Fitsarin kwance, shi ne yin fitsari a cikin barci ba tare da mutum ya sani ba, normal ne yaro ya dinga yin fitsarin kwance idan yana ƙasa da shekaru 7. Amma yaron da yakai shekara bakwai ana tsammanin ya samu isasshen horon da zai riƙe uzurin fitsari har ya isa gurin da ya dace ya yi fitsarin.
Amma idan yaro ya wuce shekara 7 zuwa kusan 18 yin fitsarin kwance na iya zama sakamakon abubuwa da dama, ciki kuwa harda wasu cututtuka. Za mu É—an yi tsokaci da wasu kamar haka:
1. Idan ya zama mafitsarar yaro ta kasance ƙarama ce toh fa galibi ko da fitsari ya taru lokacin da yaro ke bacci, fitsarin zai yiwa mafitsara sa over har sai ya fitar dashi, mafitsarar mutum takan riƙe aƙalla 400mil na fitsari, idan ta yaron 200mil za ta iya riƙewa kurum in 400 ya taru dole aga yaron yayi fitsarin kwance.
2. Yara masu lalurar da ta shafi ƙugu, misali polio kashin ƙugunsu na iya matse mafitsara ya zaman to nan ma ba sa iya riƙe fitsari da yawa.
3. Idan mafitsarar yaro ba ta riƙa ba, ma'ana tai jinkirin yin ƙwari nan ma tsokokin mafitsarar a natse su ke ba zai iya riƙewa ba, wataƙila sai ya ƙara girma.
4. Sai kuma tsoro: Idan ya zaman to yaro yana cikin stress kusan ko yaushe, shi ma wannan ya kan jya sa yaro yin fitsarin kwance.
5. Ciwon lakka, wato spinal cord idan ta taɓu a wani sashe tun daga ƙwaƙwalwa har zuwa inda ta ƙare aikin ta na lalacewa, hakan zai iya sanadiyyar fitsarin kwance tunda ita ke da alhakin sarrafa mafitsara.
5. Ciwon Suga rukuni na farko: Ga yaran da jikin su baya samar da insulin ɗin da zai rage suga, a ƙoƙarin jiki na kare sauran organ sugar kan canza zuwa fitsari a fitar da ita, nan ma za'a ga yaro na yawan malala fitsari har da fitsarin kwance.
6. Kwayoyin cuta idan suka shiga mafitsara (urinary tract infection) nan ma yaro na iya fama da fitsarin kwance.
7. Sai minshari da É—aukewar numfashi yayin bacci hakan ma na jawo fitsarin kwance.
WaÉ—annan su ne dalilai, ga yaron da abun yaki ci yaki cinyewa in an kai shi asibiti duk zasu binciki wannan sannan su fahimci inda matsalar take a ba shi magani.
0 Comments