Hanyoyin Maganin Kurajen Fuska Na Tayani-muni (Pimples)

Maganin kurajen fuska

Ƙurajen taya-ni-muni, ko Æ™urajen pimples a turance ko acne bulgaris a likitance suna É—aya daga cikin lalurori masu addabar samari da ’yan mata. 

Suna fara fitowa ne a daidai lokacin balaga, domin a daidai lokacin ne sinadarin nan na testosterone ke yawa a jinin samari maza da kuma wasu kaÉ—an daga cikin mata. 

Wannan sinadari shi ke da alhakin sa maiƙo ya riƙa taruwa a fuska. Idan maiƙo ya taru a fuska sai ƙwayoyin cuta su zo su taru a wurin su kawo ƙurji ta hanyar toshe bakin jakunkuna masu fitar da zuwa da sinadarin sebum.

Hanyoyin kariya daga ƙurajen taya ni muni su ne kiyaye taruwar maikot da ƙwayoyin cuta a fuska da ƙirji. Wannan kan ɗan yi wahala amma ta waɗannan dabaru za iya samun nasara:

1. Rage cin abinci mai maiƙo

Abinci mai maiƙo kamar irin gyaɗa, kitse da dai sauran su, suna ƙara samar da makamashin ƙirƙirar sinadarin testosterone da kuma ƙara maiƙo a fuska, haka kuma idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da matsamin kitchen wipe mai tsafta kafin a ci. Idan an yi haka an rage maiƙon kusan da kashi hamsin cikin ɗari ko ma fiye.

2. Amfani da sabulun kashe ƙwayoyin cuta

Yin amfani da sabulu mai kashe ƙwayoyin cuta (antiseptic soap) wajen wanka ko wanke fuska safe da yamma. Ba'a so a riƙa matse ƙurajen, ko yanka su da reza ko wani abu makamancin haka, saboda hakan kan iya jawo mummunan tabo ko ma shigar wasu baƙin ƙwayoyin juta a jinin mutum, an fi so a bar su su fashe da kansu sai a wanke wurin da sabulu.

3. Cin abinci mai lafiya

Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki akai-akai yakan tsane maiƙon cikin jini ya ƙara ƙarfin garkuwar jiki wajen yaƙar ƙwayoyin cuta.

4. Amfani da man shafawa mai kashe ƙwayoyin cuta

Maganin kurajen fuska na balaga

Ga mutanen da waɗannan dabaru ba su yi musu aiki ba, za su iya zuwa su nemi man shafawa a fuska da ƙirji mai ɗauke da sinadarin benzoyl peroxide su dinga shafawa safe da yamma bayan an wanke fuska.

5. Ganin likitan fata (Dermatologist)

Ga mutanen da waÉ—annan hanyoyin duk ba suyi musu aiki ba, akwai dai magunguna masu karfi har ila yau irin samfurin bitaman ‘A’ da ake badawa a asibiti, akan samu nasara sosai idan aka jarraba wadannan magungunan. Amma ba a bawa masu juna biyu.

Don haka, idan duk hanyoyin da muka ambata ba su wadatar ba, sai an je asibiti an haÉ—a da karbar magungunan kashe kwayoyin cuta da gyaran fata ta hanyar ganawa da likitan fata (Dermatologist).

Post a Comment

0 Comments