Mene ne Bushewar Gaban Mace (Vaginal Dryness)
Matuncin lafiyayyar mace shi ne a ko da yaushe gaban ta cikin danshi yake saboda dalili na tsaro daga kamuwa daga cututtukan infection da kuma saka saduwa cikin jindaÉ—i ga mata. Danshi a gaban mace yana faruwa ne ta dalilai masu yawa kamar:
- Zuwan wani ruwa da ke gangaro wa daga cikin mahaifa (uterine secretions)
- Ruwan da tantanin halittun fatar farji ta ciki (vaginal epithelium) ke samar wa
- Ruwan da jakar vestibular glands da jakar Bartholin glands ke samar wa. (Vestibular glands da Bartholin glands wasu ƙananan glands ne nasu samar da wani ruwan ni'ima masu kama da majina a gaban mace.
Waɗannan su ne hanyoyin da ake samun danshi a gaban mace. Idan mace ta shiga cikin yanayi na sha'awar ɗa namiji danshin yana ƙaruwa saboda zubar ruwan zai ƙaru domin shirya mace zuwa ga saduwa.
Mene Kankancewar Gaban Mace? (Vaginal atrophy)
Shi ne raguwar girman ramin gaban mace ko ƙanƙancewar sa tare da bushewar ni'imar ɗiya mace sakamakon rashin sinadarin hormone da ake kira estrogen.
Bushewar gaban mace yana faruwa ne ko dai ta dalilin shekaru, watau idan mace ta kusa daina al'ada al'amarin da ake kira menopouse wanda yana faruwa ne a lokacin da shekarun mace suka kai 45 +/- 2
Alamomin Bushewar Gaban Mace
- Jin kamar wurin ya tsage da kuma kaikayi ciki da wajen gaban mace.
- Jin zafi ko zugi yayin saduwa
- Yawan yin fitsari sama da yadda aka saba
- Yawan samun infection din mafitsara shine UTI's
Abubuwan Da Ke Kawo Bushewar Gaban Mace
- Yawan shekaru kamar maccen da ta haura shekaru 45.
- Shayarwa
- Magunguna: kamar irin su magungunan ba da tazarar haihuwa, magungunan ciwon daji (cancer) da magungunan ciwon damuwa.
- Matan da aka cire wa mahaifa
- Matan da ke da ƙarancin sha'awar jima'i
- Matan dake amfani da sabulu ko wasu chemicals wurin tsaftar cikin gaban su
- Mata masu ciwon sugar ko Sjogren syndrome (wani rashin lafiya ne da ke sa bushewar ido da baki)
Illolin Bushewar Gaban Mace
Bushewar gaban mace yana saka jin zugi da ciwo lokacin saduwa, yana saka ƙarancin sha'awar ɗa namiji sannan kuma yana saka cutar infection ta bacteria ko kuma yeast.
Maganin Bushewar Gaban Mace
Amfani da vaginal moisturizers waÉ—anda sun kasu kashi mai diimbin yawa. Za'a saka can cikin gaban mace don samun danshi.
Daina amfani da sabulu ko duk wani chemical wajen tsaftace cikin ramin gaban mace. Ba'a amfani da sabulu ko wani turare ko chemical a cikin ramin gaban mace, ruwan ɗimi kawai ya isa. Idan ya zama dole sai kin saka sabulu toh ki saka a wajen fatar gaba kawai, kumar ayi amfani da sabulu mai ƙanshi ko mai kaifi.
Yawan shan madarar youghurt, wannan yana ƙara wa mace lafiyayyen halittun yeist da zasu taimaka mata wurin samun ni'ima da kariya daga cututtuka.
Tsawaita wasa da abokin saduwa kafin ya tsunduma daga ciki.
0 Comments