Gabatarwa:
Allah maÉ—aukakin sarki yana cewa:
“Ya ku waÉ—anda suka yi imani! Ku ji tsoron Allah kamar yadda ya kamata a ji tsoronsa”. (Qur'an 3:102)
A cikin ayoyin farko na Suratul Baqarah, Allah Ta’ala ya bayyana halaye na muminai da suka yi TaĆ™awa.
"Wannan littafi ne wanda babu shakka a cikinsa, shiriya ne ga masu tsoron Allah." (Qur'an 2:2)
Kalmar Muttaqeen (mutanen taqwa) ta samo asali ne daga Taqwa wanda a zahiri yana nufin "jin tsoron Allah".
Mene ne Taƙawa?
TaĆ™awa kalma ce ta larabci. Babu kalma É—aya tak a cikin harshen Hausa da za ta iya fassara ma'anar taĆ™awa yadda ya kamata. Ana siffanta taĆ™awa da tsoron Allah, da kiyaye wannan tsoron Allah da tawakkali a cikin zuciya wanda zai hana mutum aikata ayyukan da shari’ar Ubangiji ta hana tare da bin dokokinSa sau da Ć™afa. TaĆ™awa ita ce garkuwar da ke shiga tsakanin mutum da duk wani aiki na saÉ“awa umurnin Allah.
Halayen Muttaqeen (Masu tsoron Allah)
- Suna da cikakken imani da duk abin da Annabi (SAW) ya koyar da mu.
- Suna dagewa da Sallah
- Suna ciyarwa a cikin hanyar Allah
- Sun yi imani da abin da aka saukar a cikin Alqur'ani da nassosi da suka gabata
- Suna da yakini tabbatacce da lahira
- Suna da cikakken imani a kan ƙaddara da ilmin gaibu
Allah Ta’ala ya yabi wadannan mutanen da suke kokarin tabbatar da ingancin taĆ™awa a zuciyarsu da cewa:
"Waɗannan su ne a kan shiriya daga Ubangijinsu, kuma waɗannan sũ ne mãsu rabo." (Qur'an 2:5)
A kowane fanni na rayuwa ana son mumini na gaskiya ya kawata kansa da taƙawa saboda babu shakka ɗaukaka ta haƙiƙa a duniya da lahira tana samuwa ne ta hanyar taƙawa kawai. Kamar yadda taurari ke ƙawata sammai, masu biyayya da taƙawa a doron ƙasa suna ƙawata ƙasa. Allah madaukaki yana cewa:
"Lalle ne mafi ɗaukakar ku a wurin Allah, shi ne wanda ya fi kowa taƙawa." (Qur'an 49:13)
Sau da yawa muna yiwa wasu mutane laĆ™abi da 'mafi riĆ™on addini' ko kuma 'mafi riĆ™on ibada' lokacin da suka tsaya a kan umurnin Allah kuma suka kiyaye dokokinSa. Masu taĆ™awa suna yin Ć™oĆ™ari wajen aikata abubuwan da Allah ya umarce su da nisantar abubuwan da Allah Ya haramta musu. Abin da ke Ć™arfafa takawa shi ne Ć™auna da sanin Allah Ta’ala da kuma kwaÉ—ayin irin tanadin da Allah (SWT) yayi ma ma'abota taĆ™awa, wanda hakan shi ne yanayi mai kyau wanda ya kamata mumini ya dawwama a cikinsa.
Da aka tambaye shi game da Takawa, Manzon Allah (ď·ş) ya yi nuni zuwa ga zuciyarsa, ya ce: “Takawa tana nan!” (Muslim)
Alqur'ani da Hadisi cike suke da umarni da bayanai na kwaɗaitarwa masu nuni zuwa ga wajabcin sanya Taƙawa a cikin zuciya. Yawan adadin da aka maimaita umurnin yin taƙawa ya kamata ya zama saƙo a gare mu da ke nuni da muhimmancin taƙawa.
Ga fa'idodi guda 5 na yin taƙawa daga Alqur'ani
1. Sauƙi cikin al'amura
"Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, zai sassauta masa daga al'amarinsa." (Qur'an 65:4)
Allah Ta’ala ya ambaci wannan ayar da ta gabata a cikin suratu At-Talaq inda aka yi bayani a kan sharuddan aikin da ya halatta amma Allah baya son ana aikata shi, wato saki. Duk wanda yake da taĆ™awa Allah ya sauwake masa a duniya da lahira. Wannan ba wai yana nufin cewa mutum ba zai fuskanci wahala ba, sai dai ta hanyar albarkar taĆ™awansa, yana samun sauki da karfin jurewa waÉ—annan matsaloli ba tare da rasa imani ko fatan alheri ba. Haka zalika, sakamakon waÉ—annan matsaloli da ya shiga, Allah zai musanya masa su da alheri.
2. Hanyar fita daga matsaloli da kuma ƙuncin rayuwa.
"Kuma wanda ya bi Allah da takawa, zai sanya masa mafita." (Qur'an 65:2)
TaĆ™awa tana aiki ne a matsayin kariya ta Ubangiji daga fitintinu na duniya da kuma wahalhalun lahira. Mun ga misalin haka a cikin Alqur’ani inda a cikin kissar Khidr (Alaihissalam) dabi’ar adalci ta uba ta ceci ‘ya’yansa daga rashi a bayan rasuwarsa. Alqur’ani yana cewa: “Amma ga bangon, na wasu marayu maza biyu ne a garin; Kuma a Ć™arĆ™ashinsa akwai wata taska tasu; Kuma ubansu ya kasance sĂŁlihi, kuma Ubangijinsu Ya yi nufin su isa ga Ć™arfinsu, kuma su fitar da dĹ©kiyõyinsu, dõmin rahama daga Ubangijinka (Qur'an 18:82). Muhammad bn al Munkadir (rahimahullah) yana cewa: “Saboda takawa da kyautatawar bawa Allah yana tsare ‘ya’yansa da jikokin sa da dukkan iyalansa da ma gidajen da aka gina a kewayen gidansa”. (Tafsir Mazhari)
3. Wadata ta hanyar da ba a zato
"Kuma zai azurta shi daga inda ba ya zato." (Qur'an 65:3)
Allah Ta’ala shi ne Mahalicci, mai rayawa da ciyar da halittu. Duk abin da mutum yake buĆ™ata da buĆ™atar arziĆ™i ana iya samunsa a cikin tarin dukiyarSa. Alkawarin Ubangiji shi ne cewa masu taĆ™awa za su É—ore daga mabubbugar da ba za su taba tsinkayar samun arziki ba. Alkur'ani mai girma ya sake nanata haka a wata ayar: "Kuma da mutanen wata alĆ™arya sun yi imani kuma suka yi takawa, da mun bude musu albarkoki daga sama da kasa." (Qur'an 7:96)
4. Ikon bambance gaskiya da karya
“Ya ku wadanda suka yi imani! Idan kun bi Allah da taĆ™awa, zai sanya muku ma'auni (furqan). (Qur'an 8:29)
Idan mumini ya ga biyayyarsa ga Allah da son da yake masa ya kasance sama da komai, toh Allah ya yi masa baiwar furkan (irin wannan fahimtar da ba ta bari mutum yayi shakka tsakanin gaskiya da karya). Kowane al'amari ya kan bayyana a cikin zuciyarsa kuma idan ya fuskanci yanayi na rudani na zuciya, za a shiryar da shi zuwa ga daidai. A cikin Alkur’ani mai girma, an kira ranar yakin Badar “Yawm-al-Furqan” (ranar rarrabewa). Wannan rana ce mai muhimmanci a tarihin Musulunci wadda ta tabbatar da cewa babu wani makiyi da zai iya halaka mutanen da suke da goyon bayan Allah kuma irin waÉ—annan mutane za su yi nasara a dukkan ayyukan da suka yi.
5. Natsuwa
"Shi (Allah) ne Ya saukar da natsuwa a cikin zukatan muminai." (Qur'an 48:4)
Ana neman natsuwa da kwanciyar hankali a cikin dukkanin al'amuran rayuwa na yau da kullum. WaÉ—annan falala ne daga Allah waÉ—anda suka keÉ“anta musamman ga zukatan muminai na gaskiya. Mutane suna neman kwanciyar hankali a cikin kayan duniya, wasanni, dangantaka kuma wasu ma suna neman kwanciyar hankali a cikin aikata zunubi da mugunta, alhali kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya suna samuwa ne kawai daga Mahaliccin zuciyar. Idan bawa ya jingina zuciyarsa da ayyukansa da burinsa da buĆ™atunsa zuwa ga Allah, Allah Ta'ala yana ganin al'amuransa kuma ya sanya shi cikin kwanciyar hankali wanda hatta masu dimbin dukiyar duniya ke hassada. Alkur’ani yana cewa: “Wadanda suka yi imani kuma zukatansu suka natsu da ambaton Allah. Kuma lalle ne, da ambaton Allah zukata suke tabbatuwa a cikin natsuwa. (Qur'an 13:28)
Bayan fa'idodin da suka gabata na riƙon taƙawa, Ubangijin falala mai girma yana da fa'idodi na dogon lokaci da ya tanada ga muminai salihai. Matsayin ma'abota taƙawa ya zo a cikin ayoyi daban-daban na Alqur'ani mai girma wanda daya daga cikinsu itace:
"Ga waɗanda suka yi taƙawa, suna da babban rabo (Aljanna)." (Qur'an 78:31)
Addu'ar Manzon Allah (s.a.w) da ya yawaita ita ce: “Ya Allah! Ka kyautata taĆ™awa a cikin zuciyata, kuma ka tsarkake ta, Kai ne mafificin wanda zai iya tsarkake ta, Kai ne Mai kula da ita kuma Majibincinta”. (Muslim)