Yadda ake maganin warin baki (Treatment of mouth odour - Halitosis)

Gabatarwa:


A Æ™iyasin masana, warin baki yana damuwar aÆ™alla kashi ashirin da biyar cikin É—ari na mutanen duniya (25%), ma'ana a duk cikin mutum huÉ—u (4) za'a samu aÆ™alla mutum É—aya na fama da warin baki. 

Warin baki yana iya faruwa sanadiyyar cututtuka a cikin baki ko cututtukan huhu ko kuma akan wani kalan abinci da mutum ke amfani dashi wanda zai iya canja warin numfashin mutum. 

Amma mafi yawancin warin baki yana aukuwa ne saboda rashin tsaftace baki yadda ya kamata. Ko ma miye sanadi, warin baki abu ne mai matuƙar kunyatarwa a cikin jama'a. A cikin wannan rubutu zamuyi bayani game da warin baki, abubuwan da ke kawo shi da kuma yadda ake maganinsa.




Abubuwan da ke kawo warin baki

1. Abinci

Rushewar barbashin abinci a ciki da kewayen haƙoran mutane na iya ƙara ƙwayoyin cuta masu haifar da warin baki mara kyau. Haka kuma cin wasu kalan abinci irin su albasa, tafarnuwa da kaya marar ƙamshi, suma na iya haifar da warin baki. Bayan mutum yaci irin waɗannan abinci akan narkar dasu zuwa cikin jini, idan suka shiga cikin jini suna shiga cikin huhu sannan su haifar da numfashi mai wari wanda zai fito ta baki.

2. Kayayyakin taba (sigari)

Shan taba (sigari) yana haifar da warin baki irin nasa marar dadi.  Masu shan tabar sigari da masu shan tabar gari  sun fi saurin kamuwa da cututtukan dasashi (gums). Cututtukan dasashi suma suna yawan haifar da warin baki.

3. Rashin tsaftace baki

Idan mutum baya kula da tsaftace bakinsa akai-akai musamman idan yaci wasu kalolin abinci yakan haifar da warin baki. Idan anci abinci barbashin abincin yakan laÆ™e akan haÆ™ora da kuma dasashi, wanda hakan yakan janyo hankalin dandazon Æ™wayoyin bacteria domin suci sauran abincin kuma su rugurguza shi su sanya shi ya ruÉ“e ya haifar da warin baki. 

Haka kuma ƙwayoyin bacteria idan suka daɗe suna cin abincin da ke kan haƙoran mutum sukan iya haifar da ruɓewar haƙora da kuma kawo wani cuta da ake kira periodontitis, wanda wani babban tushe ne na warin baki.

3. Bushewar baki

Yawun da ke cikin baki suna taimakawa wajen tsaftace baki da kuma kare haƙora daga ƙwayoyin cutar bacteria. Bushewar baki wanda ake kira da turanci xerostomia, wanda ke aukuwa sanadiyyar wasu cututtuka yana haifar da warin baki.

4. Magunguna

Wasu magunguna suna haifar da warin baki ta hanyar kawo bushewar baki wasu kuma suna haifarwa ne ta hanyar samar da wasu sinadarai a cikin jini waÉ—anda zasu je cikin huhu su shafi numfashin mutum.

5. Cututtukan baki

Cututtukan baki kamar irin su periodontitis, periodontal abscess, gingivitis, dental caries, ruɓewar haƙori, kogon haƙori, cututtukan dasashi da kuma wasu cututtuka da ke iya biyowa bayan anyi tiyata a baki suna iya haifar da warin baki.

6. Cututtukan hanci da maƙogwaro

Wani lokaci warin baki yana samo asali ne daga cututtukan maƙogwaro kamar irin su tonsillitis and paratonsillar abscesses. Haka kuma, wasu cututtuka daga hanci kamar irin foreign body a hancin, suna sanya warin baki.

7. Wasu cututtuka

Wasu cututtuka na daban, wadanda basu da alaƙa ko kusanci da baki suna iya kawo warin baki ta hanyar samar da wasu sinadarai a cikin jini. Misali cututtukan huhu irinsu cutar pneumonia, marurun huhu, ciwon sukari, ciwon hanta da ciwon sanƙara.

8. Azumi ko daÉ—ewa ba'a ci abinci ba

Idan mutum ya daɗe bai ci abinci ba, jikin shi yakan samar da wasu sinadarai da zasu taimaka masa ya samu ƙarfin jiki. Waɗannan sinadaran ana kiransu da sinadaran ketones, suna shiga cikin jini zuwa cikin huhu su shafi numfashin mutum sannan su haifar da warin baki.

Yadda ake maganin warin baki

Don rage warin baki, yana da kyau mutane su kula wajen guje wa kogon haƙora da rage abubuwan dake kawo cututtukan dasashi, da kuma koyaushe yin kyakkyawan tsaftar baki. Maganin warin baki ya danganta da abinda ya kawo shi.

Idan warin baki ya samo asali ne saboda dalilai masu alaÆ™a da cututtukan baki, likitan hakori zai yi aiki tare da ku don taimaka muku wajen magance wannan cutar. 

Idan kuma warin baki ya samo asali ne daga cututtukan da basuda alaƙa da baki, kamar irinsu cututtukan huhu, cututtukan maƙogwaro, ciwon suga, toh likitan baki zai tura ku zuwa ga likitoci masana wannan fanni.

Haka kuma idan warin baki ya samo asali ne daga Æ™arancin tsaftace baki likitan baki zai bada shawarwari game da amfanin tsaftar baki da kuma illolin rashin yin haka. Sa'annan zai bada wani man wanke baki mai É—auke da sinadarai masu kashe Æ™wayoyin bacteria wanda za'a yi  amfani dashi ayi brush kullum bayan an gama cin abinci. 

Haka kuma, za'a yi brush da safe daga zarar an farka bacci da kuma dadare a lokacin da za'a kwanta bacci. Idan anzo yin brush ba haÆ™ori da dasashi kawai ake wankewa ba, ana wanke dukkan baki ne, musamman harshe da rufin baki da kuma Æ™asan harshe. 

Saboda akwai ƙwayoyin bacteria dayawa masu kawo warin baki da suke ɓuya a waɗannan wurare.

Haka kuma anason yawan yin asiwaki da kuma kurkure baki da ruwa.
Man brush da ake iya amfani dashi sun haÉ—a da;
  1.  Sensodyne
  2. Colgate
  3. Oral B
  4. Euthymol
  5. Longrich
Haka kuma akwai ruwan kurkurar baki na bature masu ɗauke da sinadarai masu kashe ƙwayoyin cutar bacteria. Idan mutum na amfani da waɗannan ruwan, ana so ya kurkure bakinsa aƙalla sau uku (3) kullum da ruwan. Misalin ruwan ya sune kamar haka;
  1. Listerine mouthwash
  2. Oral B mouthwash
  3. Medex breath freshening
  4. Colgate mouthwash


Bugu da ƙari ana so mutum ya ziyarci likitan baki aƙalla sau biyu (2) a wata domin yin wanki baki na musamman.

Yadda zan kare kaina daga warin baki

  1. Kula da tsaftace baki: Anason kullum mutum yayi brush da man goge baki aƙalla sau biyu kullum. Da safe idan an farka daga bacci da kuma dadare idan za'a kwanta.
  2. Yin asiwaki akai-akai da yawan kurkure baki da ruwa
  3. Yin brush ko asiwaki duk mutum ya gama cin abinci
  4. Kaucewa chin wani kalan abinci mai wari kamar albasa da tafarnuwa
  5. Idan mutum na amfani da haƙoran roba ya kula da wanke su kullum.
  6. Zuwa wajen likitan baki aƙalla sau ɗaya a wata domin wankin baki na musamman.
  7. Magance cututtuka masu iya kawo warin baki kamar irinsu kogon haƙori, cutar pneumonia da marurun huhu.

Kammalawa

A ƙiyasin masana a duk cikin mutum huɗu (4) toh za'a samu aƙalla mutum ɗaya na fama da warin baki. A cikin wannan rubutun munga cewa mafi yawancin warin baki yana aukuwa ne saboda rashin tsaftace baki yadda ya kamata, haka kuma munga wasu cututtuka masu kawo warin baki da kuma yadda ake magance warin baki.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Post a Comment

0 Comments