?
Idan har namiji ya sadu da mace mai É—auke da wannan cutar ta sanyin mara ko kuma ya sadu da mace mai É—auke da cutar Gonorrhoe ko Chlamydia wadda ba ta riga ta haifar da cutar sanyin mara na mata ba toh tabbas zai kamu da cutar kuma ya fara nuna alamomin sanyin mara na mata.
Haka kuma a lura cewa, ba kowane zubar ruwa daga gaban mace ke nuna cewa mace na da cutar sanyin mara ko sanyin PID ba, saboda haka, kar ayi zargin kowa, idan mace ta lura kamar ta na fama da wasu alamomin sanyin mara toh to garzaya asibiti domin sanin abin da ke damunta.
- Fitar da wasu ruwa fari mai kauri da wari bayan ya gama fitsari
- Jin zafi yayin fitsari
- Jin ciwo a ya'yan marina
- Kumburin 'ya'yan marina
- Yawan kasala
- Ciwon gabbai
- Zazzaɓi (bai cika aukuwa ba)
Yadda ake gane cutar sanyin mara (PID) a asibiti
1. Ta hanyar daukar tarihin yadda ciwon ya fara da sauran bayanai
Na farko shi ne za'a É—auki ingantaccen bayani daga marar lafiya dangane da yadda ciwon ya fara da kuma irin alamomin sanyin mara da take ji. Haka kuma za'a tambayi marar lafiya ta bada ingantaccen bayani akan rayuwarta a fannin jima'i.
Bayan ɗaukar taƙaitaccen tarihin ciwon daga bakin marar lafiya za'a duba marar lafiya akan gadon asibiti. Duba marar lafiyar ya ƙunshi duba lafiyar jikinta baki ɗaya (general examination) da kuma duba farjinta da mahaifar ta (Pelvic examination).
Wannan shi ne duba mai matuƙar amfani a cutar sanyin mara. Idan za'a yi wannan duban likita zai fara duba lafiyar farjin mace da wata roba da ake kira speculum kamin ya sanya yatsan sa aciki. Likita zai sanya yatsan sa a cikin farjin domin gano wasu manyan alamomi na cutar sanyin mara. Manyan alamomin sanyin mara da za'a iya samu yayin da likita ya sanya yatsan sa acikin farji sune:
- Lower abdominal tenderness: Raɗaɗin ciwo idan an taɓa mara ta waje (ana duba shi kamin a sanya yatsa).
- Adnexal tenderness: Raɗaɗin ciwo idan an taɓa gefen mara ta ciki (gefen hagu ko na dama).
- Cervical excitation tenderness: Raɗaɗin ciwo idan an taɓa bakin mahaifa.
- Hyperemic cervix: Bakin mahaifa yayi jajir
- Abnormal cervical discharge: Fitar wani mummunan ruwa daga bakin mahaifa.
3. Gwaje-gwajen da za'a iya yiwa mace mai alamomin sanyin mara
1. High vaginal swab M/C/S: Wannan wani kalan gwaji ne da za'a sanya auduga a can cikin ƙolin farjin mace a ɗebo farin ruwan da ke fitowa daga bakin mahaifa sannan a je ɗakin gwaje-gwaje sai a auna shi domin tantance wace irin ƙwayar bacteria ce ke da alhakin kawo cutar.
Bayan an gano cutar haka zalika, za'a gwada mata magunguna daban daban domin gane wane magani ne yafi inganci wajen kashe ƙwayar cutar.
2. Hoton ciki - Abdominal Ultrasound: Wannan wata fasaha ce da ake amfani da igiyoyin sauti domin É—aukar hoton abubuwan da ke cikin ciki. Yin wannan hoton yana da amfani a ciwon sanyin mara saboda zai nuna yanayin da mahaifa take ciki da kuma sauran kayan ciki.
Haka kuma idan akwai taruwar ruwan ƙurji a cikin ciki ko kuma a cikin bututun Fallopian za'a gani, wanda hakan yana yawan faruwa a cutar sanyin mara.
3. Gwaje-gwajen jini - Blood tests: Waɗannan sun ƙunshi gwaje-gwajen da za'a ɗibi jini aje ayi, kamar su FBC - wanda zaj iya nuna ƙaruwar WBC fiye da misali saboda maida martani ga cutar, ESR - zai yi sama, C-reactive protein shima zai yi sama da kuma sauran gwaje-gwajen cututtukan da zasu iya yaɗuwa ta hanyar jima'i kamar su HIV, Hepatitis B and C, Sphyllis da dai sauransu.
5. Endometrial biopsy: Wannan wani gwaji ne da za'a É—ebi wani sashe na bangon mahaifa na ciki domin aje dashi a gwada a É—akin gwaje-gwaje.
Yadda ake maganin cutar sanyin mara na mata (Sanyin PID)
Yana da kyau da an fara ganin alamomin cutar sanyin mara na mata ko alamomin cututtukan da ke yaduwa ta hanyar saduwa toh a gaggauta neman maganin sanyin mara ingantacce na asibiti. Saboda cutar sanyin mara ana iya maganinta kai tsaye amma ba'a iya maganin wasu illolin da take haifarwa a jikin mace ko namiji.
1. Amfani da magungunan antibiotics
Wajibi ne ayi amfani da magungunan antibiotics yadda ya kamata a wajen magance cutar sanyin mara, ana amfani da allurorin antibiotics da kuma magungunan sha.
Idan mace tazo asibiti cikin yanayin gaggawa (emergency) sakamakon cutar sanyin mara to ya wajaba a ba ta gado a asibiti ayi mata allurorin jijiya na antibiotics na aƙalla kwana biyu (2 days). Allurorin da za'a yi mata su ne:
- IV Ceftriaxone 1g dly × 2/7
- IV Metronidazole 500mg bd × 2/7
- IV Doxycycline 100mg bd × 2/7 (Saboda IV Doxycycline yana da ciwo sosai anfi so ayi amfani da Æ™wayoyin magani)
- Tabs Metronidazole 400mg tds x 2/52
- Caps Doxycycline 100mg bd x 2/52
- Tabs cefixime 400mg bd x 2/52
Wadda kuma ta zo ba cikin yanayin gaggawa ba amma tana da wasu alamomin cutar sanyin mara, toh ana yi mata allura daya ta Ceftriaxone a duwawu (IM Ceftriaxone 500mg stat) sannan sai a aza ta kan magungunan sha har sati biyu kamar yadda muka ambace su a sama.
2. Barin yin jima'i har sai mace ta warke
Dalilin wannan sharadi shi ne, idan mace ta cigaba da saduwa kuma tana shan maganin sanyin mara, toh na farko za ta cigaba da yaÉ—a cutar zuwa ga abokin saduwar ta, na biyu shi ma zai cigaba da yaÉ—a mata ko da tana kan magani, cutar za ta cigaba da shiga jikinta.
3. Yiwa abokan saduwa magani
Idan aka gane mutum yana da sanyin mara, mace ko namiji, toh duk wanda ya taɓa yin jima'i dashi cikin kwanaki sittin (60) da suka shuɗe ya zama wajibi yasha maganin sanyin mara.
Dole ne abokin jima'i ayi masa allurar tsoka ta ceftriaxone kamar yadda muka ambata a baya kuma yasha maganin ƙwayoyin da muka ambata a sama har na tsawon sati biyu koda ko baya da wata alamar rashin lafiya a tattare dashi. Haka kuma dole ne su daina yin jima'i har sai kowannen su ya gama shan magani kamar yadda muka ambata a sama.
WaÉ—annan su ne sharuÉ—É—an da aka gindaya idan ana so a warke daga cutar sanyin mara kuma a kaucewa illolin da take haifarwa.
Illolin cutar sanyin mara (PID)
1. Infertility - Rashin haihuwa ga mata: Cutar sanyin mara tana haifar da rashin haihuwa ga mata ta hanyar toshe musu bututun Fallopian. Wannan bututun kamar yadda muka sani shi ke da alhakin ɗauko ƙwan mace daga ovary zuwa cikin mahaifa domin a samu ciki (Domin ƙarin bayani game da amfanin bututun Fallopian a waje samun juna biyu toh karanta wannan rubutu "Ingantaccen bayani akan ilimin kimiyyar jima'i")
2. Ectopic pregnancy - Mace ta samu ciki a wajen mahaifa ko kuma ciki a bayan mahaifa (pregnancy outside uterus).
3. Tubo-ovarian abscess - Ƙurji tsakanin ovary da bututun Fallopian.
4. Yawan ciwon mara da kwankwaso
5. Urethral structure - Tsukewar bututun fitsari na maza da ke cikin azzakari: Kamuwa da cutar sanyin Gonorrhoe ko Chlamydia yakan iya sa bututun fitsarin maza ya tsuke har namiji ya kasa fitar da fitsari da kansa sai anyi masa tiyata. Hakan yana faruwa ne idan cutar ta daÉ—e a jikin namiji ba tare da magani ba. Wannan baya shafuwar mata saboda bututun fitsarin mata baya da tsayi sosai kuma yana da faÉ—i da yelwa.
6. Adhesions: Adhesions wasu abubuwa ne masu kamar zare da ke faruwa a cikin ciki sakamakon irin wannan cutar, adhesions suna da matsala sosai, domin sukan iya hana mace haihuwa ko kuma su kawo mata toshewar hanji.
Yadda zan kare kaina daga cutar sanyin mara na mata (PID)
Kammalawa
Cutar sanyin mara cuta ce da wasu ƙwayoyin bacteria da ke yaɗuwa ta hanyar jima'i ke kawo wa. Ita wannan cutar tafi shafuwar yan mata ƙanana waɗanda ke yin jima'i barkatai. Alamomin cutar sanyin mara ko sanyin PID sun haɗa da fitar wani mummunan ruwa mai wari daga farjin mace, jin ciwo yayin jima'i, rikicewar al'ada, yawan ciwon mara da kuma jin ciwo yayin fitsari.
Haka kuma ana maganin wannan cutar ta hanyar shan magungunan ƙwayoyi na antibiotics, kamewa daga jima'i har na tsawon lokacin shan magani da kuma yiwa abokan jima'i magani.
0 Comments