Samun gyambo, ƙurji ko rauni a cikin baki shi ne "mouth ulcer", kuma yana iya samuwa ta hanyoyi daban-daban. Wasu daga cikin su sun haɗa da:
1. Rashin Ci Da Shan Abubuwa Masu Gina Jiki: Rashin sinadarai masu muhimmanci kamar su iron, vitamin B12, ko folic acid yana iya haifar maka da kurajen baki. Bugu da ƙari, rashin isasshen sinadarin iron shi kaɗai yana iya haifar tsagewar kwanar baki (crack on the angle of the mouth)
2. Rauni Ko Karcewa: Misali, idan mutum ya cije kansa da hakori ko ya samu rauni a baki yayin amfani da toothbrush, hakan yana iya jawo masa kurajen baki.
3. Gajiya ko Rashin Barci: Tashin hankali ko rashin yin barci mai kyau yana iya jefa mutum cikin matsalar kurajen baki.
4. Ci Ko Shan Abinci Mai Yaji ko Tsami: Wasu nau'ukan abinci kamar kayan marmari masu tsami (irin su lemon tsami) ko abinci mai yaji suna iya tayar da kurajen baki.
5. Ciwon Ciki (Stomach Ulcer): Wasu mutane masu fama da ciwon ulcer na ciki suna samun kurajen baki mouth ulcer sakamakon ulcer na ciki É—in.
6. Rashin Lafiyar Jiki: Wasu cututtuka ko matsalolin rashin lafiyar jiki suna iya haifar da kurajen baki, kamar cututtukan tsarin garkuwar jiki (autoimmune diseases).
7. Cututtuka Masu Karya Garkuwar Jiki: Waɗannan cututtukan su na sanya kurajen cikin baki har da maƙogwaro sakamakon raunin garkuwar jiki.
Hanyoyin Kariya Daga Ƙurajen Baki
Don gujewa kurajen baki ko mouth ulcer, ga wasu matakai da zaka iya bi:
1. Ci Da Shan Abinci Mai Gina Jiki: Ka tabbata kana samun isassun vitamin da sinadarai kamar vitamin B12, iron, da folic acid a cikin abincin ka.
2. Gujewa Abinci Mai Yaji: Ka rage cin abinci mai yaji ko mai tsami sosai domin ka guji tayar da kurajen baki.
3. Gujewa Tashin Hankali: Ka yi ƙoƙarin sarrafa damuwarka da kuma samun isasshen barci.
4. Kulawa da Tsaftace Baki: Ka riƙa amfani da brush mai laushi don tsaftace haƙora, tare da kurkure bakin ka da ruwan ɗumi mai gishiri safe da yamma.
5. Nemi Shawarar Likita: Idan mouth ulcer ko kurajen baki yana yawan dawo maka bayan daukar matakan da na faÉ—a a sama, toh, yana da kyau kaje asibiti domin likita yayi cikakken gano tushen matsalar, sannan ya É—oraka akan maganin da ya dace.
Ƙurajen baki yana iya haifar da jin ciwo sosai, amma bin waɗannan matakan yana iya taimakawa wajen rage yawan samuwar sa.
0 Comments