Yadda Ake Shirin Saduwar Aure: Abubuwan Da Ya kamata Mata Suyi Kamin Saduwa Da Namiji

Yadda ake saduwa


1. Me Ya Kamata Mace Ta Chi Kamin Saduwar Aure?

Ba ko wane irin abinci mace ya kamata taci ba kamin tayi saduwa da mijinta, domin akwai wasu abincin da ba su dace mace ta chi su ba daf da lokacin da za ta soma saduwa da namiji. Wasu kalan abincin suna iya ragewa mace ni'ima ko kuma su kwantar mata da sha'awa na saduwa ko su kawo mata bushewar gaba, don hake ne ya zama dole mace ta san irin abinci da ya kamata taci kamin gudanar da jima'i.

Abinci mai nauyi bai kamata mace taci ba a  sa'o'i hudu ko uku kamin ta soma saduwa da mijinta a cewar Anna Robensun wata mai illimin girke-girke. A nazarin Mrs. Anna, wata likitan mata, abinci mai nauyi yakan jawo kasala ga mace kuma ya hana ta kuzari a lokacin saduwa, inda ta bada shawarar cewa duk matar data san da akwai aikin saduwa da namiji a gabanta to dole ne ta kasance sa'o'i 6 kamin lokacin da zata sadu da mijinta ba ta chi abinci mai nauyi ba.

Dukkanin masana illimin girke-girke da kayan maƙulashe sun nuna cewa, mace kamin saduwar aure abincin ta ka da ya wuce abinci mara nauyi, kuma ya kasance mai ruwa-ruwa ba busashe ba. Abinci irinsu taliya mai ruwa-ruwa, fate-fate da ire iren su, su ne abinci da mace za ta ci kamin saduwa

Haka kuma kifi ko soyayyen kwai mai ruwa-ruwan wanda bai soyu sosai ba yafi dafaffe amfani a jikin mace kamin saduwa. Haka shima ferfesu da naman da aka gasa mai ruwa-ruwa a jiki yafi tsirai ko balangu amfani a jikin mace kamin saduwa da namiji.

Abubuwan sha irin su madara da zuma, su lemun zaki ko mai tsami, haka su kunun aya ko juice suna da amfani a jikin mace kamin saduwa. Haka kuma abarba, kwakwa, kankana, ayaba da lemun bawo suna da amfani mace ta chi kamin kwanciya da namiji. 

Amma kuma mata su sani cewa, kada ki cika cikin ki sosai da abinci awa daya da rabi kamin soma saduwar aure, shi yasa ake buÆ™atar chin abinci ya kasance shi ne abu na farko da mace za ta fara yi a shirin ta na kwanciya da namiji, domin abinci ya narke kamin lokacin da za ta fara saduwa da maigidan ta. 

Muddin mace ta tunkaro saduwa bayan ta cika ciki taff, toh akwai yiwuwan za ta iya yin amai, haka kuma tana iya gajiya da wuri watakila ma tun kamin mijin nata ya samu gamsuwa da ita wanda hakan kuma illa ne babba.

Wadannan abubuwan ci dana sha da muka ambata a sama dukkanin su suna da matukar amfani da mahimmanci a jikin mace yayin saduwa. Shi yasa dukkannin abincin da muka ambata suna karawa mace ruwa ne da kuma ni'ima a jikinta, wanda hakan zai kara mata jindadin saduwa ita kanta da mijinta. 

2. Yadda ake gyara dakin saduwa

Abu na gaba a cikin jerin abubuwan da mace za ta yi kamin saduwa shi ne ta gyara dakin da zasu yi kwanciya da mijinta domin saduwa bayan ta samu abincin da muka ambata ko masu kama da su tayi kalachi.

Dole ne mace tayi wa dakin kwanciyar aure ko saduwa gyara na musamman ba irin gyran É—akin da take tsammanin zuwan Æ™awaye ko 'yan uwa ko abokan miji ba. 

Dakin kwanciyar aure ko saduwa yana bukatar tsafta kamar kowani ɓangare na gida, haka kuma yana buƙatar a kauda duk wani dauɗa ko abu mai wari, ɗoyi, zarni ko tsami daga cikin ɗakin saduwa.

ÆŠakin saduwar aure baya bukatar fitila mai haske haka kuma yana bukatar mace ta bulbule shi da turare mai Æ™amshin gaske musamman wanda ta san maigidan ta yana sha'awar kamshin sa. 

Haka kuma ana son mace tayi amfani da zanin shimfiÉ—a mai dauke da zanen fulawa ko kuma mai wani alamomi na motsa sha'awa. Shima wannan shimfiÉ—ar dole ne a bishi da turare ko ina har da matashin kai na shimfiÉ—ar.

Wasu masana ilimin saduwa suna ganin cewa yana da kyau mace ta samu wani waÆ™a mai sosa zuciyar masoya ta saka yana tashi kamin wannan lokacin, hakan a cewar su shi ma wani tsimi ne dake ratsa zuciyar ma'aurata tare da kuma motsar da sha'awar su. 

Haka kuma ɗakin saduwa ana bukatar jin sa da sanyi mara cutarwa musamman ga mazan da basu buƙatar sanyi, dole mata su tabbatar da ɗakin da za suyi kwanciyar jima'i ko saduwar aure da mazajen su ba ya dauke da zafi, domin mafi akasarin maza basa buƙatar yin saduwa a yanayi mai zafi ganin saduwa yana haifar musu da yin zufa ko da kuwa ɗakin na da sanyi.

3. Yin Wanka Kamin Saduwa 

Dole ne mace tayi wanka na musamman kamin lokacin saduwa da mijin ta, domin shi wanka na saduwa ya bambanta da sauran wankan da mata ke yi na zuwa kasuwa, unguwa wajen aiki ko sana'a, shi wanka na shirin saduwa, akwai wasu muhimman wuraren da su ne akafi la'akari dasu a lokacin wanka, don haka da zaran an tsaftacesu wankan saduwa ya samu.

A lokacin da mace za ta shiga wankan shirin saduwa da mijinta, dole ta tabbatar da cewa sabulun da zata yi wanka dashi yana da Æ™amshin da mijinta yake so, kada ta sake tayi amfani da wani sabulun da tasan cewa mijinta baya bukatar jin irin Æ™amshin sa, domin hakan yana iya kauda masa sha'awar saduwa da ita gaba daya. 

Yadda ake saduwa

Don haka dole ne mata su fahimci irin sabulun da mazajen su ke so domin yin amfani da shi a wajen wanka kamin fara saduwa. Namiji yana iya kawo wa matar sa sabulun wanka, ba domin shi yana son ƙamshin sa ba, sai don ya fahimci matarsa nada sha'awar yin amfani dashi.

4. Yadda Ake Wankan Fara Saduwa 

Abu na farko shi ne, ki tabbatar da cewa kin wanke bakin ki tsaf da buroshi ko aswaki, ki tabbata babu wani wari da ke iya fitowa daga cikin bakin naki. A lokacin da kika shiga wankan fara saduwa, hamattanki, lungunan kunenki, matsaimatsinki, farjinki da kuma duburanki, ƙasan nonuwanki, sune manyan abubuwa kulawa a lokacinda ki ke wankan shirin saduwa, domin dukkanin wadannan wuraren suna da matuƙar mahimmanci a saduwa. (za ayi bayanin amfaninsu a gaba).

Don haka warin É—aya daga cikin su yana iya hana mijin ki kusantar ki. Saboda haka mata su tana di kayan tsaftace wadannan wuraren na zamani domin yanzu haka ana samun su.

4. Kwalliya kamin saduwa

Bayan mace ta fito daga wankan ta na shirin fara saduwa, abu na gaba dake gabanta a shirye-shiryen ta na kwanciya da mijinta shi ne, kwalliya kamin saduwa. Domin muddin mace bata san yadda zatayi kwalliyar fara saduwa ba, yana da matuƙar wahala ta iya shawo kan mijinta a wannan daren domin yayi kwanciya da ita.

Mafiya yawan mata suna ɗaukar cewa da zaran mace tayi wanka ta wanke waɗancan wuraren da muka ambata a baya shi kenan ta gama mai wuyan a ƙoƙarin ta na motsa sha'awar namiji, ba tare da sanin cewa wanka babu kwalliya maigida ba zai san ma anyi ba.

Kwalliya na shirin fara saduwa shi ma yana da bambanci da sauran kwalliyar da mata ke yi, domin shi wannan kwalliyar akasarin sa anayin sa ne da kayan kwalliyan da suke da Æ™amshi na motsa sha'awar namiji. Kwalliya ne da baya buÆ™atan gazal, jam baki, ja gira, fankeke bare kuma foda a fuska. 

Kawai abin da wannan kwaliyar yake buƙata shi ne ki tabbatar da cewa kina da man sanya baki ƙamshi, tare kuma da samun wata alawa ko chingam mai ƙamshi ki sanya a baki. Haka kuma ki tabbatar da cewa, idan mijin ki baya buƙatar gashi a gaba ki tabbata kin aske a lokacin wanka, idan kuma yana buƙata sai ki shafa masa man gashi mai sheƙi da kuma ƙamshi.

Hamattan ki da kuma matse-matsinki su ma ki tabbatar da cewa sun samu turare mai ƙamshin gaske. Gyara gashin kanki a wannan lokacin ya zame maki dole, domin mace da gashin kanta kawai tana iya ɗimauta namiji tare da motsa masa sha'awar saduwa idan har ta san yadda za ta sarrafashi, don haka yana da kyau mace ta gyara gashin kanta sosai ta hanyar wanke shi da kuma sanya masa man gashi mai ƙamshi irin wanda ta san mijin ta yana buƙatar jin ƙamshin sa ba irin mai warin nan da wasu mata ke sanyawa ba wanda kuma akasarin maza basu buƙatar ƙamshin sa.

Man shafin da zaki shafa a lokacin kwalliyar ki na fara saduwa shi ma abun la'akari ne, dole ne ki tabbatar da cewa man shafin mai sa laushin jiki ne ba mai busar da jiki bane, domin namiji baya buƙatar jin jikin mace a bushe. Haka kuma ki tabbatar da cewa hannun ki kin shafe shi da man shafawa mai laushi domin hannun shi ne sarkin aiki.

5. Ado Kamin Saduwa 

Bayan mace ta kammala kwalliyar ta na shirin fara saduwa, abu na gaba shi ne ado ta hanyar sanya tufafi, domin ita ma saduwa ta na da irin adon daya kamata mata suyi, amma akasarin mata basu da fahimtar hakan. 

Don haka shi ke sa wasu matan bayan sunyi wankan fara saduwa sunyi kwalliya sai kuma su ga mazan basu kula ba, wannan kuwa na faruwa ne saboda rashin ƙarasa wannan kwalliyar da akayi da ado mai kyau.

Adon saduwa ba a sanya masa zobe, sarka ko awarwaro. Haka kuma ba a ɗaura masa atamfa ko sanya masa wando mai tauri irin jeans, abin da adon shirin saduwa yake buƙata shi ne kaya masu nuna tsiraici, kaya masu shara-shara, kayan da zasu fito da nonuwanki a kamar a fili, kayan da mijin ki zai dinga hango kan nonuwanki, kayan da zasu rika fito da kuma nuna motsin ɗuwawunki a duk lokacin da kika motsa.

Ado na saduwa yana son mace ta sanya kayan da baza su danne hakkin nonuwan ta da É—uwawun ta ba idan kina bukatar son juyawa mijin ki. Kaya ne da babu damuwa idan sun fito da sashen cinyoyin ki a fili, ko kuma suna baiwa mijin ki sararin haÉ—a idanuwa da wandon fatarin ki. 

Akwai rigan nono da kuma wandon fatari na mata wanda da zaran mace ta yi adon saduwa dasu kamin mijin nata ma ya matso ya É—imauce, wani ma zai iya yin zuwan farko. WaÉ—annan su ne irin shiga na ado da ya kamata mata su dinga yiwa mazajen su. Haka kuma da akwai tufafi na bacci masu kyau da kuma sauki ga mata domin amfani dasu a lokacin adon su na fara saduwa.

6. Yanayin Lokacin Saduwa 

Saduwa mace da namiji

Abu na ƙarshe a wannan babin kamin fara saduwa da namiji shi ne, ya zama dole mace tayi la'akari da lokacin da ya kamata ta shiryawa yin saduwa, ganin shi lamarin saduwa lamari ne dake buƙatar lokacin da babu wani da zai shiga rayuwar ma'aurata.

Kashi 80 cikin 100 na ma'aurata sun fi son yin saduwa a tsakiyar dare ne domin ganin cewa shi ne lokacin da babu wani da zai shiga rayuwar su, don haka mace ta tabbatar da cewa kamin ta shirya yin saduwa babu wani da zai raba mata hankali. 

Ta tabbatar da cewa idan ita mai shayarwa ce ta shayar da É—anta nono har lokacin da take tunanin ba zai sake tashi ba. Haka kuma idan tana da Æ™ananan yara, ta tabbatar sunyi baccin da baza su sake neman kulawar ta ba. 

Idan tana da baƙi ko ƙawaye da suka kawo mata ziyara na kwana ta tabbatar ta kamala dasu. Haka kuma babu barin waya a kunne ko kuma duk wani abinda ta san cewa yana iya ɗauke hankalinsu a lokacin da suka soma saduwa da mijinta.

Post a Comment

0 Comments