Shin ko kun san cewa idan jariri na shan nono a lokacin da uwa take kwance akwai hatsari a lafiyar jaririn?
Shin an taɓa gaya muku shayar da yaro a kwance na haifar da ciwon kunne/ruwan kunne? Ku biyo mu sannu a hankali domin ku ji me yake kawo hakan.
Iyayen mu da kakanni idan mace ta haihu musamman haihuwar farko da ake dawowa gida yin jego su na hana shayarwa a kwance sai dai uwa ta tashi zaune komai dare saboda suna ganin ko dabbobi sukan tashi idan za su shayar da Æ´aÆ´ansu, toh ballantana mutane.
Hancı, baki da kogon kunne na tsakiya (middle ear cavity) suna da ta inda suka haɗu gaba ɗaya a cikin kogon pharynx, kogon pharynx ya haɗu da kogon kunne na tsakiya ta hanyar wani bututu mai suna Eustachian Tube, wanda aikın sa shi ne daidaita pressure kunne ta zama dai-dai da ta waje kuma yana tsane ruwa daga kunne na tsakiya.
Shi wannan bututun Eustachian na yara ba ya da girma sannan yafi zama a miƙe kuma ba ya da kusurwa sosai kamar na manya.
Toh, yaro yana shan nono a lokacin da uwa ke kwance, wani sashe daga cikin ruwan nonon do yaro ke tsotsa zai iya samun damar shiga bututun Eustachian a lokacin da yake kan hanyar sa ta shiga cikin ciki.
Hakan zai fara danne dodon kunne ta ciki(medial part of tympanic membrane) wanda hakan zai sa Æ™wayoyin cuta su samu wurin zama sai kunne ya fara ciwo, yaro yayi ta kuka ba gaira ba dalili, idan abin ya ta'azzara yana taÉ“a kunne sannan sai a samu kumburin dodon kunne na tsakiya (otitise media) wanda idan ba’a kula ba kunne zafi iya fara ruwa.
Iyaye a daure a dinga tashi zaune lokacin shayarwa musamman cikin dare saboda kare yara daga cututtukan kunne. Wani lokaci son jiki zai iya sa ku yıwa yaran ku illah da koda ansamu waraka sai an sha wahala.
0 Comments