Yadda ake maganin fitsarin kwance - (Enuresis)

 Gabatarwa:

A rubutun baya munyi bayani dallah-dallah game da fitsarin kwance da abubuwan da ke kawo shi tare da yin tsokaci a kan wasu illolin sa. Yana da kyau a karanta rubutun da mukayi "Bayani game da fitsarin kwance" kamin karanta wannan rubutun domin samun ingantacciyar fahimta.


Gwaje-gwajen da za'a iya yiwa mai fitsarin kwance a asibiti

1. Urinalysis
2. Urine Microscopy Culture and Sensitivity
3. FBS
4. Abdominopelvic ultrasound

Yadda ake maganin fitsarin kwance

Mafi yawancin yara masu fitsarin kwance suna daina yin fitsarin kwance da kansu a lokacin da suka Æ™ara yawan shekaru ba tare da anyi wani magani ba. Amma idan yaro ya wuce mizanin yin fitsarin kwance kuma bai daina ba, wannan na iya zama sanadiyyar shigar sa cikin damuwa dashi da mahaifan sa. Hakan yakan iya sa wasu iyaye neman magani. 

Yadda ake maganin fitsarin kwance ya ƙunshi yin amfani da wasu dabaru na sauya yadda yaro yake gudanar da rayuwar sa, yin amfani da ƙwayoyin magani da kuma amfani da wasu na'urori na musamman masu fitar da wani sautin ƙararrawa a duk lokacin da yaro ya fara fitsarin kwance.

Canja hanyoyin gudanar da rayuwa da magungunan da za'a iya yi a gida.

A cikin wannan babi mun tsaro muku canje-canje da zaku iya yi a gida waɗanda zasu taimakawa yaro sosai ya daina yin fitsarin kwance ba tare da ya buƙaci wasu ƙwayoyin magani ba.

1. Iyakancewa yaro shan ruwa da yamma

Yana da matuÆ™ar mahimmanci yaro ya sami isasshen ruwa yasha a rana, don haka babu buÆ™atar iyakance yawan abin da yaranku ke sha a rana. Duk da haka, idan yaro yana da matsalar fitsarin kwance ana buÆ™atar mafi yawancin shan ruwan sa ya kasance da safe da farkon rana, amma da yamma sai a iyakance ruwan da yaro zai sha. Ba'a son yawan shan ruwa da yamma idan yaro na fama da fitsarin kwance. A lura cewa, idan  yaro yana shiga harkar wasanni kamar wasan Æ™wallon Æ™afa ko wata wasan da ta Æ™unshi guje-guje a yamma, ba'a iyakance masa shan ruwa da yamma.

2. Hana yaro shan abinsha ko abinci mai É—auke da sinadarin caffeine.

Ana so a hana yaro shan abubuwa masu ɗauke da sinadarin caffeine a kowane lokaci, musamman ma da yamma. Saboda maganin caffeine na iya tayar da mafitsara. Abubuwa masu ɗauke da caffeine sun ƙunshi coffee (kofi), Nescafe da dai sauransu.

3. A tabbatar da yaro yana fitsari a banÉ—aki akai-akai a cikin yini

Yana da kyau a tabbatar da cewa yaro yana amfani da banɗaki wajen yin fitsari a ƙalla duk bayan awa biyu a cikin yini.

4. A tabbatar da yaro yayi fitsari a ƙalla sau biyu a cikin dare kamin ya kwanta bacci.

Yin haka yana tabbatar da cewa yaro bai kwanta da mafitsara cike da fitsari ba

5. Kare yaro daga ƙurajen gaba

Don hana yaro samun Æ™urajen da fitsarin kwance ke haifarwa, yana da kyau a taimakawa yaron yayi wanka ko ya wanke  al'aurarsa kowace safiya, sannan kuma ya cire tufafin da yayi bacci dasu daga zarar ya tashi daga baccin. Hakan yana taimakawa yaro sosai, ba hana Æ™uraje kaÉ—ai ba har ma da tsaftace jikinsa da kuma hana shi warin fitsarin kwance. Bugu da Æ™ari akwai wani man cream da ake iya shafawa yaro a gabansa kullum idan zai kwanta bacci, wanda zai kare shi daga Æ™urajen gaba da kuma wasu mummunan abubuwan da fitsari ke iya haifarwa fatar mutum. Ku nemi shawarar likitocin ku game da man da zakuyi amfani da shi.

Amfani da ƙwayoyin magani

Idan babu wani yanayin rashin lafiya kamar ciwon fitsari, da aka gano shi ne musabbabin fitsarin kwance ga yaranku, babu ainihin buƙatar bada wani magani. Fitsarin kwance yana tafiyar shi a lokacin da yaro ya girma ko da ba'a yi maganin komai ba. Duk da haka, idan bayan yin magana da likita, kuka yanke shawarar yi wa ɗanku magani, akwai magungunan ƙwayoyi da yawa da ake amfani da su.

Idan har likitanku ya gano rashin lafiyar da ya haifarwa yaronku fitsarin kwance kamar irin ciwon fitsari da ciwon sugar toh ya wajaba a fara maganin waÉ—annan cututtuka, idan anci nasarar maganin su toh yaro zai daina fitsarin kwance.

Idan kuma ba'a gano wata cuta da ta haifarwa yaro da fitsarin kwance ba, kuma iyayen suna buÆ™atar a yiwa yaro magani toh akwai magunguna guda biyu da hukumar tantance abinci da magunguna (FDA) ta amince ayi amfani da su don maganin fitsarin kwance.  Magungunan sune:
  • DDAVP 
  • Tofranil. 
Sauran magungunan da ake amfani da su a wasu lokuta don maganin fitsarin kwance sun haÉ—a da:
  • Ditropan  
  • Levsin. (Wannan magani yana da haÉ—ari sosai, idan za'a yi amfani da shi a tabbata Æ™wararren likita ne ya rubuta yadda za'a sha)
A magana ta gaskiya, magungunan ƙwayoyi ba kowa da kowa suke wa aiki yadda ya kamata ba, kuma waɗannan magunguna na iya samun tasirin kawo wata matsala idan har ba'a sha su a bisa ƙa'ida ba. Yi magana da likitan ɗanku don sanin ko maganin ƙwayoyi ya dace da yaronku.

Amfani da na'ura mai Æ™ararrawa a lokacin da yaro ya fara fitsarin kwance 

Saboda yara masu fitsarin kwance, turawa sun ƙirƙiri wasu ƙananan na'urori masu amfani da batir, waɗannan na'urorin ana sanya su ne a cikin wandon yaro ko a jikin pampers ɗinshi lokacin da zai kwanta bacci. Haka zalika, na'urar tanada wani agogo da ake ɗaurawa a hannu wanda ke fitar da sautin ƙararrawa idan yaro ya fara fitsari. Idan yaro yana bacci daga ya farara yin fitsarin kwance wannan na'urar zata gane ta hanyar jin sanyin fitsarin sai ta fitar da wani sautin ƙararrawa (alarm) wanda zai tada yaro daga bacci yaje ban haya yayi fitsarin sa. Idan yaro ya kasance mai nauyin bacci toh ƙarar sautin wannan ƙararrawa ba zai tada shi ba, toh ana buƙatar mamar sa ko wani ya kwanta tare dashi domin ya tada shi daga yaji sautin na'ura.


Babban amfanin wannan na'urar shi ne koyawa yaro tashi yin fitsari a yayin da yake bacci a duk lokacin da yaji fitsarin. Haka zalika tana hana yaro jiƙe makwancinsa da kuma ƙarƙare fitsarin kwance idan ya fara, saboda sautin da zai tada shi yaje banɗaki. Wannan na'urar tanada inganci sosai, saboda idan anyi amfani da ita na wani ɗan lokaci, yaro zai koyi tashi daga bacci da kansa yayi fitsari.

Kammalawa

A nan muka zo ƙarshen wannan rubutu, muna fatar ya amfanar da ku bakin gwargwado. Idan kunji daɗin wannan rubutu kuma kun amfana toh ku faɗamana ra'ayoyin ku akan wannan shafi a cikin akwatin tofa albarkacin baki da ke ƙasa.

Post a Comment

0 Comments