Maganin Kara Girman Nono Da Man Shafawa Na Gyaran Nono: Hanyoyin Gyaran Nono A Likitanci

Gabatarwa:

Maganin gyaran nono na shafawa

Nonowa wasu sassan jiki ne guda biyu waÉ—anda su ke tsiro wa a kan Æ™irjin mutane. Duk da kasancewar namiji shi ma yana da nono, toh, amma bashi ake magana a nan ba, zamu karkata zuwa nonon mace su da ke girma. 

Nonon mace halitta ce wadda ta Æ™unshi churin tsoka(muscler tissue), kitse (fats), kananan bututu (ducts) da jijiyoyin jini (veins). Sai dai kitse da jijiyoyi sunfi yawa a cikin sa. Wannan ne ma ya sanya cewa girman nonon mace da laushin sa ya danganta ne da yawan kitsen da yake cikin sa. 

Nonowan mace suna fara girma ne daga lokacin da ta isa mizanin balaga (puberty) wanda yake farawa daga shekara 12 zuwa sama. Nono ya Æ™unshi wasu Æ™ananan jakunkuna dunÆ™ulallu (lobes) kimanin 15 zuwa 20, waÉ—anda su ne su ke samar wa da kuma adana ruwan nono (breast milk). 

Kowace jaka ta ruwan nono tana da bututu waÉ—anda suka haÉ—u da juna, kuma ta cikinsu ne ruwan nonon yake biyowa ya fito waje ta hanyar kan nono (nipple) wanda shi kuma yake a saman nono. 

Kan nono yana kewaye da wani shashi mai duhun launi (areola) kuma akwai wasu Æ™ananan abubuwa a kan sa masu kumburi kamar Æ™uraje (areola bumps). Amfanin wadannan Æ™urajen shi ne su na samarda maiÆ™o wanda yake sanya kan nono ya zama mai laushi kuma ya sami kariya daga Æ™wayoyin cuta (infection). 

Areola yafi amfani a lokacin shayarwa, domin shi ne yake tattaro ruwan nono ya fito da shi waje. Nono yakan samu siffarsa ne ta kasancewa a tsattsaye (breast firmness) idan jijiyoyin sa da tsokarsa su na a manne da juna sosai, kuma hakan yafi samuwa a lokacin Æ™uruciya. 

Domin haka idan shekarun mace suka fara nisa wannan mannewar ta tsoka da jijiyoyi takan rage, daga nan sai nono ya zube yayi sujjada (sagging).

Yadda Nonon Mace Ke Tsokano Sha'awar Namiji

Bincike ya tabbatar da cewa nonon mace yana É—aya daga cikin abubuwa masu matuÆ™ar tasiri wajen É—aukar hankalin É—a namiji zuwa gare ta, musamman a lokacin saduwar aure. Wannan ne dalilin da yasa al’ummomi da yawa suke alaÆ™anta nono da jima’i, ta yadda ba’a cika son ayi magana Æ™iri-Æ™iri a kan nono ba, sai idan ya zama dole. 

Al’ummar hausawa ma tana da wannan fahimtar. Sannan la’akari da tasirin nono ga namiji ne ya sanya mata suke yin Æ™oÆ™arin gyaran nonowan su domin su janyo hankalin mazan su. Wannan al’marin haka yake a tsakanin duk matan duniya ba namu na Nigeria kaÉ—ai ba.

Maganin kara girman nono

Saboda haka mata masu neman maganin girman nono da kuma yadda za suyi gyaran nono ba za a zarge su da yin laifi ba. Abin da su ke buƙata shi ne a wayar musu da kai a ilmance kuma cikin lafazi mai laushi.

Maganin Karin Girma Da Gyaran Nono Na Asibiti 

Maganin girman nono na shafawa

Hanyoyin da mata su ke amfani da su wajen gyaran nono (watau karin girman nono da kuma tsayuwar sa) sune:

1. Kwayoyin maganin girman nono (breast enhancement pills)

WaÉ—annan su ne Æ™wayoyin maganin girman nono da aka sarrafa su a likitance (pharmaceutical drugs), kuma su ne ake kira da  supplements. Mata su na yawan tambaya a kan ingancin su. Kwayoyin maganin girman nono su na É—auke ne da sinadarin estrogen wanda yake Æ™ara girman nono. 

Sauran abubuwan da ake sanyawa sun haÉ—a da barley (sha’ir), fenugreek (hulba), oats (hatsi), palmetto (dabino), dong quai (wani itace ne da ake samunsa a Æ™asar China), blessed thistle, pueraria mirifica, fennel seed, hops, bovine ovary extract (duka ban san sunayensu da hausa ba). 

Bincike ya tabbatar da cewa Æ™wayoyin maganin Æ™ara girman nono da kuma tsayuwar nono su na da illah, musamman idan an daÉ—e ana amfani da su. Misalin waÉ—annan Æ™wayoyin maganin girman nono su ne; 

  • Lady Capsule
  • BustMaxx
  • Curves Capsules
  • Curvinexx
  • Pueraria Mirifica 3000
  • Natural Pueraria Mirifica, 
  • IsoSensuals Enhance da dai sauran su.

2. Mayukan shafawa masu ƙara girman nono (breast enhancement creams)

Wasu daga cikin ire-iren waÉ—annan magungunan shafawa masu Æ™ara girman nono su ne: 

  • Divine Derriere 
  • Breast and Butt Enhancement Cream
  • COS Naturals Breast Plumping Lotion
  • NanoMed Finale Bust Cream
  • Diva Fit N' Sexy Breast Cream
  • True Level Breast Plumping Lotion
  • Must Up Bella Cream Breast Enhance Cream
  • Liduoliya Breast Enhancement Frost
  • Breast Full Intensive Breast Enlargement Cream
  • Miracle Bust Cream
  • Eveline Slim Extreme 4D Intensive Serum.

3. Allurar kara girman nono (breast enhancement injections)

Maimakon shan Æ™wayoyi ko kuma shafa mayuka na gyaran nono, wasu matan su kan yi allura a nonon su. Dalili shine ita allurar tana shiga cikin tsokar nonon ne kai-tsaye domin ta bayar da tasirin da ake buÆ™ata. Allurai da ake amfani da su sun hada da 

  • Botox
  • Vampire Breast Lift
  • Hyaluronic Acid (Ha)-based Dermal Fillers da dai sauransu.

4. Aikin tiyatar kara girman nono (breast enhancement surgery)

Wannan yana nufin yanka nono a cikin É—akin tiyata domin a Æ™ara yawan kitsen da ke cikin sa, ko kuma ayi dashen wata jaka ko balun-balum  wadda take É—auke da ruwa mai kauri (cohesive gel implants) a cikin nonon mace. Balun-balum É—in ce za ta baiwa nono siffar tsayuwa tsaye Æ™yam kamar na budurwa. Anfi yin wannan tiyatar a Æ™asashen turawa, kuma tana da hatsarin haddasa cutar dajin nono (cancer), sannan kuma ga ta da tsada.l sosai.

5. Kara girman nono da hasken na'ura (laser treatment breast lift)

Ana yin amfani da hasken radiation domin a ƙone ƙwayoyin halittar nono matattu (dead skin cells of the breast), domin matattun cells ɗin ne sukan sanya fatar nono ta yankwane, sai ya zube. Idan sun mutu daga nan zasu ba da damar hayayyafar lafiyayyen cells na fatar nono, waɗanda zasu ƙara wa nono girma da kuma tsayuwa.

Nau'in Nonowan Mata

Ire-iren nonon mata


Kowace mace tana da irin siffar nonon da Allah ya halicce ta da shi. Wannan yana nufin halittar nonuwan mata ta bambanta daga wata mace zuwa wata. WaÉ—anda aka fi sani su ne kamar haka:

1. Cikakke kuma kewayayyen nono (round breast)

Irin wannan nonon halitta ne wanda maza su ka fi so, domin yana da ban sha’awa, kuma a tsattsaye yake.

Maganin girman nono ga budurwa


2. Nono É—aya yafi É—aya girma (asymmetrical breasts)

Wannan ba wata matsala bace a likitance, domin dama halittar jikin dan-adam ta wani gefe ta kan É—an fi wani gefe girma, ko da kuwa ba’a ganin haka a zahiri. Abubuwan da su ke sanya nono É—aya yafi girma sosai sun haÉ—a da: 

  • Ciwon nono (infection)
  • Rashin daidaiton sinadarai (hormonal imbalance)
  • Rashin lafiyar halittun da su ke cikin nono (developmental disorders of breast tissues)
  • Rauni a nono (breast injury)
  • Matsalolin shayarwa (breast feeding complications) da dai sauransu. 

Dukkan su waÉ—annan ana iya magance su ta hanyar shan magani, amma banda rashin lafiyar halittun nono, domin shi sai ta hanyar tiyata ake iya magance shi.

3. Nono mai siffar zunguru (tubular breast)

Wannan shi ne nono wanda yake da tsawo kamar zunguru ko shantu maimakon dunƙulewa wuri ɗaya, kuma akwai tazara tsakaninsu, sannan sashen baƙin su (areola) su na da faɗi sosai. Mafi yawan lokaci ɗaya yakan fi ɗaya girma. Irin wannan nonon halitta ne ba cuta take haifar da shi ba, kuma sai ta hanyar tiyata ake daidaita su.

4. Karamin nono (athlethic breast)

Shi ne nono maras girma, wanda da kaɗan ya ɗara nonon namiji girma. Wannan shi ma halitta ne, amma ana iya ƙara masa girma ta hanyar wasa da shi lokacin saduwar aure (stimulation), atisaye (physical exercise), da kuma cin abinci mai gina jiki (balanced diet).

5. Nono fiye da biyu a kirji (supernumerary breasts)

Wasu matan su na da nono uku a ƙirjin su. Wannan matsala ce ta halitta (genetic disorder), kuma tiyata ake yi domin magance ta. Sannan akwai matan da suke da kan nono a cikin hamatar su amma ba za su gane ba sai lokacin da su ke shayarwa domin ruwan nono zai rika fita ta hamatar. Wannan shima ba matsala bane.

Amfani Da Illolin Magungunan Kara Girman Nono

Girman nono

A haÆ™iÆ™anin gaskiya ba za'a ce ba su aiki ba, domin matan da su ke amfani da su suna ganin tasirin su. Abinda magungunan suke yi shi ne suna kumbura tsoka da kitsen nonon ne kawai, sai aga ya Æ™ara girma. Amma daga bisani suna iya haddasa cutar daji ko kuma wasu matsaloli a nono. 

Sannan kuma su na takura fatar nono ne sai a gan su sun cicciko sun yi tsattsaye. Amma da zarar sun gama aikinsu (tunda ba dauwama za su yi ba) sai fatar ta saki, kuma nonon ya ƙanƙance kuma ya sake zubewa. Da wannan masana lafiya su ke ganin ya kamata mata su guji amfani da waɗannan hanyoyin ƙara girman nono, kamar yadda manyan likitocin duniya suke bayar da fatawa.

Kammalawa 

Nonon matan turawa da muke gani a cikin fina-finai ba duka bane na gaskiya. Dayawa daga cikin su implants ne, ma'ana an saka musu balun-balum a ciki. Kuma babu wani nonon da baya faduwa, sai idan lokacin faÉ—uwar sa bai yi ba. 

Don haka bai kamata maza su matsawa mata da cewa sai sun nemi maganin gyaran nono ba. Amma ana iya É—aukar wadannan matakan domin inganta lafiya, siffa, girman nono da cikowar sa:

  1. Yawaita wasannni da nono tsakanin ma’aurata.
  2. Yin atisaye akai-akai.
  3. Cin abinci mai gina jiki.
  4. Tsaftar jiki da tufafi, musamman rigar nono.
  5. Yawaita amfani da rigar nono.
  6. Kauce ma zafin rana.
  7. Kiyaye shan magunguna barkatai ba tare da umurnin likita ba.
  8. Yin ingantacciyar shayarwa ga wacce ta haihu.

Usman Shehu Hassan

Post a Comment

0 Comments