Maganin Matsi Na Asibiti: Tiyatar Tsukewar Gaban Mace

Gabatarwa:

Maganin matsi

Tiyatar da ake yiwa mata domin a matse musu farjin su, ma'ana mashigar farjin mace ya koma ba yada girma ko kuma a matse, ita ce ake kira da "vaginoplasty" a likitanci. Wannan tiyatar ana yin ta ne domin a karfafa ko a tsuke tsokokin farji (strengthening or tightening the vaginal muscles and tissues). 

Manufar yin hakan shi ne domin a inganta gamsuwar jima'i (enhancing sexual pleasure). Wani lokacin kuma akan yi tiyatar ne saboda a kyautata siffar farji (reconstructive or cosmetic purposes). A takaice, ana yin vaginoplasty ne saboda dalilai kamar haka:

1. Gyaran tsokokin farji bayan haihuwa (post-delivery vaginal repair)

Idan mace ta haihu ta gabanta, ko tsokokin farjin su ka bubbuɗe (stretched) ko su ka yi rauni (weakened), hakan yana sanya ƙofa da ramin farjin suyi sako-sako, ma'ana su zamo basu matse ba (decreased vaginal tone and elasticity). A wannan yanayin, vaginoplasty yakan taimaka wajen samar da matsi a farjin.

2. Canje-canjen matsin farji saboda shekaru (age-related changes)

Tsufa yana sanya matsin farji ya ragu, sakamakon raguwar danƙon dake tsakanin tsokokin sa (collagenosis). Hakan yakan sanya mata su nemi ayi musu tiyatar matsi, watau vaginoplasty.

3. Cututtukan shimfiÉ—ar mara (pelvic floor disorders)

Cututtuka kamar zazzagowar sassan jiki da ke cikin mara (pelvic organ prolapse), wanda yake faruwa idan mafitsara (bladder), da mahaifa (uterus), ko uwar hanji (rectum) suka turo bangon farji ta ciki. Wannan yana sanya yin vaginoplasty.

4. Neman kyautata gamsuwar jima'i (enhanced sexual pleasure)

Wasu matan sukan zaɓi ayi musu tiyatar vaginoplasty domin su samar da ƙaruwar gamsuwar jima'i ga mazan su. Dalili shi ne mutane dayawa su na tunanin cewa matsin farji yafi samar da gamsuwar jima'i. Amma hujjojin binciken kimiyya na asibiti ba su tabbatar da hakan ba, saboda gamsuwar jima'i, a kimiyyance, tana da alaƙa da abubuwa masu yawa ne, ba matsin farji kawai ba.

5. Halittar farji wacce ta saɓawa al'ada ko samun rauni a farji (congenital vaginal abnormalities or perineal trauma)

Za'a iya gyara halittar farji wacce ta saɓawa yadda aka saba gani ta hanyar yin tiyatar vaginoplasty, kamar "vaginal agenesis".

6. Canja jinsin namiji zuwa mace (gender transformation surgery)

A Æ™asashen turawa a kan sami maza waÉ—anda su ke zuwa asibiti domin ayi musu tiyatar canza azzakarinsu ya koma farji (gender reassignment surgery or transgender). Anan, za'a iya yin vaginoplasty domin Æ™irÆ™irar farji. 

7. Neman kyautata siffar farji (cosmetic preferences)

Wasu matane ana yi musu tiyatar vaginoplasty domin farjinsu ya canza siffa, saboda haka suna son siffarsa ta koma daidai da na budurwa. 

Shin yawan jima'i ko haihuwa yana sa buÉ—ewar farjin mace har akai ga tiyata?

Maganin matsi na asibiti


Maganar gaskiya ita ce ba dole ba ne ayi wa mace vaginoplasty domin dawo da tsukewar farjin ta, saboda kawai ta taɓa yin jima'i kafin aure ko kuma ta taɓa haihuwa. Buɗewar bakin farji da ramin farji (vaginal laxity) yana faruwa ne sakamakon abubuwa masu yawa, ba lallai yin jima'i ko haihuwa ba. Ma'ana, ana iya samun matan da farjin su yake buɗewa ba tare da sun taɓa yin ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ba. Ga yadda abin yake:

1. Haihuwa (childbirth)

Tsokokin farji suna buÉ—ewa a lokacin da mace za ta haihu, domin bai wa jaririn ta damar fitowa cikin sauÆ™i. Hakan yana haifar da rashin tsukewar farjin. Amma daga baya farjin zai koma ya tsuke yadda yake sannu-sannu, tsananin buÉ—ewar da kuma saurin komawar sa yadda yake kafin haihuwa, yana bambanta a tsakanin mata. 

Mata da yawa suna samun tsukewar farjin su ya dawo yadda yake kafin haihuwa, da kansa ko kuma ta hanyar yin atisayen Kegel (Kegel's exercise). Wannan yana nufin cewa, matan da suke jin cewa farjin su bai koma yadda yake ba ne kaɗai suke buƙatar ayi musu tiyatar vaginoplasty. Sannan yin hakan zai dogara ne ga idan sun fahimci cewa mazan su suna nuna rashin gamsuwar jima'i dasu.

2. Yin jima'i da maza masu yawa (multiple sexual partners)

Wannan ya shafi mata ne masu bin maza da yawa, ko yawan aure-aure. BuÉ—ewar farji baya faruwa saboda wannan dalilin kaÉ—ai. Allah SwT yayi halittar farji ne ta yadda tana iya buÉ—ewa kuma ta matse da kanta gawargwadon yanayin da yake ciki. 

Don haka, yin vaginoplasty ba zai zamo dole ba saboda yawan haihuwa ko yawan yin jima'i. Wannan ya haɗa da matan da suka taɓa yin jima'i kafin aure. Ma'ana, yin jima'i kafin aure shi kaɗai ba zai sanya mace ta bukaci yin vaginoplasty ba domin dawowar matsin farjin ta.

Abubuwan da ke kawo buÉ—ewar farji (Vaginal laxity)

BuÉ—ewar farji yana faruwa ne sakamakon haÉ—akar abubuwa masu yawa, kamar haka:

1. Tsufa (ageing)

Nisan shekaru yana iya haifar da buÉ—ewar farji idan danÆ™on dake rike da tsokokin farji ya rage karfi. 

2. Sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai (hormonal changes)

ÆŠaukewar al'ada (menopause) da sauran sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran hormones na estrogen da progesterone a cikin jiki zai iya haifar da buÉ—ewar farjin mace. 

3. Cututtukan shimfiÉ—ar mara (pelvic floor health)

Raunin shimfiÉ—ar mara sakamakon kamuwa da cututtukan mara yana iya haifar da wannan matsalar. 

Kammalawa 

A taƙaice ana yin vaginoplasty ko kuma tiyatar matsi ne a kan zaɓin mace, amma ba dole bane kawai saboda ta taɓa yin jima'i kafin aure, ko ta taɓa yin jima'i da maza masu yawa, ko ta hayayyafa da yawa, ace dole ne sai tayi vaginoplasty sannan matsin farjinta ya dawo.

Likitocin da suke iya yin vaginoplasty su ne gynaecologists, urologists, da cosmetic surgeons. Cibiyoyin kiwon lafiya waÉ—anda ake yin vaginoplasty a Nigeria sun haÉ—a da teaching hospitals, asibitoci masu zaman kansu, da sauran cibiyoyin kiwon lafiya masu ingantattun kayan aiki. 

Aikin tiyatar vaginoplasty tana da tsada sosai, domin zata iya kamawa daga ₦200,000 zuwa ₦1,000,000 ko fiye da hakan, bisa la'akari da asibitin da kuma kwarewar likitan. Don haka ya kamata mata su lura, idan suka ji kuÉ—in yin vaginoplasty yayi arha da yawa, to, suyi hattara, kila akwai rashin Æ™warewa ko rashin ingancin kayan aikin.

WalLahu A'lam.

Usman Shehu Hassan 

Post a Comment

0 Comments