Gabatarwa:
Hormonal imbalance yana nufin samun rashin daidaituwa tsakanin hormones din mata da hormones din maza a cikin jinin mace.
Nasan wasu za suyi mamaki, nace hormones din maza kuma a cikin jinin mace, tabbas haka ne ana samun hormones din maza a cikin jinin mata, hasalima sai an kirkiri hormones din maza a cikin jinin mata, sannan jikin mace ya mai da su zuwa hormones din mata.
Bugu da kari, ana samun hormones din mata a jikin maza, amma hormones din mata sunfi yawa a jikin mata, haka kuma hormones din maza sunfi yawa a jikin maza. Hormones din mata su ne estrogen da progesterone, hormones din maza kuwa sune testosterone da dihydrotestosterone.
A wajen kirkiran hormones din mata, sai jikin mace ya fara kirkiran testosterone (wanda shi ne babban hormones din maza) sannan ya maida shi zuwa hormones din mata estrogen da progesterone a cikin jini.
Wannan ya kara jaddada mana imanin mu na cewa Allah ya halicci mace daga namiji, saboda waÉ—annan hormones na estrogens da progesterone da ake samowa da ga testosterone su ke kula da sarrafa rayuwar 'ya mace tun daga balagar ta har zuwa lokacin da zata daina yin al'ada.
Alamomin hormonal imbalance
Hormonal imbalance a jikin mata yana faruwa ne a lokacin da aka samu hauhawar sinadarin testosterone a jikin mace ko kuma ƙarancin sinadaran hormones din mata sakamakon rashin mayar da testosterone zuwa hormones din mata na estrogen da progesterone ko kuma wani sashen jiki na mace yana samar da hormones din testosterone fiye da ƙima.
- Manya manyan alamomin hormonal imbalance a jikin mace su ne kamar haka:
- Rikicewar jinin haila, ko tsallaken wata ba al'ada ko jinin haila mai wasa.
- Zubar jinin haila mai É—imbin yawa fiye da yadda aka saba
- Fitowar gashin maza kamar gashin gemu, saje da gashin kirji ga mace
- Murya mai nauyi irin ta maza
- Yawan kurajen fuska na tayani muni na ko kuma pimples wadanda basu jin magani, wata rana kurajen lan iya fitowa har a kirjin mace
- Rashin haihuwa, wasu kuma su na
- Rashin sha'awar É—a namiji
- Jin zafi yayin saduwa
- Bushewar gaban mace
- Ganin zubar ruwan nono ba ciki ba shayarwa.
- Raguwar gashin kan mace
- Yin muguwar kiba
- Da dai sauransu.
Maza duk da cewa su ma suna da hormones din mata amma basi gaye samun hormonal imbalance ba, saboda jikin su baya dogara ga hormones dayawa a magi yawancin rayuwar su.
Amma duk da haka wasu masa suna iya samun matsalar hormonal imbalance musamman ma lokacin da suke balaga, wannan shi ke sa ka ga wani yaro ya fara fitar da nono a lokacin balaga, daga baya kuma bayan ya gama balaga sai hormones din nasa su daidaita, nonon ya É“ace.
Sauran alamomin hormonal imbalance ga mata su ne:
- Muryar mata
- ÆŠabi'un mata kamar yan daudu
- Rashin fitowa gashin gemu, saje ko gashin kirji
- Karancin sha'awa
- Kankancewar gaban namiji
- Da dai sauran su
Yadda ake maganin hormonal imbalance
Yadda za'a magance shi ne aje asibiti a auna dukkan hormonal profile na mace, sannan a dora ta akan supplement na hormones din mata ta yanda zasu rinjaye hormones din maza a jininta.
A lura cewa ba ko wane hormonal imbalance ke bukatar magani ba, sai irin wanda cututtuka kamar PCOS suke kawowa. Hasalima kowace mace zata iya samun hormonal imbalance a wani lokaci a rayuwarta, amma daga baya zai zo ya daidaita.
Haka kuma ana iya samun irin wannan imbalance musamman a lokacin da mace ke yin al'ada koh take daf da farawa, wannan shi ne musabbabin chanjin yanayin da ke faruwa da mata, a irin wannan lokaci, kamar mood swings da kuma bacin rai ba gaira ba dalili.
0 Comments