MENENE ZIHARI
Zihari wata É—abi’ace da Larabawa keyi tun zamanin Jahiliyyarsu ta farko, don su cutar da matansu.
Da zarar É—ayansu ya gaji da mace, sai ya dube ta yace:
"Kin haramta a gareni kamar yadda gadon bayan mahaifiyata ya haramta gare ni".
"Ko kuma yace mata: Kin haramta a gareni kamar yadda `Æ´ar uwata ta haramta gareni".
Wannan muguwar al’ada na É—aya daga cikin al’adun jahiliyyar Larabawa da suka yaÉ—u a cikin wannan al’umma a yanzu.
Shari’ah ta haramta wannan al’ada da duk wani abu mai kama da ita, da ke cutar da mata.
ALLAH TA'ALAH yace:
"WaÉ—anda keyin Zihari daga cikinsu game da matansu, su matan-nan ba uwayensu ba ne, uwayensu kam sune waÉ—anda suka haife su".
"Suna faɗar abin ƙyama na magana da ƙarya, kuma haƙiƙa ALLAH mai yafewa ne, mai gafara".
[ Alƙur'ani: Mujadalilah Ayata: 27]
Hukuncin duk wanda ya aikata irin wannan laifi a matsayin kaffara, a shari’ar musulunci, shine irin kaffarar wanda ya kashe wani a kan kuskure, ko ya sadu da matarsa a cikin watan azumi da rana.
Kuma haramun ne ya kusanci matar sai bayan yayi kaffara.
ALLAH TA'ALAH yace:
"WaÉ—anda keyin Zihari game da matansu, sannan su koma wa abinda suka faÉ—a, to akwai `Æ´anta baiwa a gabanin su shafi juna".
"Wannan anayi maku wa’azi da shi, Kuma ALLAH mai Æ™ididdigewa ne ga abinda kuke aikatawa"
"To, wanda bai samu abinda zai `Æ´anta baiwa ba, sai yayi azumin wata biyu jere a kafin su shafi juna".
"Sannan wanda bai sami ikon yi ba, to, sai ya ciyar da miskinai sittin".
"Wannan domin kuyi imani da ALLAH da Manzonsa, Kuma waÉ—annan hukunce-hukunce iyakokin ALLAH ne, Kuma kafirai suna da azaba mai raÉ—aÉ—i".
[Mujadilah Aya ta:3-4]
TAMBAYA:
Mutum ne yayi wa matarsa zihari, a maimakon yayi kaffara sai kawai ya sake ta, ya sake wani auren.
Ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.
AMSA:
Auransa na biyun ya inganta saboda basu da alaƙa da juna.
Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutuƙar saki uku ne, to wancan ziharin ya warware amma idan saki ɗaya ne kuma yayi kome, to bai halatta ya taɓa ta ba, har sai yayi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudamah ya faɗa a cikin Al-Mugni.
Saboda haka kaffarar zihari itace 'ƴan baiwa ko mutum yayi azumin wata biyu a jere babu hutu, wato azumin kwana sittin, ko kuma ya ciyar da mutum sittin mabuƙata.
ALLAH shine mafi sani.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.
Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3.
0 Comments