Gabatarwa:
Samun ciki a bayan mahaifa wanda likitoci ke kira da ectopic pregnancy yana faruwa ne a lokacin da fertilised egg (ƙwan mace da ya haɗu da maniyyin namiji bayan saduwa) ya dasa kansa a wani wuri saɓanin cikin kogon mahaifa, haka kuma, kwan ya kyankyashe ya zama ciki, kuma cikin ya cigaba da girma a muhallin da ya dasa kansa.
Samun ciki a bayan mahaifa abu ne mai haÉ—arin da zai iya zama sanadiyar rashin lafiya mai tsanani ko ma yayi sanadin mutuwar mace mai ciki idan ba'a yi saurin gane shi da É—aukar mataki ba, musamman idan cikin ya dasa kansa ne a cikin bututun Fallopian (wanda anan ne mafi akasari), cikin ya kan cigaba da girma ya fasa bututun Fallopian tare da haifar da ambaliyar jini.[¹]
A kasashen da suka ci gaba, tsakanin kashi 1% zuwa 2% na duk masu ciki da aka ruwaito suna É—auke da juna biyu a bayan mahaifa. A kasashe masu tasowa kamar Nigeria adadin samun ciki a bayan mahaifa ga mata masu ciki ya kai 5%.[¹]
Me ke kawo samun ciki a bayan mahaifa?
Har ila wa yau babu tabbacin takamaiman abin da ke kawo samuwar ciki a bayan mahaifa ko da yake an gano wasu abubuwan da ke Æ™ara haÉ—arin faruwar haka. WaÉ—annan abubuwa ko kuma cututtuka masu Æ™ara haÉ—arin samuwar ciki a bayan mahaifa sun haÉ—a da[¹];
- Cutar sanyin mara na PID
- Matar da ta taɓa samun zubewar ciki
- Matar da ta taɓa samun ciki a bayan mahaifa
- Matar da ke da shekaru masu yawa ko da ta dauki ciki (shekaru 35 - 45)
- Cututtukan infections masu biyo bayan zubewar ciki
- Mace mai shan sigari
- Cututtukan infections masu damuwar gaban mace
- Cikin da aka samu da taimakon hanyoyin zamani na assisted reproductive techniques kamar IVF.
- Amfani da robar bada tazarar iyali wadda ake sakawa a cikin mahaifa
- Kumburin fibroids
- Sankarar mahaifa
- Sankarar ovary
- Matar da ta fara jima'i tun tana da ƙananan shekaru
- Matar da ke saduwa da fiye da namiji É—aya
- Matar da aka haifa da matsalolin mahaifa
- Matar da ta samu toshewar bututun Fallopian
Alamomin ciki a bayan mahaifa
- Rashin ganin jinin al'ada: Wannan itace alama ta farko da mace zata fara kokwanton ko ta samu ciki.
- Ciwon mara mai tsanani: Watarana mace ta kan ji wannan ciwon a gefen mara ko ma cikin ciki, ciwon ya danganta da inda cikin yake zaune. A lura cewa, mata suna iya samun ciwon mara a yayin da suke da É—anyen ciki, amma ciwon mara mai tsanani wanda wani lokaci zai iya kai ga kafadar hannu yana iya nuna cikin da aka samu bayan mahaifa yake.
- Zubar jini daga farjin mace: Wasu mata baza su iya bambanta wannan jinin da na al'ada ba, sai dai wannan jinin bai kai yawan jinin al'ada ba. Saboda haka, duk macen da ake saduwa da ita, taji waɗannan alamomi guda uku ya kamata ta garzaya asibiti domin binciken ƙwaƙwaf.
Yadda ake gane ciki yana bayan mahaifa a asibiti
A halin yanzu, a cikin ƙasashen da suka ci gaba, da kuma ƙasashe masu tasowa, ana gane cikin da aka samu a wajen mahaifa ta hanyar yin gwaji guda biyu zuwa uku.
- Gwajin ciki (Pregnancy Test): Wannan gwaji ana yinsa domin tabbatar da mace ta samu ciki ko akasin haka.
- Hoton ultrasound da ake kira Transvaginal Scan (TVS): Wannan wani hoto ne na musamman da ke nuna duk abinda ke cikin mahaifar mace da kuma kunkuminta. Ana yin wannan hoton ne domin duba mahaifa da kuma abin da ke cikinta. Idan har gwajin ciki ya nuna mace na É—auke da ciki amma wannan hoton bai iya nuna komai a cikin mahaifa ba, toh lokacin za'a tabbatar cewa cikin da mace ke dauke da shi yana zaune a bayan mahaifa ko wani wuri na daban. Daganan likita mai daukar hoton zai yi kokarin ya duba wuraren da yake tsammanin cikin zai iya dasa kansa. Wuraren da cikin yafi dasa kansa sune; bututun Fallopian, farfajiyar peritoneum, akan bakin mahaifa da kuma cikin ovary.
- Gwajin gane adadin sinadarin β-hCG a cikin jinin mace; Wannan ba dole bane, yawan sinadarin a cikin jinin mace yana nuna cewa mace tana ɗauke da ciki. Idan sinadarin yakai wani adadi yana kara tabbatar wa likita cewa cikin yana a wajen mahaifa.
Yadda ake maganin cikin da ya zauna a bayan mahaifa
Idan har ba'a yi saurin gane cikin ba har sai da ya fashe a cikin inda ya zauna (wanda mafi akasari yana fashewa ne a cikin bututun Fallopian) toh mace tana zuwa ne a cikin yanayin gaggawa tare da matsanancin rashin lafiya, ciwon ciki da kuma zubar jini daga gabanta.
A irin wannan yanayi ya zama wajibi ayi aikin tiyata cikin gaggawa domin cire wannan ciki da kuma ceto rayuwarta. Haka kuma za'a kara mata jini idan tayi asarar jini mai yawa.[¹][²]
A É—aya bangaren kuma, idan akayi saurin gane cikin mace yana zaune ne a bayan mahaifa ko wani wuri da bai kamata ba. Da farko za'a iya zura masa ido tare da bibiyar sa akai akai da fatar zai gangara ya koma cikin mahaifa. Idan yaÆ™i komawa bayan wa'adin da aka diba ya cika, sai ayi aiki ko ayi wasu alluran da zasu sa cikin ya tarwatse.[²]
Kammalawa
Ectopic pregnancy shi ne samun ciki a bayan mahaifa. Samun irin wannan ciki babbar matsala ce, saboda cikin ba zai iya girma yakai mizanin haihuwa ba. Ya zama wajibi a raba mace da cikin ta ko wane irin hali, saboda barin sa yakan sa ya cigaba da girma har ya fashe cikin ciki ya kawo zubar jini mai matukar haÉ—ari da barazana ga rayuwar mace.
Idan mai karatu na da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba.
Rubutu Masu Alaqa
1. Bushewar Gaban Mace, Rashin Ni'ima Da Kuma Kankancewar Gaba
2. Budewar Gaban Mace Da Kuma Yadda Yake Samun Kari Yayin Haihuwa
0 Comments