Assalamu alaikum, Barka da wannan lokaci likita taimakon da ku ke yi Allah ya muku sakayya da gidan aljannah, dan Allah tambaya gareni, anyi min C's yau kwana 40 da yin aikin kuma yaron babu rai amma tun da a kamin gefen cikina yake riƙewa da azabar ciwo, kuma jini baya fita sai wani abu kamar nama shi ma sai ina jawo shi, na koma asibiti nayi musu bayani sun ce zai daina, to yanzu kuma sai jinin yazo da yawa idan nayi motsi kamar ana tunkuɗo shi sosai yau kwana biyar amma baya sauki, wannan C's na uku aka min duka biyun bai min haka ba, dan Allah idan da wata shawara a taimaka min, kayi hakuri na biyo ka private tambayar ce ta yimin nauyi yinta a group a taimaka min a ɓoye sunana.
Amsa
Macen da aka yiwa aikin tiyatar CS (cesarean section) bai kamata ta riƙa fitar da wani abu mai kama da nama daga gaban ta ba, sannan daga baya ta riƙa zubar da jini sosai. Wannan irin fitar nama-naman da kuma jini mai yawa, yana iya zama alamar matsala, kamar ragowar sassan mabiyiya ko uwa (placental tissue), ko kamuwa da cututtukan (infections), ko rashin cikakken warkewa bayan aikin (incomplete healing after the surgery).
Abubuwan Da Ke Kawo Zubar Jini Dayawa Bayan Haihuwa
1. Ragowar mabiyiya a cikin mahaifa (retained placental tissue)
Bayan haihuwa, ko dai ta farji ko ta CS, dole ne a tabbatar dukkan sassan mabiyiya ko uwa (placenta) tarebda dukkan abin da jariri yaje É—auke da shi sun fita. Idan wani É“angare ya rage a cikin mahaifa, zai iya haifar da fitar abu nama-nama daga farji da kuma zubar jini mai yawa.
Wannan abin dake fita mai kama da nama yana iya zama ragowar sassan mabiyiya ne, wanda kuma zai iya haifar da jin zafi ko ciwon ciki ko mara, tare da kumburi, da kamuwa da cututtuka.
2. Kamuwa da Cututtuka (infections)
Kamuwa da cututtuka a mahaifa, kamar kumburin mahaifa (endometritis) ko wurin da aka yanka wajen yin aikin CS É—in, yana iya haifar da fitar wani abu mai wari daga farji, tare da zubar jini mai yawa. Yawanci, zai iya haÉ—uwa da zazzabi, jin zafi, da rashin jin daÉ—in jiki. Yana da muhimmanci ayi maganin cutar da wuri don kaucewa matsaloli masu tsanani.
3. Rashin Komawar Mahaifa Yadda Take Kafin Haihuwa (Subinvolution of Uterus)
Wannan yana nufin mahaifa ba ta dawo matsayin ta yadda ya kamata ba bayan haihuwa. Bayan haihuwa, fitar jariri daga mahaifa ya kan sa mahaifar ta matse ta rage girma sannu-sannu har ta koma yadda take kamin mace ta samu ciki. Rashin matsewar ta da rage girma yana iya haifar da zubar jini mai yawa na tsawon lokaci ko kuma fitar abubuwa kamar nama-nama ko jini mai kauri.
4. Zubar Jini Mai Yawa Bayan Haihuwa (Postpartum Hemorrhage)
Ko da yake yawan zubar jini bayan haihuwa yafi faruwa bayan haihuwa ta farji, amma yana iya faruwa bayan CS ma. Wannan yawanci yana faruwa ne saboda matsaloli irin su rashin tsayawar mahaifa daga miƙewa yadda ya kamata, ragowar gabar haihuwa, ko matsaloli a wurin da aka yi ɗinki mahaifa.
5. Rashin Cikakkiyar Warkewar Gurbin Dinki a Mahaifa (Incomplete Healing of Uterine Scar)
Zubar jini mai yawa bayan CS yana iya zama yana da alaƙa da rashin cikakken warkewar wurin da aka yi dinki a mahaifa. Idan ba'a samu warkewar gurbin ba yadda ya kamata ko kuma akwai jini a cikin mahaifa da ba'a a kula dashi ba, hakan yana iya haifar da fitar abu mai kama da nama-nama daga farji da zubar jini mai yawa.
Dukkan fitar abu nama-nama daga farji da zubar jini mai yawa alamomi ne na matsaloli da ke buƙatar a gaggauta ganin likita akansu. Yana da matukar muhimmanci ki koma asibiti don a dubaki sosai, sa'annan a doraki akan maganin da ya dace.
Rubutu Masu Alaqa
1. Bushewar Gaban Mace, Rashin Ni'ima Da Kuma Kankancewar Gaba
2. Budewar Gaban Mace Da Kuma Yadda Yake Samun Kari Yayin Haihuwa
0 Comments