Gabatarwa:
Yawancin waɗannan alamomin shigar ciki ba su keɓanta ga shigar ciki kaɗai ba. Wasu na iya nuna cewa rashin lafiya yana batun kama mace ko kuma jinin hailar ta ya kusa farawa. Haka kuma, wata mace za ta iya samun ciki ba tare da fuskantar yawancin waɗannan alamomin shigar ciki ba.
Alamomin shigar ciki a jikin mace
Manya-manyan alamomin shigar ciki na farko da kan iya nuna mace ta É—auki ciki sune kamar haka;
1. Rashin zuwan jinin al'ada
Idan mace na cikin shekarun haihuwa kuma mako daya ko fiye ya wuce ba tare da ta ga jinin hailar da take tsammani ba, zai iya yiwuwa ta samu ciki. Wannan ita ce babbar alamar daukar ciki, amma duk da haka, wannan alamar na iya zama mai rikitarwa idan dama mace na fama da jinin haila mai wasa.
2. Kumburin nono da ciwo kaɗan idan an taɓa
3. Yawan tashin zuciya ko amai
Duk da cewa, mafiyawanci mata suna jin yawan tashin zuciya a farkon shigar ciki amma wasu kuma ba su taɓa samun tashin zuciya a lokacin da suke da ciki. Wasu kuma suna samun matsanancin laulayi da zai kai har a kwantar da su a asibiti.
4. Yawan fitsari
Mace zata iya samun kanta tana yawan fitsari fiye da yadda ta saba. Wannan ya samo asali ne saboda yawan jini a jikin mace yana ƙaruwa lokacin da ta dauki ciki, hakan yana haifar da kodar mace ta tace fitsari mai yawa.
5. Kasala da yawan gajiya
Alamomin shigar ciki a satin farko
- Yawan É“acin rai: wannan yana faruwa ne saboda rashin daidaituwar sinadaran hormones da ke faruwa a lokacin da mace ta samu shigar ciki. Watarana mace kan iya yin har kuka ba tare da anyi mata komai ba, haka kewai ba gaira ba dalili.
- Yawan kumburin ciki idan mace taci abinci da kuma fitar da iska.
- Zuwan wani jini É—an kaÉ—an daga gaban mace. Wannan jinin wasu mata sukan É—auka kamar jinin al'ada ne, toh amma suna da bambanci sosai da jinin al'ada saboda bai kai jinin al'ada yawa ba kuma jinin al'ada yafi duhu da wari.
- Ciwon mara matsakaici
- Yawan jin ƙamshi ko warin abubuwa, ƙamshin wasu abubuwa yakan iya sa mace tayi amai duk da cewa ta saba jin ƙamshin ba tare da samun wata matsala ba.
- Rashin jindaÉ—in abinci
- Ko kuma kwaÉ—ayin wasu kalolin abinci
- Yawan toshewar hanci
- Yawan zazzaɓi ko ciwon kai
- Yawan taruwar yawu a baki
- Ƙaruwar zubar ruwa a gaban mace
- Fitar ƙuraje a fuska
Ya mace take gane tanada ciki?
- Mace zata iya fara yin awon ciki na fitsari tun a gida. Idan sakamakon ya nuna akwai ko babu sai taje asibiti ayi mata awon ciki na jini.
- Idan an ga sakamakon awon ciki na jini ya nuna akwai ciki toh sai aje ayi hoton ultrasound domin tabbatar da cikin da aka samu da lafiyarshi
- A ƙa'idar ilimin likitanci, ana tabbatar da cewa mace tana da ciki ne kawai idan anyi hoton ultrasound an ga hoton dan tayi a cikin mahaifar ta.
0 Comments