Ciwon gwiwa da yadda ake maganinshi (Knee Osteoarthritis)

Gabatarwa:

Daga cikin ire-iren ciwon gwiwa da mutane ke fama da shi akwai ciwon gwiwa wanda ake cewa "Knee Osteoarthritis" a turance, watau amosanin gwiwa. Wannan ciwo ne da har a yanzu wasu mutane ke na É—aukar cewa ciwon sanyi ne musabbabin kawo shi. Amma bisa ga magana mafi rinjaye wannan ciwo ba shi da alaÆ™a da sanyi ko kaÉ—an. 

Gwiwa wata gaÉ“a ce da ta haÉ—a Æ™ashin gwiwa da Æ™ashin Æ™wabri a wuri É—aya, sannan take bada damar motsi a tsakanin Æ™asusuwan. Irin wannan ciwon gwiwa wanda ake kira Osteoarthritis  yana faruwa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaÉ“a wanda wani matashi ne da ke cikin gaÉ“ar gwiwa tsakanin Æ™ashin cinya da Æ™ashin Æ™wabri domin bada damar Æ™asusuwan gwiwar su riÆ™a gogayya da juna cikin sauÆ™i ba tare da tirjiya ba.

GaÉ“ar gwiwa gaÉ“a ce da ke É—awainiyar dakon nauyin jiki tun daga kai har zuwa gwiwa a lokutan tsayuwa ko tafiya da kuma buÆ™atar motsawarta a mafi yawan lokuta yayin zirga-zirga da kuma ayyukan yau da kullum. 

Hakan shi ya sa ciwon ke kama gwiwowi duka guda biyu duka duk da cewa ciwon gwiwa ɗaya na iya fin na ɗayar, watarana kuma gwiwa ɗaya kawai ciwon zai yiwa illah. Wannan aikin da gwiwa ke yi kulli yaumin, shi yasa tsananin ciwon yana ƙaruwa ne a lokacin da shekarun mutum ke ƙaruwa, haka kuma ciwom yafi damuwar mutane masu nauyi da kuma tsofaffi.

Bincike ya nuna cewa wannan ciwon gwiwa na kan-gaba a jerin larurorin da ke iya nakasa mutum sannan kuma ya tsugunar da mutum É—ungurugum! Saboda haka, tasirin wannan ciwon yana da babbar illah ga ingancin rayuwa, walwala da tattalin arzikin masu fama dashi.


Alamun ciwon amosanin gwiwa 

Masu irin wannan ciwon gwiwa suna fama da wasu alamomi da suka ƙunshi:
1) Ciwo mai É—abi’ar suka a cikin gwiwa, musamman da daddare ko da safe kamin a fara tafiya.
2) Kumburin gwiwa.
3) Riƙewar gwiwa.
4. Tirjiya a lokacin tafiya ko motsa gwiwa
5) Idan ma ciwon ya ta'azzara a kan ji sautin gugar Æ™asusuwan akan juna — Æ™urus-Æ™urus yayin lanÆ™wasa ko miÆ™ar da Æ™afa ko kuma yayin tafiya. 
Haka kuma, yau da gobe ciwon gwiwar kan iya haifar da sauye-sauye a kan gaɓar gwiwa tun daga ƙasusuwa, gurunguntsi, har zuwa tantanai da kuma tsokokin da ke aiki a kan gwiwar. Misali, raguwar tazarar da ke tsakanin ƙasusuwan gwiwa (sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓa), ɗaurewar tsokokin cinya na baya, da kuma raunin tsokokin cinya na gaba, da dai sauransu.

Masu haÉ—arin kamuwa da ciwon amosanin gwiwa

Mutane da suka fi yawan kamuwa da wannan amosanin gwiwa sun haÉ—a da:

1. Tsofaffi waɗanda shekarunsu suka miƙa, 45 zuwa sama.
2. Mutane masu ƙiba (taiɓa)
3. Masu haɗarin samun rauni ko buguwa a gwiwa, misali masu wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, masu wasan ƙwallon ƙafa.
4) waɗanda sana'o'insu ke buƙatar ɗaukan nauyi tare da daɗewa a tsaye ko ana tafiya, misali, yan dako.
5) Masu wasu nau'o'in tawayar gwiwa
6) Gado: Ana iya gadon wannan ciwon gwiwa, ma'ana idan cikin iyayen mutum wani yana fama da ciwon, akwai yiwuwar wani cikin Æ´aÆ´an sa yayi fama dashi idan lokaci yayi.

Kasancewar wannan ciwo yana farawa ne sannu-sannu, yana da matakan ciwo da naƙasu hawa-hawa kamar haka
1) Mataki na farko shi ke da mafi ƙarancin ciwo da nakasu.
2) Mataki na biyu shi ke da matsakaicin ciwo da matsakaicin nakasu.
3) Sai mataki na uku shi ne lokacin da zaizayewar ta kai maƙura kuma shi ne yake da mafi tsananin ciwo da mafi tsananin nakasu.



Yadda ake maganin ciwon amosanin gwiwa (Osteoarthritis)

Samun sauƙin wannan ciwon gwiwa yana da alaƙa da ɗaukar mataki da gaggawa tun da wuri domin fara shawo kan ciwon tun kamin ya ta'azzara. Misali, matakin farko na ciwon zai fi sauƙin magani a kan mataki na biyu, na biyu zai fi sauki a kan na uku. Saboda haka, ya wajaba ga mutum ya garzaya a asibiti cikin sauri da zarar an fara jin ciwon gwiwa domin shawo kan ciwon cikin sauki da kuma kaucewa nakasun da yake kawowa.

Sai dai, mafi yawancin masu fama da wannan ciwo na ɗaukar ɗabi'ar nan ta amfani da magungunan rage ciwo barkatai domin rage raɗaɗin ciwon gwiwa. Amma waɗannan magunguna ba sa iya warkar da wannan ciwo, sai dai suna rage raɗaɗin ciwon na wani ɗan lokaci.l ƙayyadadde. Saboda magungunan rage ciwo suna da wani ƙayyadajjen lokaci da suke ɗauka suna aiki a jikin ɗan adam, idan lokacin aikinsu ya ƙare, toh ciwo zai dawo har sai an sake shan wani magani, gashi kuma yawan shan irin magungunan yana da illar haifarwa mutune da cutar ulcer.

To ko mutum zai daina shan maganin rage raɗaɗi? A haƙiƙanin gaskiya babu lokacin daina shan maganin rage ciwo idan ba a je wurin ƙwararrun likitocin da ya kamata ba.

Likitocin fisiyo (Physiotherapists) ne ke kula da masu irin wannan ciwo. Waɗannan likitoci ƙwararri ne a wannan fanni, suna duba marar lafiya sannan su rage masa ciwon a sauƙaƙe ta hanyar amfani da wasu na'urorin rage ciwo na zamani ba tare da dogaro da magani kullum ba.

Bayan haka, za su bayar da keɓaɓɓun atisaye da motsa jiki na musamman na ciwon gwiwa domin tsokokin da ke kula da motsin gwiwa su sami ƙarfin iya riƙe ƙasusuwan gwiwar yadda ya kamata ba tare da ƙasusuwan na gugar juna ba.
Sannan suna koyar da wasu dabarun motsa jiki a cikin ayyukan yau da kullum domin kiyaye ire-iren motsin da ka iya sa ciwon ya ta'azzara.

Daga Æ™arshe, idan an gwada duk waÉ—annan hanyoyi amma ba su yi nasarar shawo kan wannan ciwo ba, hakan na iya tilasta É—aukar matakin Æ™arshe wajen magance wannan ciwon, wato É—aukan matakin yin aikin tiyata domin dashen gwiwar da zai maye gurbin zaizayayyen gurunguntsi. Ana É—aukar matakin yin aikin tiyata ne idan ba a fara ganin likitan fisiyo da wuri ba har sai da aka bari ciwon ya nakasa gaÉ“ar gwiwar. 

Kammalawa

Idan kana fama da ciwon gwiwa kuma ka sha magunguna har ka gaji amma abin ya faskara, toh ka hanzarta zuwa asibiti domin tuntuɓar likitan fisiyo (Physiotherapist) a yau domin magance ciwon gwiwa cikin lumana.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Post a Comment

0 Comments