Ko Mace Za Ta Iya Daukar Ciki Ta Hanyar Amfani Da Wandon Namiji Da Ke Dauke Da Ruwan Maniyi?

Daukar ciki

Tambayoyi 

1. Wani abu ne ya daure min kai nake son don Allah a wayar min da kai game da shi l. Akwai can wani lokaci a wani group É—in mu na mata, sai wata tace wai Æ™awar ta tayi ciki sanadiyyar sanya wandon yayan ta, duk da cewa a lokacin  anyi ta Æ™aryata ta.

To kawai jiya sai brother na ya bani wani wandon shi na Jessy na saka shi kawai da safe da na tashi sai maganar nan ta group É—in mu ta faÉ—o min a rai sai naji tsoro ya kamani saboda ina kan lokacin ovulation ne duk na kasa samun nutsuwa wallahi. 

Shi ne nace bari na maka bayani ta private don Allah ka taimakeni ka warware min wannan matsalar pls, saboda yana amfani da wandon shi hakanan ya bani kuma nima ina ovulation ruwan nan na fita to ban san ya abin yake ba duk na shiga damuwa wallahi.

Please ka taimake ni kayi min bayani, kuma tsoro naji a raina saboda na taɓa ji anyi irin maganar a group shi yasa na tambaya don naji da gaske ne ko kuwa.

2. Ko mace za ta iya daukan ciki sanadiyyar amfani da wando jiƙaƙƙe wanda yake da maniyi ɗin mijin ta ko kuma ta hanyar amfani da hannu? Ya zama mijin yasa mata hannu alhali akwai sperm ɗinsa a hannun?

Amsa

A haƙiƙanin gaskiya waɗannan maganganun duk tatsuniyar gizo da ƙoƙi ne, hakan ba zai sa mace ta dauki ciki ba, mace ba za ta ɗauki ciki ba saboda hakan bisa dalilai kamar haka:

1. Mace na anfani da lokaci wajen samun ciki akwai iya adadin lokacin da mace ke da damar daukar ciki, lokacin ovulation ka ɗai take iya daukan ciki. Ovulation na da matuƙar amfani a ɓangaren daukan ciki. Koda za a kwana ana saduwa da mace in dai har ba wannan lokacin ba ne b za ta dauki ciki ba.

2. Samun cikin mace na amfani da YAWA KO ADADI. Dole sai namiji ya shigar da wani adadi na ruwan maniyyi a ƙalla sannan zai iya yiwa mace ciki. Maniyyin da zai liƙe a yatsu ko wanda zai rage bayan jiƙe wando ba zai iya hada ƙarancin adadin ruwan maniyyi da za su iya kyankyanshe kwan halitar mace ba da za ta saki a lokacin ovulation.

Duk da cewa ƙwayar halittar sperm ɗaya ce ke ƙyanƙyashe ƙwan mace, amma akwai ƙarancin halittun ruwan maniyyi da ake son su shiga a cikin mace kamin ta dauki ciki, dalili kuwa shi ne, mafi yawancin maniyyin da suka shiga cikin mace sukan mutu ne ba tare da sun samu haɗuwa da ƙwai ba, toh dole sai sun shiga dayawa sannan a samu yiwuwar ɗaya ya haɗu da kwan mace ya ƙyanƙyashe shi har a samu ciki.

Wasu mazan fah duka maniyyin da suka fitar yake shiga a cikin mace amma duk da haka ko tayi ovulation ana iya ƙin samun sa'a ba maniyyin da zai haɗu da kwan, toh balle ɗan ruwan maniyin da aka dangwala da yatsa ko kuma sauran da ya jiƙa wando?

Haka kuma, sauran ruwan maniyyin da ya jiƙa wando, mafi akasarin sperm cells ɗin da ke cikin sa sun mutu, saboda cells din ba sa rayuwa cikin tsananin zafi da iska, soh su kan mutu cikin yan mintuna bayan zama a kan wandon.

Bisa waÉ—annan kai É—ai mace ba za ta É—auki ciki ba gaskiya dan amfani da wandon brother É—inki. 

Post a Comment

0 Comments