Taƙaitaccen tarihin garin Aliero, Kebbi State, Nigeria




Aliero gari ne, da ke a jihar Kebbi a arewacin Najeriya. Wanda yake a kudu maso gabashin jihar Kebbi akan mizanin longitude da latitude na 12°16′42″N 4°27′6″E a sararin doron duniya. Sunan Aliero ya fito ne daga wani makiyayi da ake kira Ali ɗan Yaro. Ali ɗan Yaro makiyayi ne dake kiwon dabbobinsa a wurin da ake kira Aliero yanzu. Yan uwan Ali ɗan Yaro idan zasu zo ziyararsa sukan ce zamuje gun Ali Yaro, shikenan mutane suka maida gurin Aliyaro. Da turawan mulkin mallaka suka zo sai suka chanja sunan daga Aliyaro zuwo Aliero.




 Galibin mutanen karamar hukumar Aliero manoma ne, tare da ba da fifiko kan noman rani da damana. Mazauna Aliero an san su da ƙoƙari sosai a fannin siyasa domin sune gari na farko da suka samar da gwamna na farar hula a jihar Kebbi a shekarar alif ɗari tara da tis'in da tara (1999) watau tsohon gwamna Muhammadu Adamu Aliero wanda kuma har wa yau shi ne jigon siyasa a jihar Kebbi.
Bugu da ƙari, mazauna garin Aliero suna neman ilimin addini ta hanyar almajiranci da makarantun islamiyyu na zamani. Haka kuma samun babbar jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi a garin Aliero ya sauƙakawa mutanen garin neman ilimin zamani har a matakin jami'a. Yawan mutanen Aliero ya kai kimanin mutum dubu sittin da biyar da ɗari tara da saba'in da uku (65,973) a ƙidayar da aka gudanar a shekara ta dubu biyu da shida (2006).

Noma da kasuwancin albasa shi ne babban tattalin arzikin garin Aliero. Garin yana da kasuwar albasa mafi girma a arewa maso yammacin Najeriya kuma ita ce babbar kasuwar albasa a Najeriya. Ba albasa kaɗai ba, mutanen garin suna noman hatsi, gyaɗa, dawa, kayan lambu da dai sauransu. 

Idan kuna son samun cikakken tarihin garin Aliero da muka rubuta da harshen turanci domin taimakawa ɗaliban jami'a masu bincike ku shiga wannan rubutun: HISTORICAL BACKGROUND OF ALEIRO LOCAL GOVERNMENT AREA, KEBBI STATE, NIGERIA.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Post a Comment

0 Comments