1. Tambaya
Salam Dr barka da safiya dan allah agaya man maganin da zanrika sha yasani kiba wanda ko nadaina sha bazai zama damuwaba agareni.
Amsa
Ya kamata mutane su san cewa wadannan magungunan steroids amfani da su domin yin ƙiba ba ƙaramar katoɓara ba ce, saboda illolin su ya fi amfanin su yawa.
Wasu kuma suna amfani da multivitamins da zasu dinga sanya su cin abinci sosai domin kiba. Wasu suna amfani da supplements, mutane na yin abubuwa da yawa.
Amma a sani cewa babban maganin yin kiba na gaskiya shi ne kwanciyar hankali da chin abinci mai gina jiki yadda ya kamata, idan har kana da jikin yin ƙibar ba makawa zakayi. Idan kuma bakada jikin yin ƙibar kace sai kayi ta hanyar shan wasu ƙwayoyi toh ka saka kanka wata hanyar da ba za ta bulle ba.
2. Tambaya
Amsa
3. Tambaya
Slm Dan Allah inafama da ciwon mara kuma shekera ta ukku ban samu rabo ba.
Amsa
Ya kamata gaskiya kije babban asibiti domin ganin likitocin mata. Yana yiwuwa kina fama da infection ne har yayi sanadiyar toshewar hanyoyin ƙwan da kike samar wa. Kije babban asibiti ayi miki hoto da sauran gwaje-gwaje domin tabbatar da abinda ya kawo miki rashin rabo.
Mai tambayar: Ok tu ngd dama na tabayin scanning sai ya nuna normal
A cikin amsar da na baki shi yasa nace kije babban asibiti, saboda a lokacin da nace hoto ba ina nufin ordinary scanning ba, domin ordinary scanning ba zai nuna duk abubuwan da ake bukata ba. Akwai special hoton da ake kira HSG, wannan shi zai nuna idan akwai wata tangarÉ—a a cikin reproductive tract dinki.
4. Tambaya
Dan allah Dr miye maganin ciwon kafafu, sae naji kafafuna namin tauna, kuma duk lokacin da akayi sanyi Sae su kama ciwo.
Amsa
Ya kana yini kullum kana trekking sannan kazo ka tmby ni maganin ciwon ƙafafu? 😂
Maganin ciwon ƙafafun ka shi ne ka samu ka sarara🌚
Amma a lokacin sanyi duk wani mai ciwon ƙassa yafi ta'azzara a wannan lokaci. So kar ka sabawa kanka da shan magungunan kashe ciwo domin zasu rage maka ciwo ne kawai na wani ɗan lokaci, idan sun ƙare aiki kuma ciwon ya dawo.
Haka kuma magungunan suna da illah idan an dade ana sha, zasu iya saka maka cutar ulcer ko ma su taɓa maka ƙoda idan ka jima kana sha. Amma idan har ciwon ya dame ka, zaka iya samun pain relieving creams kamar neurogelsic cream ka dinga shafawa.
5. Tambaya
Aslm, docter mekekawo ciwan gefen kungu ya ringa rikewa mutum bai iya dukkawa, sanan km tafin kafa yana zafi.
Amsa
Abubuwan da suka fi kawo ciwo a gefen ƙugu ya danganta da gefen hagu ne ake jin ciwon ko gefen dama.
A gefen dama za'a iya samun
1. Infection na ƙodar dama wanda aka fi sani da pyelonephritis, yana faruwa mostly tare da zazzabi, jin zafi yayin fitsari, da sauran alamomin cutar magudanan fitsari kamar yadda muka yi bayani a rubutun mu.
2. Infection na hanta, yana faruwa ne tare da ɗorawar idanu ko shawara, ƙaiƙayin jiki da yawan kasala da kuma sauran alamomin tabuwar anta
3. Infection ko dutse a cikin gall bladder (Ɗatanna). Ciwon ciki ne a gefen dama da ke tashi yana sauka, yana tasowa mafi yawanci idan mutum yaci abu mai maiƙo, yana iya zuwa da ɗorawar idanu
4. Ciwon ulcer shima watarana yakan yi radiating daga tsakiyar kirji ya riƙe maka gefen ciki na dama ko na hagu.
A ɓangaren hagu mafi yawanci infection ne a ƙodar a hagu.
A je asibiti a duba domin gane ko menene.
6. Tambaya
Ngd dr. Meyakamata Me ciwan koda bazai ciba da kuma mai hepatitis B.
Amsa
A fannin abinci mai ciwon koda bayada restrictions dayawa, zai iya chin almost duka healthy abincin da normal individual zai ci, sai dai ana masa gargadi ga shan magungunan na gargajiya da na bature. Kar ya taba shan kowane irin magani ba tare da shawartar likitan shi ba. Saboda akwai magunguna dayawa masu ƙara illata ƙodar.
Tunda kin kawo maganar hepatitis B. Bari in yi sharhi akan wata mas'ala da ta zama ruwan dare game da abincin masu hepatitis B. za ku ga wasu daga zarar ance suna da hepatitis B, sai ace su daina cin duk wani abincin da ke dauke da sinadarin protein, kamar nama, kifi, kwai, wake, awara da dai sauransu. WANNAN BA DAI DAI BA NE KUMA KATOBARA CE, Idan mutum yana da hepatitis ko wane iri ne ba a cewa ya rage chin sinadarin protein har sai hepatitis din ya lalata masa hanta baki daya, ya kai stage inda ake cewa 'cirrhosis' da turanci.
Ko a wannan stage ana cewa ne mutum ya rage chin sinadarin protein amma ba ya daina chi ga baki daya ba. Saboda a wannan stage hantar sa tayi raunin da bata iya sarrafa sinadarin proteins dayawa, overload din wannan sinadarin zai iya haifar masa da wani complication da ake kira H.E.
Protein sinadari ne da jiki ke buƙata dole, wanda kuma rashin sa zai iya haifarwa mutum illar da hepatitis bai haifar masa ba.
Don haka don ance mutum nada hepatitis ba shi zai sa ace mutum ya daina chin abincin da ke dauke da protein ba, akwai ma wasu masana da ke ganin mutum na iya doubling din protein din da yake chi domin ƙarawa garkuwar jikinsa ƙarfin fada da hepatitis.
Bugu da kari, yana da kyau a lura cewa, ba kowane infection na hepatitis B ko C ne ke lalata hanta har ya kai stage din cirrhosis ba, wasu suna da cutar hepatitis B amma har su gama rayuwar su baza su gane ma suna dashi ba, wasu ma ana gano cutar kwatsam yayin da aka je tantance su domin bada jini ga yan'uwansu.
Haka kuma bincike ya nuna cewa fiye da rabi na hepatitis B infection baya kai stage din cirrhosis.
7. Tambaya
Assalamu Alaikum
Barka d yamma dn Allah meyake kawo yawan ciwon mara game ciki qarami
Amsa
A farkon ciki abubuwan da ke kawo ciwon mara su ne kamar haka.
1. Ciki a bayan mahaifa
2. Cutar magudanan fitsari kamar yadda mukayi bayani a dazu
3. Miscarriage
4. PID coexisting with pregnancy kamar yadda muka yi bayani a sama
Da dai sauransu.
Shawara shi ne aje asibiti domin yin hoto a ga me ke kawo ciwon marar.
Kammalawa
Zaku iya shiga WhatsApp group dinmu domin turo mana naku tambayoyi ta hanyar danna hoton WhatsApp da ke hannuku na hagu a ƙasa. Idan kuma group din yana kulle zaku iya turo mana tambayoyin ku ta private message.
0 Comments