Alamomin Ovulation Da Hanyoyin Samun Ciki Ga Ma'aurata

Gabatarwa:

A yayin da daukar ciki ya kan zama kamar shan ruwa a wajen wasu ma'aurata, wasu ma'aurata suna shan wahala sosai kamin su samu dacewa. 

Samun ciki abu ne da ya ta'allaka da abubuwa da dama kamar, lafiyar mace, adadin shekarun ta, sanin kanta da wayewar ta, lafiyar namiji, yawan saduwa tsakanin ma'aurata da dai sauransu. 

A cikin wannan rubutu zamuyi bayani akan yadda mace zata gane ranar da take yin ƙwai (ovulation) da kuma hanyoyin da mace zata bi domin samun juna biyu a cikin sauƙi.

Mene ne ovulation?

Ovulation shi ne fitar da Æ™wai (egg) da yake faruwa a kowane wata daga ovaryn mace baliga. Wannan Æ™wai shi ne tantanin halittar da mace ke bada gudunmawa domin samun ciki. 

Ana samun ciki ne idan wannan Æ™wan ya haÉ—u da É—aya daga cikin Æ´aÆ´an halittun haihuwa dake cikin ruwan maniyyin namiji. 

Wannan haɗuwar itace ake kira da turanci 'fertilisation' wanda hakan shi zai sa ƙwan mace ya ƙyanƙyashe ta samu juna biyu. Domin ƙarin bayani game da yadda mace ke ɗaukar ciki ku karanta wannan rubutun da mu ka yi akan saduwar aure.

Yadda mace ke yin ovulation

Ko wace mace tana da ovary guda biyu a cikin kwankwasonta, waÉ—annan ovaries su ke da alhakin samar da Æ™wai, fitar da shi da kuma samar da wasu sinadaran hormones na mata. 

Duk da cewa mace tana da ovary biyu amma a duk kowane wata tana samar da Æ™wai Æ™wara É—aya kacal. Ovaries É—in guda biyu suna raba aiki ne a tsakaninsu, idan ovary ta gefen dama ta samar da Æ™wai a wannan wata toh wani wata mai zuwa É—ayan ce ta gefen hagu zata samar da Æ™wai ita kuma ta farkon ta huta. 

Haka shi ne É—abi'ar samar da Æ™wai daga ovaries. Amma duk da haka wata rana wasu mata su kan sami ovaries din su duka biyu su samar da Æ™wai a lokaci É—aya, watau mace zata fitar da Æ™wai biyu (2) kenan a wata É—aya. 

Wannan shi ne asalin samun cikin tawaye (Dizygotic twins) idan har mace ta fitar da ƙwai biyu kuma ta samu saduwar aure a lokacin da duka ƙwan biyu ke raye kuma ko wane ƙwai ya samu haɗuwa da tantanin halittun dake cikin ruwan maniyyin namiji, toh shikenan za ta samun cikin tawaye.

Mace tana samar da wannan ƙwai ne (tana yin ovulation) a tsakiyar watan ta na al'ada wanda yana kamawa ne bayan kwanaki goma (10) zuwa kwanaki goma sha biyu (12) bayan gama jinin haila. Ko kuma ranar da zai rage saura kwanaki goma sha huɗu (14) chif kamin zuwan jinin hailar ta na gaba.

Idan mace tayi ovulation, Æ™wan da ta fitar ya kan É—auki tsawon kwanaki biyu (2) zuwa kwanaki uku kamin ya mutu, a lokacin da Æ™wan ke raye shi ne kaÉ—ai lokacin da mace zata iya samun ciki. Wannan shi yasa mafi kyawun lokacin da ya kamata mace tayi saduwa idan tana son samun ciki shi ne ranar da take tsammanin fitar da Æ™wai (yin ovulation). 

Amma duk da haka idan ta samu yin saduwa da mijin ta ko sau É—aya ne a cikin kwanaki biyar (5) kamin tayi ovulation zata iya samun ciki saboda wasu tantanin halittun da ke cikin ruwan maniyyin namiji sukan É—auki tsawon kwanaki biyar (5) zuwa bakwai (7) a cikin mahaifar mace suna neman Æ™wai kamin daga baya su mutu. 

Haka kuma idan mace ba ta samu yin jima'i ba sai bayan kwanaki uku (3) da yin ovulation, toh ko sau nawa tayi jima'i a cikin kwanakin da ya rage ba za ta samu ciki a wannan watan ba sai dai wani wata idan ta ƙare yin jinin al'ada. Abin da yasa haka shi ne, ƙwan da mace ke fitarwa baya iya wuce kwanaki uku bai mutu ba.

Akwai wani chamfi da mafi yawancin mutane suka É—auka gaskiya ne, chamfin shi ne wai mace tana samun ciki ne idan tayi saduwa a ranar da ta Æ™are yin jinin al'ada. Wannan magana ba gaskiya bace kuma babbar katoÉ“ara ce a tsarin ilimin likitanci. 

Hasali ma, bayan gama period ranar da mace ta ga jinin al'adar ya dauke, toh, ba za ta iya samun ciki a wannan ranar ba, saboda akwai aƙalla kwanaki goma (10) kamin ta yi ovulation kuma tantanin halittun dake cikin ruwan maniyyin da zasu shiga mahaifarta idan tayi saduwa ba zasu iya kai kwanaki goma a cikin al'aurar ta basu mutu ba.



Alamomin ovulation

Kamin mace ta iya  gane ranar da za ta yi ovulation toh dole sai ta fahimci yanayin zuwan jinin al'adar ta da kyau. Wannan shi yasa likitocin mata su ke bada shawarar kowace mace ta rinÆ™a aje rekodin na yadda take yin jinin al'ada. Munyi bayani yadda mata zasu aje rikodin na jinin al'adar su a wannan rubutun na jinin haila mai wasa .

Kamar yadda muka yi bayani a baya, kwanakin da ake tsammanin mace za ta yi ovulation su ne rana ta goma (10th) ko ta goma sha É—aya (11th) ko ta goma sha biyu (12th) bayan gama jinin al'ada. A waÉ—annan kwanakin ana so ma'aurata masu neman haihuwa su dage da nema sosai.

Bugu da ƙari, akwai wasu alamomin ovulation da mace ke nunawa idan za ta yi ovulation. Waɗannan alamomin sun haɗa da:
  1. Zata ga wani ruwa mai yauƙi, marar kala yana yawan zuba daga gaban ta
  2. Zata iya jin wani ciwo kaÉ—an a gefen marar ta na hagu ko na dama
  3. Zata kama jin matsananciyar sha'awar saduwa 
  4. Kan nonuwan ta zai ɗan yi duhu kuma ya miƙe haka kuma idan aka taɓa akwai ciwo kaɗan
  5. Jikin ta zai ɗan ƙara zafi
  6. Akwai wani gwajin fitsari da ake yi da wata takarda irin ta gwajin ciki wanda yake nuna mace ta kusan ovulation ko akasin haka. Ana kiran gwajin da turanci ovulation predictor test.

Yadda mace za ta gane ovulation 

Bayan amfani da alamomin ovulation, mace ta na iya amfani da ovulation test domin tabbatar wa ko tana cikin lokacin ovulation ko a'a. A lokacin da mace ta fara ganin wasu alamomin ovulation ko kuma ta kirga kwanaki bayan gama period dinta, taga tana cikin lokacin ovulation, toh, za ta iya siyo ovulation test kit domin aunawa.

A lura cewa, ovulation test yana nunawa mace peri-ovulatory period ne, ma'ana lokutan da ake tsammanin mace za tayi ovulation da kuma immediately bayan ta gama, ba yana nuna duk ranar da kaga ya nuna positive toh a ranar ne mace za tayi ovulation ba. Peri-ovulatory period yakan iya kai 4 days, watarana ma fiye da haka. Akwai high chance of pregnancy a waÉ—annan lokuta.

Yadda ovulation test kit yake aiki shi ne, a lokacin da mace take daf da yin ovulation ana samun hauhawar wasu sinadaran hormones a cikin jinin ta da fitsarin ta, most notably, sinadaran LH da FSH, waÉ—annnan hormones su ke da alhakin sanya mace yin ovulation. Idan test kit É—in yayi detecting high level of these hormones a jini ko a fitsari toh zai nuna positive, idan kuma babu su dayawa toh zai nuna negative.

Hanyoyin samun ciki ga budurwa cikin sauƙi

  1. Dagewa da yin saduwa a kwanakin da mace ke tsammanin ovulation
  2. Yin saduwa akai-akai da kuma ƙauracewa duk wata hanyar ba da tazarar iyali; Masana sun fassara yin lafiyayyen saduwa akai-akai da samun saduwa a ƙalla sau biyu (2) zuwa uku (3) a cikin sati ɗaya ha ma'aurata. Sannan kwanakin saduwa kar su kasance suna bibiyan juna, anaso a bada tazara a tsakanin kwanakin domin namiji ya huta kuma ruwan maniyyinsa ya taru. Wannan shi yasa ba'a son namiji yayi ta jima'i kulli yaumin a jere sai a cikin kwanaki biyu ko uku da matarsa ke tsammanin ovulation.
  3. Anaso mace ta kwanta a bayanta na kamar mintuna goma (10) zuwa goma sha biyar (15) kamin ta tashi zaune bayan kammala saduwa. Yin haka shi zai ƙara bada dama ga tantanin halittun ruwan maniyyin namiji su shiga mahaifar mace.
  4. Ƙauracewa matsanancin motsa jini: Matsanancin motsa jini yana da illa ga jikin mace, domin yakan iya hana ta  samun juna biyu cikin lumana. Wannan shi yasa wasu mata masu Æ™wallom Æ™afa, ko masu gasar tseren mita ko mata sojoji suke samun matsalar haihuwa da yawan rikicewar jinin al'ada.
  5. Ƙauracewa shan sigari da barasa
  6. Samun lafiyayyen abinci
  7. Ƙauracewa duk nau'in abincin ko abin sha da ke ɗauke da sinadarin caffeine.
  8. Mace ta kula da jikinta kar tayi ƙiba sosai kuma kar ta zama siririya sosai.

Kammalawa

A cikin wannan rubutu mun ga cewa mace tana samun ciki ne a lokacin da ƙwan da take fitarwa a lokacin ovulation ya haɗu da tantanin halittun dake cikin maniyyin mijinta. Haka kuma mun ga cewa fitar da wannan ƙwai yana faruwa ne a tsakiyar watan al'adar mace. Bugu da ƙari mun ga alamomin ovulation da kuma wasu hanyoyi da ma'aurata ya kamata su bi domin samun ciki a cikin sauƙi.

Idan har kun amfana da wannan rubutu toh ku tofa albarkacin bakin ku akan akwatin sharhi da ke ƙasa kuma ku turawa 'yan uwa domin su ma su amfana. Yin haka yana ƙara mana ƙarfin gwiwa.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karÉ“a ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group É—in mu na WhatsApp domin kasancewa damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Post a Comment

4 Comments

  1. Mungode Amman in a samu ciki alamominnan natafi ya koyaya alamomin ovulation din

    ReplyDelete
    Replies
    1. Da lokacin ovulation ya wuce, toh alamomin ovulation zasu wuce ko an samu ciki ko ba'a samu ba. In har mace ta samu ciki sai dai ta fara jin alamomin cikin.

      Delete
  2. Idan ma ajiyar Kwan mace yanayi mata ciwo ko inta tsuguna zataji kamar sun kumbura mehakan yake nufi

    ReplyDelete
  3. Tana buƙatar ganin likita, ayi mata hoton scanning don tabbatar da abinda ke damun ta. Mai yiwuwa akwai cyst a cikin ma'ajiyar

    ReplyDelete

HTML To Show Only in Mobile Devices