Kunne wani muhimmin sashe ne na jikin dan Adam da ya kamata a kula da shi sosai. Kunnen mu na da matukar muhimmanci ga lafiyar mu - amma duk da haka, sau da yawa ba ma kula da su yadda ya kamata.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Maris a matsayin ranar ji ta duniya domin wayar da kan jama'a kan mahimmancin kula da jinsu a duk shekara.
Taken ranar na bana shi ne "Canza tunani: Mu tabbatar da kula da lafiyar kunne da ji a zahiri ga kowa" - domin an gano cewa mutane suna da ra'ayoyi daban-daban da basu da tushe, kunne wanda zai iya lalata jin su.
Wani kiyasi da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewa akalla mutane miliyan 430 a duniya ke fama da matsalar ji, kuma a Najeriya sama da mutane miliyan 20 ne ke fama da wannan matsalar ta rashin ji.
Wasu alkaluman bincike na ƙara nuna cewa adadin masu fama da matsalar ji a duniya yana ƙaruwa kusan kowace rana.
Wasu masana na ganin cewa galibin mutane suna cutar da kunnuwansu da jinsu ba tare da saninsu ba ta hanyar bin wasu hanyoyin da ba su dace ba, musamman kokarin cire dattin kunne ko kuma idan sun ji wani canji ko kuma ƙaiƙayi a kunne.
Kamar yadda likitoci suka bada shawara, kada ku yi ƙoƙarin tsaftace cikin kunnen ku ta hanyar amfani da sandar auduga ko yatsa ko cushe wani abu a ciki - domin yin haka yana da haɗari, yana iya haifar da matsalar ji ko ma fashewar dodon kunne.
Shin Da gaske ne Akwai Datti a Kunne?
Yawancin mutane suna amfani da kayayyaki daban-daban, kamar, sandan auduga, yatsa, karan ashana ko karan tsintsiya don cire wani abu mai danƙo da maiƙo da suke kira dattin kunne.
Amma bisa ga binciken likitanci na zamani, babu buƙatar cire dattin kunne, dattin kunne ba shi da matsala har ma yana da kariya. Allah ya halicci kunne ta yadda zai iya rika tsaftace kansa, saboda haka, babu bukatar mutum ya sanya wasu abubuwa da nufin cire dattin kunne.
Masana sun yi imanin cewa cusa wasu abubuwa a cikin kunne da nufin tsaftace shi yana iya kawowa kunne matsala ta hanyar sanya ƙwayoyin cuta a ciki. Shi wannan abin da yake kama da datti idan aka sanya auduga ko wani abu a cikin kunny - maiko ne ba datti ba. Wannan maiƙon yana kare kunne daga kwayoyin cuta da kuma hana ƙura daga shiga cikin kunne
A wani lokaci mutum ya kan ji kunnen sa na ƙaiƙayi har ma wani lokaci yayi tsammanin wannan dattin kunne ne ya haifar masa da ƙaiƙayin. A'aha! Wannan ba haka bane ƙaikayin kunne na faruwa ne saboda shigar wasu ƙwayoyin cuta a cikin kunne, saboda haka, kuskure ne a sanya wani abu a cikin kunne don cire datti - in ji masan ilimin likitanci na zamani
Don haka, ƙoƙarin cire dattin kunne yayin da yake aiki don inganta lafiyar kunne zai iya haifar da matsala.
Illolin Yawan Ƙwaƙular Kunne
Mutane dayawa sun yi imani da amfani da audugar ƙwaƙular kunne ba ya da matsala, wasu ma na ganin rashin yinsa akai-akai ƙazanta ce. Amma kuma ƙwaƙular kunne yana da illa da har zai iya shafar jin mutum, a bisa mafi ingancin bincike na likitanci
Masana sun tabbatar da manyan matsalolin da kan iya faruwa ga yara da kuma manya masu yawan ƙwaƙule-ƙwaƙulen kunne sun haɗa da wadannan:
- Cusa auduga ko ashana ko karan tsintsiya ko tsinke, ko marfin biro a kunne kan iya huje dodon kunnen ya sa jin mutum ya ragu.
- Amfani da audugu da nufin goge ƙura a kunne kan iya tura ƙurar a can cikin kunnen. Idan ma akwai ƙura a kunne, kunne yana da hanyoyin da zai fitar da ita da kansa, ko ya narkar da ita a cikin maiƙon dattin kunne.
- Idan aka jima ana ƙwakular kunne, hakan kan iya sa kunne ya bushe, domin maikon da ke cikin kunne yana da amfani sosai wajen kare fatar kunnen daga bushewa. Kuma wannan maiƙon kariya ne daga kwayoyin cuta.
- Cusa abubuwa marar tsafta a cikin kunne kan iya daukar miyagun kwayoyin cuta zuwa a cikin kunne kai tsaye.
Masana na ganin cewa idan har kunnen mutum yana yawan ƙaiƙayi ko ciwo ko wani abin da mutum bai lamunta ba, toh abin da ya fi dacewa shi ne ya gaggauta garzaya wa asibiti.
0 Comments