Don Allah Dr menene amfanin namijin goro a cikin jikin mace, kuma mene ne illarsa?
Amsa
Namijin goro shi ne “bitter kola” da harshen turanci ko kuma “garcinia kola” a harshen kimiyya da fasaha. Yana Æ™unshe da sinadaran caffeine, vitamin C, iron, potassium, calcium, protein, carbohydrate, da fats.
A kan wannan dalilin ne masu maganin gargajiya su ke yin amfani da tsiron sa domin warkar da matsalolin gudawa (diarrhea), cutar huhu (bronchitis), cututtukan hanta (liver diseases), ciwon sanyi (gonorrhea), cututtukan kumburi (inflammatory diseases) da sauransu.
Amma duk da wannan amfanin namijin goro, jikin wasu mutane yana bijire masa (allergy) don haka yana iya haifar mu su da illah, kamar É—aukewar barci (insomnia), hawan jini (hypertension), tashin zuciya (nausea), rawar jiki (tremors), da dai sauran su.
Bai kamata mace ta ci namijin goro ba a lokacin da take yin jinin haila saboda caffeine É—in da yake cikin sa zai iya tsananta mata laulayin al’adar. Wani bincike kuma ya nuna cewa idan mace taci namijin goro a lokacin da ta kusa saka Æ™wai na haihuwa (ovulation), toh, maiko da kuma dacin da yake cikin namijin goron zai iya hanata saka kwai.
Amma ga mace mai ciki wanda ya fara Æ™wari, cin namijin goro kaÉ—an yana taimakawa wajen rage yawan tashin zuciya da Æ™warnafi, sa’annan yana gyara mahaifa. Ita kuma mace mai shayarwa, sinadarin É—aci da yake cikin namijin goro zai iya Æ™ara mata ruwan nono. Amma a rika ci kadan ba da yawa ba.
Amfanin namijin goro ga maza shi ne yana haÉ“aka yawan sinadarin testosterone a jiki, kaÉ—an daga cikin ayyukan testosterone su ne Æ™ara Æ™arfin sha’awar saduwar aure, Æ™ara yawan Æ™wayoyin maniyyi, Æ™arfin mazakuta, da karfin Æ™asusuwa.
Sai dai cin namijin goro fiye da Æ™ima zai iya sanya caffeine É—in da yake cikin sa ya ta’azzara ciwon hawan jini da kuma ciwon ido na glaucoma. Wasu mutane sukan haÉ—a namijin goro da mintin Tom Tom a matsayin maganin gargajiya na tari. Wasu kuma suna haÉ—a namijin goro da zuma domin irin wannan dalilin.
A lura cewa, amfanin da muka lissafa a sama ana samun su idan ana chin namijin goro akan ƙima, masana sun ba da shawarar kar a wuce ƙwara biyu a yini. Amma idan ana chin namijin goro fiye da ƙima, akwai hatsarin lafiya dayawa da yakan iya ɗora mutum akai. Munyi bayanin wasu a cikin wannan rubutun Harmful Effects of Bitter Kola To Health.
WalLahu A’lam.
0 Comments