Gabatarwa:
Nonuwa wasu sassan jiki ne masu tudu waÉ—anda su ke fitowa a bisa kirjin mutane da kuma dukkan dabbobi masu shayarwa (mammals). Toh, amma a cikin wannan rubutun za mu yi magana ne akan nonon mutane tare da maida hankali akan nonon mace.
Mutane maza da mata suna da halittar nono, abin da ya bambanta su shi ne nonon namiji baya girma shi kuma nonon mace yana girma. Nonowan mace su na girma ne idan shekarun ta su ka kai lokacin balaga.
Don haka girman su ya ƙunshi churin tsoka (muscler tissues), da kitse (fats), da jijiyoyin jini (arteries and veins), da jakunkunan madara (lobules), da bututun madara (milk ducts), da kan nono (nipples).
Allah ya hukunta nonon mace suyi girma ne saboda aikin shayarwa da mace ke yi idan ta haihu. Shi kuma namiji nonowan sa basu yin girma saboda Allah bai É—ora masa yin wannan aikin na shayarwa ba.
Cututtuka da yawa sukan kama nonon mata da na maza. Amma ciwon nonon mata yafi shahara saboda girma da kuma shayarwa da sukeyi. Don haka wannan rubutun zai fi karkata ne a kan ciwon nonon da yake addabar mata.
Cututtukan Nonon Maza (Male Breast Diseases)
Kadan daga cikin cututtukan nono da suke kama maza sune:
1. Cutar daji (cancer)
Wannan ita ce cutar da take sanya ƙwayoyin halittar jiki su riƙa ninninkawa su na girma babu ƙaƙƙautawa (uncontrollable division of body cells). Saboda nonon namiji baya da tsoka, kitse, da jijiyoyin jini masu yawa, ba'a cika samun cutar dajin nono a maza ba.
Idan daji ya kama nono, toh, yana yaɗuwa zuwa sassan jikin mutum cikin hanzari. Yakan fara daga ƙololo, sai ya kumbure, sai yayi ta girma, sai ya fara zafi, daga nan ya gunɗi ruwa, ya fashe, kuma yayi ta cin jiki.
Amma fa ba duka Æ™ololo ko kumburin nono ga namiji ne yake zama daji ba. Zai iya kasancewa a dalilin kumburin na Æ™wayoyin cuta ne (infection), ko bugewa, ko kumburin nono da ke faruwa ga wasu yaran yayin balaga. Binciken asibiti ne kawai zai tabbatar gaskiyar al’amari.
2. Girman nono (gynecomastia)
Wannan yanayi ne wanda yake sanya nonon namiji ya riƙa girma kamar na budurwa. Yana iya zama na ciwo ko kuma ba na ciwo ba. Na ciwo shi ne wanda ciwon hanta, ko shaye-shayen ƙwayoyi, ko wiwi, ko giya, ko magungunan gargajiya barkatai suke haddasawa. Wanda ba na ciwo ba kuma shi ne wanda taiba ko kiba suke haddasawa, da kuma kumburin nono ga matasa yayin balaga.
3. Zubar ruwan nono (galactorrhea)
Yana faruwa ne idan namiji yana da sinadarin prolactin da yawa a cikin jinin sa. Shi prolactin yafi yawa a jikin mace saboda aikin shayarwa da take yi. Amma ko macen idan tana da shi fiye da ƙima, to, yakan sanya ta rika zubar ruwan nono alhalin ba shayarwa take yi ba.
Cututtukan Nonon Mata
Lokutan da mata su kan fuskanci cututtukan nono sun rabu gida hudu kamar haka
- (1) Cututtukan nono lokacin da mace ba ta da juna biyu
- (2) Cututtukan nono lokacin da mace take da juna biyu
- (3) Cututtukan nono lokacin da mace take shayarwa
- (4) Cututtukan nono lokacin da mace tayi yaye.
Cututtukan nono lokacin da babu juna biyu
Matsalolin nono da mata su ke samu a lokacin da ba su da ciki sun haÉ—a da:
1. Kumburin jijiyoyin kan nono (periductal mastitis)
Wannan yana faruwa ne idan jijiyoyin da suke aikawa da jini zuwa kan nono (nipple) su ka kamu da ƙwayoyin cuta. Hakan zai sanya wurin ya kumbura, launin sa ya koma jazur, kuma yayi ta zugi.
Wani lokaci yakan riÆ™a fitar da ruwa mai jini-jini, ko wani lokaci maras jini. Irin wannan ciwon nonon baya rikiÉ—ewa ya zama daji. Yakan warke ne da kan sa ba sai an sha komai ba. Idan ya ta’azzara, toh, ana iya gasa wurin da Æ™yallen da aka tsoma a cikin ruwan É—umi (warm compression), sannan a je asibiti domin likita ya É—ora mace a kan maganin da ya dace.
2. Ciwon nono lokacin saka ƙwan haihuwa (breast pain during ovulation)
A wannan yanayin mace za ta ji nonowan ta sun cika kamar na mai shayarwa, su na yi mata zugi kaÉ—an-kaÉ—an, musamman nipples É—in ta. Irin wannan ciwon nonon ba’a shan magani domin warkar dashi saboda zai warke da kan sa da zarar ta gama ovulation da kwana 1 zuwa 3.
Idan kuma lokacin ovulation ya wuce amma ciwon bai daina ba, alhalin yana damun mace sosai, toh, tana iya mammatsa nonon da ƙyallen da aka jiƙa shi da ruwan sanyi (cold compression), ko ta sha maganin kashe zugi, (pain reliever), sannan ta sanya rigar nono wadda tayi dai dai da ita domin tayi supporting ɗin nonon.
3. Ciwon nono lokacin jinin al’ada (breast tenderness during menstruation)
Wannan bayanin sa dai dai yake da wanda nayi a sama game da lokacin ovulation. Haka kuma zaku iya danna link É—in da ke sama domin jin cikakken bayanin irin wannan ciwon nono.
4. Cutar daji ta nono (breast cancer)
Wannan bayanin ta dai dai yake da bayanin da ya gabata a kan ciwon dajin nono na maza. Sai dai tafi tsanani ga mata saboda girman da nonon mata yake da shi, tare da kasancewar sinadaran su na estrogen da progesterone suna yawan haifar da sauye-sauye a kan ƙwayoyin halittar nonon su (breast cells).
A kan wannan dalilin ne ake shawartar mata da su guji shan ƙwayoyi da kuma shafa mayuka masu ƙara girman nono domin gwargwadon tasirin su wajen ƙara girman nono (ƙara yawan breast cells), gwargwadon hatsarin da mace za ta fuskanta wajen kamuwa da cutar daji ta nono.
Yafi kyau ga matan da su ke son Æ™arin girman nono da su riÆ™a cin ingantaccen abinci, yin tsafta, da yin atisaye, da kyakkyawar mu’amala da maigida domin cimma burin su. Manyan alamomin cutar dajin nono su ne:
- Ƙololo a hammata
- Ƙololo a nono
- Kumburin nono
- Taurine fatar nono tare da tamuƙewar fatar
- Canjin launin fatar nono
- Fitar jini daga kan nono ko ruwa mai jini-jini
- Caki-caki a fatar nono (kamar bawon lemu)
- Noƙewar kan nono a ciki da
- Kaikayin nono mai naci
Amma samun waÉ—annan alamomin ba ya nufin cewa an kamu da ciwon dajin nono. Binciken likita shi ne zai tabbatar da haka. Don haka a hanzarta zuwa asibiti da zarar anga waÉ—annan alamomin.
5. Ciwon nono sakamakon shigar kwayoyin cuta (Mastitis)
Waɗannan wasu cututtuka ne da ke shafuwar nono a lokacin da ƙwayoyin cutar bakteriya ko wasu ƙwayoyin cuta suka harbi nono. Misali ya ƙunshi breast yeast, breast abscess, da breast tuberculosis. Su ma suna iya bada duk alamomin da muka ambata a sama, amma binciken likita ne kawai zai warware mana zare da abawa.
Ciwon Nono A Lokacin Da Mace Take Da Juna Biyu
Mai juna biyu za ta iya fuskantar duk matsalolin nono waÉ—anda wacce ba ta da ciki take dasu. Amma fitattun matsalolin nono ga mai juna biyu su ne:
1. Ciwon kan nono (sore nipples)
Mafi wannan yana faruwa ne saboda sanya matsattsun tufafi (tight-fitting dresses), karuwar zuban sinadaran estrogen da progesterone a cikin nono da kuma kamuwa da ƙwayoyin cuta (infection). Domin magance shi, ana shawaratar mace da ta daina sanya matsattun tufafi.
2. Kaikayin nono (breast itching) da tsikarin nono (breast tingling).
Su na faruwa ne saboda bijirewar fatar nono daga abin da ba ta buƙata (allergy), da sauye-sauyen sinadarai (hormonal changes), da amfani da ƙwayoyin magani waɗanda likita ya ɗora mace akan su.
Domin magance shi, ana shawartar mace da ta daina amfani da abubuwan da ta fahimci su na haifar mata da wannan matsalar kamar sabulu, turare, man shafawa, magani, da dai sauran su.
3. Tsagewar kan nono (cracked nipple)
Yana faruwa ne saboda bushewar kan nono (nipple dryness) da kuma amfani da matsattsun tufafi masu gugar fatar kan nono (friction). Domin magance shi, ana shawaratar mace da ta riƙa shafa man Vaseline a kan nonon ta. Kuma ta guji sanya matsattsun tufafi.
4. Cikar nono (antenatal engorgement)
Wani lokaci nonowan mai juna biyu sukan fara tara ruwa tun cikin ta yana ƙarami. Don haka akwai yiwuwar ta riƙa samun cikar nono, amma ba mai tsanani ba kamar na wacce take shayarwa.
A wannan yanayin, mai yiwuwa ne mace ta lura da ruwan nono ya riƙa zuba haka kawai (leaking). Bai kamata mace ta damu ba idan haka ya faru. Domin magance wannan, akwai buƙatar mace ta kauce ma taba kan nonon ta saboda gudun zaburar wa (stimulation) na zubar ruwan nono.
5. Bawon kan nono (nipple flakes)
Wannan shi ne fata mai kamar ɓawo wadda take rufe kan nono. Amfanin ta shi ne bayarda kariya ga kan nono. Mata sukan ɓamɓare ta domin suna ganinta kamar datti ce akan nono.
Babu wata illah da ɓamɓare war take haifar wa, amma tana iya sanya ruwan nono ya fara zuba tun kafin a haihu domin ɓamɓare ta yana sanya kofofin kan nono su buɗe.
Ciwon Nono Lokacin Da Mace Take Shayarwa
Mace mai shayarwa tayi tarayya da mace mai juna biyu wajen matsalolin ciwon nono. Wannan yana nufin duk matsalolin nono da mai juna biyu kan iya samu, to, mai shayarwa tana iya samun su.
Bugu da ƙari, cikar nonon mai shayarwa yakan fi tsanani domin tana da jaririn da take shayarwa. Yawan taruwar ruwan nono yana da matukar alaka da yawan tsotson da jariri yake yi.
Ma’ana, da zarar jariri ya zuÆ™e nonon sai wani ya É“uÉ“É“ugo. Saboda haka, idan jaririn bai sha nonon ba domin wani dalili, to, nonon zai cicciko kuma ya haifar mata da zugi da zazzaÉ“i.
A wannan halin ana bada shawarar cewa uwa ta ci gaba da shayarwa akai-akai domin samun sauƙi. Kuma ta tabbatar da cewa sashen nan mai launin baƙi da yake kewaye da kan nono (areola) ya shiga cikin bakin jariri. Idan ba haka ba, to, da wahala yaro ya sami ingantacciyar shayarwa, kuma uwa zata iya samun tsagewar kan nono wanda ake kira mageduwar nono a hausance.
Ciwon Nono A Lokacin Da Mace Tayi Yaye (Daina Shayarwa)
Babbar matsalar ciwon nono ga mata a lokacin yaye itace cikar ruwan nono saboda ba’a baiwa É—an yaye ya zuÆ™e alhalin ya taru. Matsala ce wacce take warware kanta bayan 'yan kwanaki. Domin samun sauÆ™in wannan matsalar, ga wasu abubuwan da mace mai yaye ya kamata tayi:
1. Tayi yaye a hankali ta hanyar rage lokutan bayar da nono maimakon yin yaye farat É—aya.
2. Kada a kai dan yaye wani baƙon wuri daban, yin haka zai cutar da yaron saboda rashin sabo, ita kuma uwar za ta rika samun matsalar ƙaruwar cikar nono a duk lokacin da tayi kewar yaron.
3. Uwa ta inganta tsaftar jikin ta, tufafin ta, abincin ta, da muhallinta.
4. Ta rika amfani da rigar nono wadda tayi mata dai-dai cif-cif.
5. Kada ta sha magungunan antibiotics, in ya zama dole, toh, tayi amfani da magungunan kashe raÉ—aÉ—i kawai.
Kammalawa
Daga Æ™arshe, ya kamata mu fahimci cewa ba za’a iya yin bayanin komai akan matsalar ciwon nono gaba É—aya ba a wannan rubutun, sai dai a wayar mana da kai a kan abubuwan da suka zama wajibi mu san su. Sauran bayanai likitocin mu zasu yi anan gaba InshaAllah.
0 Comments