Amfani Da Illolin Hanyoyin Tsayar Da Haihuwa Na Har Abada

Assalamualaikum warahmatullah likita barka da warhaka, tambaya zanyi likita ina so idan na haihu in É—inke mahaifar saboda na haifi yara sun ishe ni ga shekaru yanzu ina da arba'in a duniya, toh inason in san miye advantage da disadvantage É—insa a likitance idan bashi da illah zanyi idan akwai illoli kuma a bani shawara don Allah, sannan dole in za ayi dinkin mahaifa sai anyi C's wajen haihuwan karshe? Nagode Allah yabada ikon amsa min tambaya ta.

Amsa


Idan na fahimce ki, abin da kike buÆ™atar yi shi ne ki dakatar da haihuwa gaba É—aya har zuwa Æ™arshen rayuwarki. Toh, a gaskiya wannan shawara ce mai wahalar É—auka, domin mai yiwuwa ne idan mace ko namiji suka É—auki wannan matakin daina haihuwa na har Æ™arshen rayuwa, wani dalili ya taso daga baya wanda za su buÆ™aci haihuwar, sai ya zama babu halin yin hakan. 

Amma bari inyi miki bayanin hanyoyi guda biyu wadanda suka fi shahara wajen dakatar da haihuwa ga mace na din-din-din. Wadannan hanyoyin su ne kamar haka: 

  1. Cire mahaifa
  2. Toshewa ko ɗinke bututun ƙwan haihuwa na fallopian tube

Aikin tiyatar cire mahaifar mace shi ake kira "hysterectomy", kuma iri biyu ne kamar haka:

  1. Cire mahaifa gaba É—aya tare da bakin mahaifa (total hysterectomy)
  2. Cire mahaifa ita kaÉ—ai ba tare da bakin mahaifa ba (sub total hysterectomy)

Duk wanda aka yiwa mace a cikin su, toh, amfani ko illolin da za'a samu iri daya ne.

Amfani na kusa da za'a iya samu shi ne sauÆ™in ciwon mara, zubar jini, laulayin É—aukar ciki ko goyon ciki, da kuma rabuwa da dukkan cututtukan mahaifa. 

Illah ta kusa kuma da za'a samu ita ce ciwo da zubar jini da mace za ta yi fama dashi kafin tiyatar ta warke, da kuma hatsarin yiwuwar lalata halittun da suke kusa da mahaifar a lokacin da ake yin tiyatar.

Amfani na nesa kuma dai-dai yake da na kusa, watau kuɓuta daga cututtukan mahaifa da matsalolin jinin al'ada.

Illa ta nesa kuma ita ce rashin haihuwa har ƙarshen rayuwar mace, sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai wanda zai iya sanya mace taji ta koma tamkar namiji ta fuskar rashin sha'awa, saurin fushi, bushewar gaba, da sauransu. Amma baya hana mijinta ya sadu da ita.

Matan da aka cirewa mahaifa suna yawan samun matsalar bushewar gaba da kuma jin zafi yayin saduwa, dalili shi ne, mafi yawancin ruwan ni'imar mace suna fitowa ne daga mahaifa, kaÉ—an ne ke samo asali daga tantanin halittun fatar farji na ciki da kuma jakar Bartholin gland.

Ɗaure Bututun Ƙwan Haihuwa Na Fallopian Tube

Shi kuwa dakatar da haihuwa ta hanyar yanke bututun ƙwan haihuwa na fallopian tube, shi ake kira da "bilateral tubal litigation" ko "tubal sterilization". Itama wannan hanya ce ta tsayar da haihuwa har abada.

Wajen yin tiyatar, ana É—aure ko kuma a toshe bututun Fallopian tubes ne, wanda ta cikin sa ne Æ™wan haihuwar mace yake biyowa idan ya fito daga cikin jakarsa (ovaries) domin shiga mahaifa. 

Wannan yana nufin idan aka yanke ko kuma toshe bututun, toh, Æ™wan haihuwar mace ba zai iya zuwa wajen da 'ya'yan maniyyin namiji zasu haÉ—u dashi ba balle su Æ™yanÆ™yashe shi. Don haka babu maganar É—aukar juna biyu. 

A kan yi tiyatar ne ta hanyar yin 'yar ƙaramar yanka a marar mace (laparoscopic surgery) sai a tura ƙaramar na'urar ɗaukar hoto (camera) wacce za ta nunawa likita inda bututun fallopian tube ɗin yake, daga nan sai ya sanya ƙaramar wuƙa ko almakashi ya yanke bututun, ko ya ɗaure shi, ko ya toshe shi.

Yadda ake toshe bututun haihuwa


Amfaninsa shi ne mace za ta huta da laulayin É—aukar ciki da goyon ciki. Sannan ba za ta fuskanci matsalolin sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai wanda magungunan tazarar haihuwa suke haifarwa ba kamar zubar jini ko rikicewar al'ada. Haka kuma ba za ta samu matsalolin bushewar gaba ba, saboda mahaifar ta na nan intact. Bayan haka, mace ta huta da kashe kuÉ—in sayen magungunan tazarar haihuwa ko yin allura duk bayan yan watanni.

Muhimman illolin sa kuwa su ne idan aka yi shi, toh, ya zamo din-din-din kenan. Sannan mace tana iya samun matsalar kamuwa da Æ™wayoyin cututtuka a lokacin da ake yin tiyatar, ko kuma zubar jini. 

Bayan haka, an ruwaito cewa wasu mata ƙalilan da ba su kai kashi ɗaya cikin dubu ba, sun ɗauki ciki bayan anyi musu wannan aikin na ɗaure Bututun Fallopian, haka kuma akwai yiwuwar samun cikin bayan mahaifa (ectopic pregnancy), a yayin da daurin ya kasa, tare da yiwuwar canjin zangon al'ada (change of menstrual cycle).

A gaskiya maimakon kiyi amfani da waɗannan hanyoyin dakatar da haihuwa na har abada a kan fasalin kanki, ina baki shawarar kije asibiti wajen ƙwararru a kan tazarar haihuwa, ki faɗa musu damuwar ki, domin suyi miki aune-aune kuma su ɗoraki a kan tazarar haihuwa waɗanda suka dace dake.

Post a Comment

0 Comments