Ciwon sugar wanda aka fi sani da diabetes da turanci yazama ruwan dare a cikin al'umma a yanzu, in kai baka dashi toh ba za'a rasa wani daga cikin makusanta ko maƙwabta da ke fama da wannan ciwon ba.
Ga abubuwan da yakamata mu sani game da ciwon sugar, dan ceto rayuwan masu fama da ciwon idan ya taso kamin aje asibiti, koda kuwa baku da abun awon sugar bale ku gane tayi yawa ko tayi kadan.
1. Magungunan da suke sha na ciwon sugar suna rage yawan sugar É—in ne a jiki, idan mutum yana da ciwon sugar kashi na biyu, ma'ana type 2 diabetes. Idan kuma ciwon sugar kashi na farko ne (Type 1 diabetes mellitus) ana bashi alluran Insulin.
Amma dukan magungunan da alluran suna rage yawan sugar dake cikin jini ne. Wanda ita wannan sugar ɗin ba'a so tayi ƙasa sosai na tsawon lokaci, kuma ba'a so tayi sama sosai an fiso ta tsaya a tsakiya, tsakanin 7.1mmol/l zuwa 11.1mmol/l a ko yaushe.
2. Idan ku ka san mutum yana da ciwon sugar kuma kuka ganshi ba lafiya har ya suma, ma'ana ya zama unconscious, ko kuka ganshi kamar yana bacci mai matsanancin nauyi, ya kamata ku san abin da zakuyi kamin ku garzaya da shi asibiti, domin a irin wannan yana yi yana buƙatar taimakon gaggawa, za'a iya rasa shi idan aka ce sai an je asibiti sannan za'a fara bada taimako. Saboda haka a irin wannan yanayi:
- Abu na farko ku lura dakyau, idan yana a some kuka ga yana numfashi sama-sama. Wato idan yayi numfashi yanzu sai ya ɗan ɗauki seconds sannan ya sake yin wani, kamar mai ajiyar zuciya, sannan kuma yana jan numfashin da ƙarfi.
- Abu na biyu, idan ku ka je kusa da bakin sa ko hancin sa zakuji numfashin nasa yana warin wani abu kamar takin zamani ko kamar warin fitsari.
Toh wannan sune alamomin da ke nuna sugar sa ta hau sama sosai, kuma har ta haifar masa da wani yanayin gaggawa da ake kira DKA (Diabetic ketoacidosis).
A irin wannan yanayi, kuyi sauri kuje dashi asibiti, in dai asibitin ba nisa sosai take da ba, ko akwai wahalar ganin likita, toh akwai yiyuwar ba zai sami wata babbar matsala sosai ba kamin ku isa asibitin.
Amma idan akwai ma'aikacin lafiya kusa, a kira shi da gaggawa ya saka masa ruwan drip na "NORMAL SALINE" kamar 1 to 2 liters dan a rage yawan sugar ɗin kamin aje asibiti dan gudun ƙaruwar wata matsala. Idan anci sa'a ma da ya samu isasshen ruwan jiki sugar za tayi ƙasa sai kuga ya fara farfaɗowa, toh daga nan kuna iya garzayawa da shi a asibiti cikin sauƙi.
3. Idan kuma sugar ɗin shi tayi kasa ne, sakamakon jin yunwa ko cin abinci kaɗan, ko rashin cin abinci, ko ya motsa jiki dayawa, ko yasha maganin ciwon sugar fiye da ƙima, ko yakamata a rage adadin magungunan da yake sha saboda sugar ta fara ragewa shi kuma bai je yaga likita ba dan ya rage masa magungunan har ta kai ga magungunan suna rage masa sugar fiye da ƙima, ga Alamomin da zaku gane cewa sugar yayi ƙasa sosai:
- Abu na farko, za ku gan shi ya suma ko yana cikin deep coma, bacci mai nauyin gaske kuma bai san inda yake ba
- Na biyu za ku ga numfashin shi, da sauri da sauri ba kamar idan suga tayi yawa ba.
- Na uku za ku ga yana gumi a dukkan jikin shi
- Na huÉ—u ba zakuji wari irin na takin zamani a hancin shi ba ko bakin shi.
A irin wannan yanayi matakin farko da zaku É—auka shi ne;
Idan har yana da sauran hankalin da zai iya shan wani abu a baki, toh, ku yi gaggawar samun lemun kwalba "COCA COLA" mai sugar ba mai bakin marfi ba, NORMAL COCA COLA ɗin da muke sha, mai zaƙi, mai jan marfi, sai a bashi yasha iya shan sa. Ko kuma a jiƙa sugar a cikin ruwa a bashi yasha sannan ayi gaggawar wucewa da shi a asibiti.
Amma idan har yana some sosai, yana cikin deep coma, ba ya da hankalin da zai iya shan wani abu a baki, kar ayi kokarin bashi komai a baki domin zai iya sarƙewa yayi masa wata illah ta daban.
A irin wannan hali, yadda za'a yi shi ne, idan akwai ma'aikacin lafiya kusa a kirashi yayi gaggawar sa masa ruwan drip na 10% DEXTROSE SALINE, idan ba ya da hawan jini. Idan kuma yana da hawan jini sai yasa masa only 10% DEXTROSE WATER, har sai ya farfaÉ—o sai ayi gaggawar zuwa da shi asibiti.
A lura cewa, idan sugar tayi ƙasa sosai tafi saurin halakar da rayuwar mutum ko ta halaka ƙwaƙwalwar shi nan take. Akan idan sugar tayi sama.
4. Mafiyawan mutanen da ke mutuwa sanadiyyar ciwon sugar, ba ciwon sugar ne kaɗai ke kashe su ba, wani ciwo ne ke shigowa a jikin su, sai ya haɗu da ciwon sugar din su haɗa baki su murƙushe mutum. Shi yasa idan mai ciwon sugar yayi korafin wani alamar rashin lafiya a jikin sa, toh dole ne ayi gaggawar nema masa magani. Kar ayi wasa da irin su cututtukan:
- Malaria
- Typhoid
- Chest infection
- Hepatitis
- Urinary track infection (sanyin mara)
- Blood born infections
- Parasitic infections
- Fungal infections da sauran su
Irin wadannan cututtukan duk suna iya kama mai ciwon sugar su yi masa lahani. Sannan akwai buƙatar mai ciwon sugar ya dinga zuwa asibiti akai-akai ko da kuwa lafiya lau yake ji, aƙalla yaji asibiti ganin likita sau ɗaya a wata.
Saboda, idan ba ya zuwa asibiti akai-akai ba lallai bane yan uwan shi su iya gane cewa ba ciwon sugar É—in ne ke wahalar da baban su ba wani ciwon ne daban, wanda in da babu ciwon din da ciwon ba zai sami damar hallaka mutum kai tsaye ba.
Ko kuma waɗannan cututtukan su sanya mutum zazzaɓi sosai har sugar level ɗin jinin shi yayi ƙasa, alhalin yana shan maganin sa dai-dai kuma yana cin abinci dai-dai, kun ga a nan wani ciwo ne daban yazo ya harzuƙa ciwon sugar ɗin, ko yasa sugar ta hau sama ko ta sauka ƙasa.
Kammalawa
Ciwon sugar da ciwon hawan jini cututtuka ne masu buƙatar FULL FAMILY PARTICIPATION, wato kowa da kowa sai ya sa ido kuma da rawar da yake takawa wajen kula da marar lafiyar su. Dan haka hakkin kowa ne yasan wannan
0 Comments