Shanyewar ƙwaƙwalwa shi ake kira da turanci cerebral palsy ma'ana shanyewar ƙwaƙwalwar yara a lokacin da suke jarirai.
Shanyewar ƙwaƙwalwar jarirai yana faruwa ne mafi akasari sakamakon rashin samun isasshen jini da iska zuwa ga ƙwaƙwalwar jariri a lokacin haihuwa. Wannan rashin samun jini da iska zuwa ga ƙwaƙwalwar a lokacin haihuwa shi ake kira da birth asphyxia ko kuma severe perinatal asphyxia, kuma shi ne kan gaba waje kawowa jarirai shanyewar ƙwaƙwalwa.
Matsalar birth asphyxia ta kan faru ne a lokacin haihuwa, daf da za'a haifi yaro ko kuma daga zarar an haife shi. Duk da cewa birth asphyxia tana iya faruwa tun kamin a haifi jariri a lokacin da uwa ke nakuda, amma babbar alamar faruwar birth asphyxia shi ne jariri ya kasa yin kuka daga zarar an haifeshi kuma har yakai akalla kimanin yan mintuna ba tare da yayi kukan ba.
Wajibi ne ga duk lafiyayyen jariri ya kurma ihu yayi kuka daga zarar ya faɗo duniya, Saboda wannan kukan shi ne zai bude masa huhu domin ya iya shaƙar iska wadda zata shiga cikin jinin sa ta zagaya zuwa a ƙwaƙwalwar sa da sauran sassan jiki.
Idan jariri bai samu yin kuka ba bayan haihuwa har na tsawon yan mintuna, huhun sa ba zai iya daukar iskar duniya ba, rashin jini da iska ga ƙwaƙwalwar jaririn yakan sa ƙwaƙwalwar sa ta ji mummunan rauni. Tsananin raunin ya danganta da yawan mintunan da yaro ya dauka bai yi kuka ba. Idan lokacin ya tsawaita yakai na mintuna goma (10 minutes) ya kan sa ƙwaƙwalwar ta shanye ko kuma ta samu mummunan raunin da ba zai taɓa warkewa ba har abada.
Jariran da suka samu wannan matsalar ta birth asphyxia wasun su sukan rasu tun suna jarirai, wasu kuma su kan rayu amma suna tasowa da alamomin shanyewar ƙwaƙwalwa. Tsananin waɗannan alamomin ya danganta da tsananin raunin da ƙwaƙwalwar jariri ta samu.
Alamomin Shanyewar Ƙwaƙwalwar Jariri
Shanyewar ƙwaƙwalwar jariri ya kan sa jaririn ya samu jinkirin iya duk wani abu da ake tsammanin ya iya, ya kan sa yaro ya taso da wauta, ko dolo-dolo ko kuma da wata nakasa a jikin sa. Kadan daga cikin alamomin da yaro ya kan samu sun hada da:
1. Jinkiri a Wajen Girma; Yaro mai shanyewar ƙwaƙwalwa yakan taso da jinkirin iya komai a rayuwa, wani ba zai iya riƙe wuya ba sai bayan shekaru ɗaya zuwa biyu, abinda ya kamata ace ya iya tun yana watanni uku zuwa hudu. Wani ba zai iya zama ba sai bayan shekaru hudu ko biyar, haka iya tsayuwa, tafiya, magana, gane mutane da dai sauransu. Duk yaro yakan iya samun jinkirin su, sai dai jinkirin ya danganta daga wani yaro zuwa wani yaro. (Wannan shi ne babban alama).
2. Naƙasa; Wasu jarirai sukan taso da wata nakasa ko tawaya a jikin su kamar irin, shanyewar hannu, ƙafa ko shanyewar rabin jiki ko ma shanyewar duka ƙafafu da hannuwa.
3. Yaro ya kan taso da wauta da rashin kaifin basira
4. Yawan dalalar yawu
5. Yaro ya kan taso yana yawan yin rashin lafiya akai akai
6. Wani yaro yakan samu tanƙwarewar jiki ko wani sashe na jikinsa
7. Wani jariri yakan taso yana yawan fisge-fisge ko kuma yawan motsa hannuwa da ƙafafu ba tsari
Alamomin da jariri zai nuna sun danganta da tsananin shanyewar ƙwaƙwalwa.
Abubuwan da ke kawo shanyewar ƙwaƙwalwar jarirai
- Rashin jini da iska a ƙwaƙwalwar yaro (birth asphyxia) kamar yadda muka yi bayani a sama
- Shawara (Jaundice): Jaririn da aka haifeshi da ɗorawa idanu da jiki ko kuma ya samu ɗorawar idanu da jiki bayan haihuwa
- Cututtukan infection: Cututtukan infections masu iya shafuwar ƙwaƙwalwar yaro kamar jariri ya kamu da cutar ɗan sanƙarau, kumburin ƙwaƙwalwa (encephalitis) ko kuma ya kamu da wasu cututtuka da ake cewa congenital infections a lokacin da yake cikin ciki.
- Zubar jini a cikin ƙwaƙwalwar jariri
- Raunin kai (Head injury)
Abubuwan hatsari da ke sa jariri ya samu wannan matsalar sun hada da:
1. Jaririn da aka haifa a gida
2. Jaririn da aka dade ana nakuda a wajen haihuwar sa
3. Jaririn da zaren cibiya (umblical cord) ya shakewa wuya a wurin haihuwa
4. Jaririn da nauyin sa a lokacin haihuwa ya wuce Kilo huɗu (4kg)
5. Jaririn da nauyin sa a lokacin haihuwa ya kasa kilo biyu da rabi (2.5kg)
6. Bakwaini (Premature Baby) Jaririn da aka haifa bai cika watanni tara a mahaifa ba.
7. Jaririn da mamar sa ke da ciwon sugar
8. Jaririn da mamar sa ta samu hawan jini a lokacin da take da juna biyu (preeclampsia ko eclampsia)
9. Jaririn da mamar sa ba ta zuwa awon ciki
Wadannan kadan kenan daga cikin abubuwan hatsari da ke iya sanya yaro ya samu shanyewar ƙwaƙwalwa. Kar a manta abubuwan hatsari suna nuna cewa yaro yafi sauran yan'uwansa jarirai yiyuwar samun matsalar, amma ba dole bane ya samu. Wasu kuma basu da abubuwan hatsari ko daya amma zasu iya samun matsalar.
Yadda Ake Maganin Shanyewar Kwaƙwalwa
Shanyewar ƙwaƙwalwar jarirai ba ya da takamaiman maganin da za'a sha a warke. Amma ana neman kulawar asibiti domin inganta rayuwar yaro da kuma taimaka masa a lokacin da yake tasowa.
Ana bukatar bada kulawa ta musamman ta hanyar bada abinci mai gina jiki, yin alluran riga-kafi da kuma kai yaro asibiti akai-akai domin ganin likitan ƙwaƙwalwar yara.
Nassoshi
2. Aisen ML, Kerkovich D, Mast J, et al. Cerebral palsy: clinical care and neurological rehabilitation. Lancet Neurol. 2011;10:844–52.
3. Van Naarden BK, Doernberg N, Schieve L, Christensen D, Goodman A, Yeargin-Allsopp M. Birth prevalence of cerebral palsy: a population-based study. Pediatrics. 2016;137. https://doi.org/10.1542/peds.2015-2872.
4. Oliveira V, Singhvi DP, Montaldo P, Lally PJ, Mendoza J, Manerkar S, Shankaran S, Thayyil S. Therapeutic hypothermia in mild neonatal encephalopathy: a national survey of practice in the UK. Arch Dis Child Fetal Neonatal Ed. 2018 Jul;103(4):F388-F390. [PubMed]
0 Comments