Abubuwa 10 Da Ya Kamata Kusani Game Da Ciwon HIV/AIDS (Ƙanjamau)

Maganin HIV

1. HIV ba cuta bace a karan kanta, a'a, ƙwayoyin halittar virus ne waɗanda suke lalata ƙwayoyin halittar garkuwar jiki (antibodies or immune system), domin hana su yin yaƙi da cututtuka. 

Mutum yakan iya kamuwa da wata cuta kuma ya warke bai ma sani ba saboda ƙwayoyin halittar garkuwar jikin sa sun yi yaƙi da cutar har sun kashe ta bai sani ba. Toh, ƙwayoyin halittar HIV/AIDS suna hana garkuwar jiki yin irin wannan aikin.

2. Idan garkuwar jiki tayi rauni saboda shigar ƙwayoyin HIV/AIDS, toh, cututtuka daban-daban zasu sami damar shiga jikin mutum suyi masa illah. Ma'ana, ba ƙwayoyin cutar HIV/AIDS ɗin ne ke kashe mutane ba, amma suna baiwa cututtuka masu yawa damar shiga cikin jiki har suyi ma jikin illah.

3. Zazzaɓi ba cuta bane mai zaman kan sa. A'a, alamar kamuwa da wata cuta ne. Don haka idan mutum yaji zazzaɓi, toh, shan maganin kashe raɗaɗi kamar paracetamol ba zai wadatar ba. 

Abinda ya dace shi ne a gano matsalar da ta haifar da zazzaɓin kuma a magance ta. Don haka mutum mai HIV/AIDS zai iya jin zazzaɓi iri-iri sakamakon cututtuka iri-iri da suka shiga jikin sa, saboda kowane ciwo da irin zazzaɓin da yake haifar wa. 

A takaice, ba za'a cewa mai HIV/AIDS ga irin zazzaɓin da zaiji ba. Ya danganta ne da irin cutar da ta shiga jikin sa.

4. Suma ƙurajen da za su fitowa mai HIV/AIDS ba za'a iya cewa iri kaza ne kawai ba. Ya danganta ne da irin cutar da ta shiga jikin sa wacce take haifar da ƙuraje.

5. Ƙwayoyin halittar HIV/AIDS suna yaɗuwa ne a tsakanin mutane ta hanyar ruwayen jikin mai HIV/AIDS idan suka hadu dana maras HIV/AIDS din sanadiyyar rauni. Ruwan jikin su ne maniyyin namiji, ruwan saduwar mace, ruwan nono, da jini.

6. Manyan alamomin HIV/AIDS sune zazzaɓi, kaluluwa da ƙuraje.

7. Tsawon lokacin da cutar take bayyana a jikin mutum bayan ya kamu da ita shi ake kira da "window period", kuma yana bambanta a tsakanin mutane, bisa la'akari da abinda suke ci, muhallin da suke zama, karfin garkuwar jikin su, da sauransu. 

Window period din yakan fara daga makonni 3 zuwa 12 ko abinda yafi haka. Idan akayi awon HIV/AIDS a lokacin window period, toh, ba za'a iya ganin sa ba.

8. Awon gano ƙwayoyin halittar HIV/AIDS yana da matakai daban-daban, kuma wani ilimi ne ma zaman kansa.

9. Sau da yawa mutum zai tsalgu da cewa yana da HIV/AIDS, alhalin ba haka bane, damuwa ce kawai ko kuma wata cutar ta daban. Awo ne kawai zai iya tabbatarwa. Ba'a gane cutar a fuska ko a jiki.

10. Akwai cututtuka masu yawa waɗanda sukafi HIV/AIDS haɗari da kuma haifar da matsaloli ga mutum, amma ba'a cika damuwa da magance su ba, kamar ciwon sugar, ciwon hanta, ciwon ƙoda, hawan jini, da sauransu.

A takaice, idan mutum yaji alamomin rashin lafiya, toh, ya tafi asibiti domin ganin likita saboda yayi bincike ya tabbatar da abinda yake faruwa dashi.

Post a Comment

0 Comments