Yadda Jarirai Ke Shan Nono Har Na Tsawon Watanni Shida

Tambaya 

Yadda ake ba yara nono

Aslm Doctors don Allah kuban Shawara na kasance ina goyon "yan biyu, to exclusive breast feeding nake musu, toh yanzu watan su hudu sai mutane suke ban shawara na basu kunu wai yaran sun rame. Ni kuma nafison sukai, 6 months sannan na fara basu amma Kuban shawara me ya dace.

Su fa ruwa da ake cewa kada a ba jarirai har tsawon wata 6, ba wai cutarwa suke yi ba, idan aka bada mai tsafta da kyau, ba abinda hakan zai haifar na matsaloli, sai dai rashin bayarwa yafi tasiri a fagen samar da ingantaccen garkuwar jiki ga yara.

Rashin bayar da ruwa ko wani abun sha da ba ruwan nono ba, na watanni 6 na farko wato shirin exclusive breastfeeding, rashin cika sharruÉ—É—an sa ke sa ana samun matsaloli. 

Yawaita ruwa fiye da ruwan nono, idan ana fifita bayar da ruwa fiye da ruwan nono a rana yaro zai iya kamuwa da ciwon yunwa saboda ruwan mama na É—auke da wasu sinadarai, kamar sinadaran protein, kitse da kuma antibodies waÉ—anda ba'a samun su a cikin ruwa.

Acikin ruwa akwai ɗimbin cututtukan dake yaɗuwa dan haka akwai sauƙin kamuwa da cuta sanadiyar ruwa ga jarirai. Ba lallai mata ko iyalai su iya cike waɗannan sharruɗɗan ba na tsaftace ruwa, mata za su ce ai da ruwan gora ko roba suke anfani to ruwan robar a ina ake ajiye su, lokacin bayarwa da kuma abin da ake bayarwa dashi. Dan haka adai bada fifiko ga bayar da ruwan nono zallah har tsawan watanni 6. Ko banza ruwan nono kashi 75% ruwa ne.

Matakin daya dace shi ne kije dasu asibiti ayi masu awon ƙibar jiki a tabbatar da suna da ciwon yunwa ko a'a, duk maganar mutane ce, idan akwai yunwa a jkin su za a gane a asibiti sannan za'a ɗorasu akan madarar tamowwa wacce ake bayarwa kyauta. Dan haka gaskiya ba zamu baki shawarar ki basu kunu ba a yanzu sai idan babu halin zuwa asibiti.

Lokacin da jariri yakai wata 6 daganan za a fara bashi tsaftataccen ruwa, kunun gyada, kamu ko kuma custard powder har zuwa wata 11. Idan yaro yakai wata 12 za'aci gaba da bashi abinci mai ruwa ruwa, kamar faten doya, dankali da kuma faten wake.

Ba za'a bashi kowane normal abinci na gida ba sai lokacin da yakai wata 15 daganan kam tuwon masara, dawa, shinkafa za a iya bashi lafiya lau.

Post a Comment

0 Comments