Gabatarwa:
A cikin wannan rubutu zamu fayyace muku abubuwan da ke kawo rikicewar jinin al'ada da kuma yadda ake maganin su[¹].
Mene ne lafiyayyen adadin jinin haila?
Kamin mu san mene ne jinin haila mai wasa ko kuma rikicewar jinin al'ada ya kamata mu É—an yi tsokaci game da mene ne lafiyayyen al'ada.
Masana sun Æ™ayyade cewa lafiyayyen jinin al'ada yakan shafe kwanaki huÉ—u (4) zuwa kwanaki bakwai (7) yana zuba sannan ya É—auke, idan ya É—auke yakan shafe kwanaki ashirin da É—aya (21) zuwa kwanaki talatin da biyar (35) kamin kuma ya sake dawowa[¹].
Mafi yawancin mata su kan shafe kwanaki ashirin da É—aya (21) idan jinin ya É—auke kamin su sake ganin wani jinin yazo, idan yazo sai suyi kwana huÉ—u (4) zuwa kwana bakwai (7) suna yinsa kamin ya É—auke.
Masu yin haka su ne waÉ—anda watan al'adan su yake da kwanaki ashirin da takwas (28 days cycle), ma'ana tsakanin farawar jinin al'adan wannan wata zuwa farawar jinin al'adar wani wata akwai kwanaki ashirin da takwas (28). Amma duk da haka wannan ya danganta daga wata mace zuwa wata mace.
Bugu da ƙari ko a mace ɗaya wannan adadin zai iya bambanta daga wani wata zuwa wani wata sai dai lafiyayyen wa'adin da mace zata yi idan jinin al'adarta ya ɗauke kamin ya sake dawowa ba zai kasa kwanaki ashirin da ɗaya ba (21) haka kuma ba zai yi sama da kwanaki talatin da biyar (35) ba.
Wani babban bincike da Æ™ungiyar Flo da Jami'ar Adelaide suka gudanar ya nuna cewa kusan kashi 16 cikin 100 na mahalarta binciken ne kawai ke da zagayowar kwanaki ashirin da takwas (28) cif-cif, duk da cewa ana yawan cewa wannan shi ne lafiyayyen adadin watan jinin haila[²].
Jinin haila mai wasa shi ne zuwan jinin haila wanda duk ya sabawa bayanin da muka a sama yi a matsayin lafiyayyen adadin jinin al'ada.
Yadda mace zata gane lafiyayyen adadin ta na al'ada
Ta fara bin diddigin al'adan ta a kowane wata har tsawon watanni dayawa a jere domin gano matsakaicin adadin jinin al'ada da take yi.
- Ranar da ta fara ganin jinin al'ada a wata
- Kwanaki nawa tayi tana zubar da jini
- Ranar da jinin al'adar ya É—auke
- Kwanaki nawa tayi kamin ta sake ganin wani al'ada.
- Kwanaki nawa ke tsakanin ranar da ta fara al'adan wannan wata zuwa ranar da ta fara al'adan wani wata na gaba.
- Pad nawa take yin amfani dasu kullum
- Matsalolin da take samu lokacin al'ada
Lafiyayyen adadin mace shi ne = Matsakaicin (average) kwanakin da take yi tana zubar da jinin al'ada + Matsakaicin kwanakin (average) da take yi idan jinin ya É—auke kamin ta sake ganin jinin al'ada na wani wata.
Ma'ana idan mace tayi rikodin na kwanakin jinin al'adarta kamar yadda muka yi bayani a sama toh za ta É—auki matsakaici (average) na kwanakin da takeyi tana zubar da jini sai ta haÉ—a da matsakaici (average) na kwanakin da take yi kamin jinin ya sake dawowa.
Ko kuma idan a ko wane wata tana yin kwanaki 4 tana zubar da jinin al'ada, sannan idan ya É—auke ta kan kwashe kwanaki 26 kamin ta sake ganin wani jinin al'ada, toh lafiyayyen adadin watan jinin al'adarta shi ne 4+26 wanda ya kama kwanaki 30 kenan (30 days cycle).
Mene ne jinin haila mai wasa ko rikicin jinin haila?
- Delayed period: Wannan shi ne jinkirin jinin haila ko rashin zuwan jinin al'ada lokacin da ya kamata. A ƙa'idance ana cewa mace ta samu jinkirin zuwan jinin al'ada ne idan mace ta ƙara aƙalla kwanaki biyar (5) tana jiran al'adanta kuma bai zo ba.
- Oligomenorrhea: Jinin al'adan da yaƙi zuwa har mace ta wuce kwanaki talatin da biyar (35) da yin tsarki amma yazo kamin ta kai kwanaki casa'in (90 days).
- Amenorrhea: Shi ne daukewar jinin haila har na tsawon watanni uku, ma'ana, jinin al'adan da yaƙi zuwa bayan mace ta shafe tsawon kwanaki casa'in (90) da yin tsarki.
- Polymenorrhea: Jinin al'adan da yake zuwa kamin mace takai aƙalla kawanaki ashirin da ɗaya (21) da yin tsarki ko kuma yin jinin haila sau biyu a wata ɗaya.
- Menorrhagia: Rashin daukewar jinin haila bayan mace ta yi kwanaki 7 da farawa. Ko kuma zuwan jinin al'ada da ƙarfi sosai yadda zai tilasta wa mace yin amfani da fiye da pad (kaɗar tare jini) ɗaya (1) acikin awa ɗaya (1). Masana sun sabunta sunan menorrhagia zuwa heavy menstrual bleeding (HMB) saboda wasu 'yan dalilai.
- Intermenstrual bleeding: Shi ne jinin haila mai wasa a tsakiyar watan mace, shi ne jinin da yake zuwa bayan mace tayi tsarki kamin lokacin zuwan wani al'ada, haka kuma zai É—auke kamin cikar kwanakin da take yi tana zubar da jinin al'ada. Mafi yawanci jinin yakan zo É—an kaÉ—an kuma baya daÉ—ewa yana zuba, wata rana ma mace zata ga alamunsa ne kawai a wandonta. Amma watarana jinin yakan iya zuwa dayawa[³].
Abubuwan da ke kawo jinin haila mai wasa
Amma rikicewar al'ada ga mata masu yawan shekaru da tsofaffi chan ba'a rasa ba yakan iya samo asali daga wasu cututtuka masu tashin hankali kamar irin su cutar sanÆ™arar bangon mahaifa na ciki (Endometrial cancer) ko sanÆ™arar bakin mahaifa (Cervical cancer) ko kuma kumburin fibroid. WaÉ—ansu abubuwa masu kawo rikicewar jinin al'ada sun haÉ—a da[²][³]:
- Stress; Yawan gajiya da kuma damuwa sukan iya sa mace ta daina ganin jinin al'adar ta yadda ya kamata.
- Lifestyle changes: Chanji game da yadda mace ke gudanar da rayuwar ta shi ma yakan iya kawo chanji game da yadda take jinin ta na al'ada. Misali mace mai ƙiba wadda ta rage ƙiba sosai ko kuma mace ramammiyar da tayi ƙiba cikin ƙanƙanin lokaci, rashin samun motsa jini irin yadda aka saba, ko kuma motsa jini fiye da yadda aka saba, chanjin kalar abincin da mace ke ci, da dai sauransu. Waɗannan sauye-sauyen duk sukan iya rikita jinin al'adar mace.
- Contraception: Amfani da magungunan ba da tazarar iyali, ko allurorin bada tazarar iyali ko kuma robar da ake sakawa a hannu domin bada tazarar iyali duk suna rikita al'adar mace. Idan mace tana amfani da waÉ—annan to zata iya fuskantar rikicewar al'ada, wannan yana É—aya daga cikin manyan matsalolin amfani da abubuwan bada tazarar iyali masu É—auke da sinadarin progesterone kawai. Sannan a lura cewa, koda mace ta daina amfani dasu to ba kai tsaye al'adan ta zai dawo dai-dai ba, yakan iya É—aukar lokaci har tsawon watanni shida (6) bayan ta daina amfani dasu.
- Pregnancy and lactation: Samun ciki da kuma shayarwa. Samun juna biyu yakan kawo daukewar jinin al'ada baki daya har sai an sauka da aƙalla sati shida (6). Haka ma mace mai ɗanyen jego takan ɗauki lokaci kamin al'adan ta ya dawo.
- Uterine polyps: Uterine polyps wani ƙurji ne dake fitowa a jikin bangon mahaifa na ciki. Wannan ƙurjin yakan kumbura yasa zubar jini ba bisa tsari ba.
- Uterine fibroids: Wannan wani kumburi ne da ke samo asali daga tsokokin mahaifa (tsokokin mahaifa su ne suka gina bangon mahaifa na tsakiya). Idan aka ƙyale kumburin yakan iya girma sosai ta yadda ana iya tsammanin ciki ne. Wannan kumburin yakan sa zubar jini sosai yayin al'ada da kuma lokacin da ba na al'ada ba. Haka kuma idan ya girma sosai yakan iya taushe mafitsara ya sa mace yawan fitsari.
- Endometriosis: Wannan shi ne samun ƙwayoyin halittun bangon mahaifa na ciki a wani wuri na daban. Yayin jinin al'ada wannan bangon mahaifa na ciki shi ne ke rushewa ya zubar da jinin al'ada. Samun ƙwayoyin halittun wannan bangon a wani wuri yakan haifar da ƙarin fitar jini yayin al'ada, Haka kuma yakan haifar da mummunan ciwon ciki ko ciwon mara yayin da jinin yake fita.
- Pelvic inflammatory disease: Cutar sanyin mara ita ma tana haifar da zubar jini ba bisa ƙa'ida ba. Bayanin wannan cutar ya gabata a cikin wannan rubutu "Bayani akan cutar sanyin mara da kuma yadda ake maganin ta"
- Polycystic ovary syndrome: Wannan wata cuta ce dake sa sinadaran hormones na namiji suyi yawa a cikin jinin mace. Wannan cutar takan haifar da oligomenorrhea (munyi bayanin mene ne oligomenorrhea a sama). Bayan haka wannan cutar ta kan hana mace samun ciki kuma ta kan sa mace ta siffantu da wasu halaye na maza kamar irin su gashin gemu ga mace ko gashin baki, ko muryarta ta koma irin ta maza da dai sauran halayen maza.
- Premature ovarian failure: Wannan cuta ce da ke sanya ovaries ɗin mace su daina aiki gaba ɗaya tun kamin takai shekara arba'in. Ovaries su ne ke da alhakin samar da sinadaran hormones na mata, waɗannan sinadaran kuma su ke sa mace tayi al'ada. Mace mai wannan cutar za ta daina al'ada baki ɗaya tun kamin lokacin dainawar ta yayi (aƙalla shekara arba'in da biyar (45) zuwa sama).
- Endometrial cancer: Wannan ita ce cutar sanƙarar bangon mahaifa na ciki. Tana sa zubar jini sosai
- Cervical cancer: Wannan itace cutar sanƙarar bakin mahaifa, itama tana sa zubar da jini barkatai.
- Use of steroids or anticoagulant: Shan wasu magungunan daga dangin steroids da kuma anticoagulant shima yana iya kawo zubar jini.
- Some medical conditions: Wasu cututtuka masu sa zubar da jini daga jikin mutum ba bisa tsari ba kamar irin su Haemophilia A, B and C, Von willebrand disease da dai sauransu. Waɗannan cututtukan sukan iya sa mutum yawan zubar da jini daga hanci (haɓo) ba tare da wani dalili ba.
Yadda ake gane rikicewar al'ada a asibiti.
Hakanan kuma za'a iya gano cutar endometriosis ko wasu yanayin cutar sanyin mara ta hanyar amfani da wani hoton bidiyo da ake kira laparoscopy inda likita zai yi ɗan ƙaramin huduwa a ciki sannan ya sanya wani siririn bututun ɗaukar hoto mai haske don ɗauko hoton bidiyon mahaifa da ovaries da sauran kayan ciki.
Yadda ake maganin rikicewar jinin al'ada
Haka kuma ana amfani da wasu magungunan bada tazarar iyali waÉ—anda suke É—auke da sinadarai biyu (Oestrogen da Progesterone) domin rage yawan jinin da ke zuba a lokacin lo kuma maganin daukewar jinin al'ada [⁴].
Magungunan bada tazarar iyali waÉ—anda suke É—auke da sinadaran oestrogen da progesterones (combined oral contraceptives pills) da kuma robar bada tazarar iyali wadda ake sanyawa a mahaifa (mirena) su ake amfani dasu wajen maganin daidaita jinin al'adar da ta rikice.
Haka kuma idan fibroid É—in Æ™arami ne akwai Æ™wayoyin magani da ake amfani dasu domin rage masa girma da miyagun alamomin da yake kawowa. WaÉ—annan magungunan sun haÉ—a da Æ™wayoyin busereline, leuprolide, triptorelin da goserelin. Haka kuma ana iya amfani da allurar Depo provera da sauran magungunan bada tazarar iyali na dangin progestin only pills[⁴].
5. Ko da yake babu takamaiman magani ga cutar endometriosis, amma akan yi amfani da maganin rage raÉ—adin ciwo domin rage ciwon da wannan cutar ke kawo wa. Magungunan da ke É—auke da sinadaran hormones irin su maganin hana haihuwa na iya taimakawa wajen hana girman endometriosis daga cikin mahaifa da kuma rage yawan asarar jini a lokacin haila.
Idan har abin yayi tsanani sosai ana iya amfani da ƙwayoyin goserelin da leuprolide domin tsayar da jinin al'ada. Haka kuma idan abin ya faskara ana iya yin tiyata domin cire waɗannan ƙwayoyin halittun bangon mahaifa da suka fito ba wurin su ba
Kammalawa
Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3.
10 Comments
Gaskiya ne
ReplyDeleteMe hukuncin jinin ya dauke har anyi wanka da Kwana daya ya sake dawowa
ReplyDeleteA jira sai ya kara daukewa sai a kara yin wanka. Wannan duk yana cikin rikice-rikicen al'ada.
DeleteAssalamu alaikum ina samun heavy flow,sakamakon tsayar da taxar iyali danai tun a watan july 2023,kuma kwanakin suna tsawaita xuwa kwana 8
ReplyDeleteKi yi amfani da wannan maganin Tabs tranexamic acid 500mg sau daya kullum idan kin fara period. insha'Allah zai daina
DeleteAssalamu alaikum period Dina ba ya rushing Dan Kadan yake fitowa kuma bakikirin.
ReplyDeleteHar tsawon kwanaki nawa yake miki haka
DeleteMeye kawo fitar ruwa Mai kama da jini Amma brown bayan gama al'ada da kwana ki sai yayi ta fitowa har zuwa wani al'adan
ReplyDeleteWannan yana cikin alamomin infection. Ki karanta wadannan post domin samun cikakken bayani https://www.lafiyata.com.ng/2023/03/yadda-ake-maganin-infections-vaginal.html?m=1
DeleteAslm Dan Allah meke kawon fitar jini brown Mae fatan data majina maji ko xare bayan gama al.ada da kamar kwana6
ReplyDelete