Yadda ake kamuwa da cutar HIV/AIDS ta hanyar saduwa

Assalamu Alaikum. Dr barka da safiya dan allah inada tambaya. Likita, shekara 12 baya wata Æ™anwata su ka haÉ—u da "yanfashi a gidan yayar mu, toh Allah bai ba su nasara ba a kanta da tuni sun yi mata fyaÉ—e. 

Sun dai taÉ“a ta amma ba su shiga jikin ta ba, toh shi ne yanzu tayi aure shekara kusan 6, shi ne abin yake faÉ—o mata a rai wai kar taje ko sun saka mata cutar HIV, kuma babu wanda ta faÉ—awa sai ni nima ban daÉ—e da sani ba shi ne nace zan tambaye ka naji. 

Yanzu yaranta biyu, ba ta taɓa jin alamomin wani abu ba kuma mijin ta a matsayin budurwa ya same ta ba ta sani ba ko mutanen suna da cutar HIV. Allah ya taimaka dr ina jiran bayani yanzu haka kuma tana da wani cikin gashi tana shiga damuwa sosai. Dr ina jiran amsa bana so a saka a group.

Yadda ake kamuwa da cutar HIV


Amsa

Kasancewar na bayar da amsar wannan tambayar taki a cikin group ta wannan sigar ba zai zamo wata matsala ba, domin kuwa ni kaɗai ne na ga sunan ki. Sannan dalilin da yasa ake bayar da amsar tambayoyin ku a cikin group shi ne domin sauran members su ƙaru da bayanin da za'a yi.

Kamar yadda ki ka faɗa cewa waɗanda suka yi kokarin yi mata fyaɗen ba su samu damar yin ainihin jima'i da ita ba, toh, hakan yana nufin cewa ba'a sami haɗuwar ruwayen al'aura ko jini a tsakanin ta da wanda yayi ƙoƙarin yin jima'in da ita ba. Haka kuma ba'a samu saduwar al'aurar sa a cikin na ta ba.

Wannan yana nuna cewa babu wani haÉ—arin kamuwa da cutar HIV/AIDS a gare ta, saboda cutar HIV tana yaÉ—uwa ne ta hanyar jini ko ruwayen jiki ko saduwar al'aura da al'aura kai tsaye.

Bugu da kari, kin ce al'amarin ya faru ne tun shekaru 12 da suka wuce, kuma yanzu tayi aure tun shekaru shida da suka gabata, amma kuma har yanzu kin ce ba ta nuna wasu alamomin kamuwa da cutar HIV/AIDS. 

Hakan yana nuna mana cewa ba ta kamu da cutar ba, domin yawanci alamomin kamuwa da HIV/AIDS suna fara bayyana ne bayan sati 4 zuwa sama, bisa la'akari da koshin lafiyar mutum ko ƙarfin garkuwar jikinsa da sauransu.

Amma duk, da haka ba yanda za'a yi mutum ya kamu da cutar HIV/AIDS har yayi shekara 12 ba magani kuma ba ta nuna a jikinsa ba, hasalima, ana tsammanin cutar za ta kashe mutum cikin shekaru 10 bayan kamuwa idan har bai fara shan magani ba.

Sannan kin nuna cewa ta taɓa haihuwa, kuma yanzu ma tana da ciki wata 6. Toh, idan har tana zuwa asibiti wajen yin awon juna biyu na antenatal care (ANC), ya kamata kisan cewa an taba yi mata awon HIV/AIDS.

Saboda a ƙa'idar yin awon juna biyu na antenatal a asibiti, sai anyi ma mai juna biyu awon cutar HIV/AIDS, Hepatitis B da Hepatitis C. Idan har tana da ɗaya daga cikin su, lallai ne ma'aikatan lafiya za su sanar da ita, domin ɗaukar matakan kare ta da jaririn ta daga matsalolin da waɗannan cutuka za su iya haifar wa. Don haka, rashin faɗa mata cewa tana da cutar, ya nuna cewa ba ta kamu da cutar ba kenan.

Haka kuma, ko da ba ta yin awon juna biyu na antenatal, idan dai ta taɓa haihuwa a asibiti, toh shi ma nan ana yi mata awon waɗannan cutuka domin kare domin bin hanyoyin da za'a kare jariri da kuma da kuma masu karɓar haihuwa daga kamuwa daga waɗannan cututtukan.

A bisa ga dukkan alama ta sanya wa kanta damuwa da zullumi ne kawai, shi yasa take ganin kamar tanada cutar. Saboda haka ya kamata ta daina damuwa, ba ta tare da cutar HIV. Fakat.

WalLahu A'lam.

Dr. Usman Shehu

Post a Comment

0 Comments