Gabatarwa:
Nayi wannan rubutun a matsayin bayar da amsa ga wata tambaya a private. Amma sai na ga ya dace in fitar da shi a matsayin rubutu yadda mutane dayawa za su amfana. Ana kiran wannan matsalar ta zubar ruwan nono babu gaira ba dalili da suna galactorrhea da harshen likitanci.
Haƙiƙa matsalar zubar ruwan nono ga budurwa ko yan mata alhalin babu ciki kuma babu goyo tana matuƙar damun matan mu a yau. Babban abin da wannan matsalar take haifar wa shi ne hana mace samun juna biyu. Na tabbata mata da yawa a cikin group ɗinnan waɗanda su ke da matsalar rashin haihuwa, wacce ta shafi lafiyar su, suna da wannan matsalar.
Alamomin Zubar Ruwan Nono Na Hauhawar Prolactin
1. Rashin kauri (watery), ma'ana kaurinsa zai iya zamo wa bai kai na ainihin ruwan nono da jariri yake sha ba.
2. Kauri (sticky or viscous), ma'ana zai iya zamo wa kaurin ruwan nonon da ke zuba yafi na normal ruwan nono, watau mai danƙo.
3. Zai iya zamowa maras launi (colourless) ko ruwan ƙwai (yellowish), ko ruwan ganye (greenish), ko ruwan ƙasa (brownish).
4. Rashin jini a cikin sa (absence of blood), ma'ana idan a ka ga jini yana fitowa daga nono, toh, wata matsalar ce ta daban amma ba hauhawar sinadarin prolactin ba.
5. Zai iya zamo wa yana zuba da kansa ba sai an matsa ba (auto dripping), ko ya riƙa yin yoyo (leaking) idan aka matsa kan nono (nipple stimulation), ko idan aka matsa nonon (hand expression), ko aka sanya matsattsun kaya (tight fitting dresses).
6. Cigaba da zubar ruwan nono bayan yaye (continuation after weaning). Amma wannan ba dole bane ya tsaya ga wasu mata, domin akwai mata da suke yin tazarcen zubar ruwan nono. Ma'ana zai ci gaba da zuba bayan sunyi yaye har sai sun sake samun wani cikin kuma sun haihu.
Don haka ba za'a yi saurin sanya wannan a cikin matsala ba, sai idan É—aukewar haihuwa ta biyo bayan zubar nonon. Daga nan sai aje asibiti domin likita ya sanya ayi awo a tabbatar da abin da yake faruwa.
Abubuwan Da Ke Kawo Zubar Ruwan Nono Ba Ciki Ba Goyo
Idan mace ta ga ruwan nono yana mata zuba kuma babu ciki ko goyo, toh, tana da matsalar hauhawar sinadarin hormone na prolactin ne a jikin ta, wanda ake kira "hyperprolactinemia" a likitanci.
Shi wannan sinadarin hormone na prolactin aikin sa shi ne bada umurni zuwa go nonowan mace domin su samar da madara. Hauhawan wannan sinadarin shi ke sa nonowa ya samar da madara har ruwan nonon su fara zuba ko da ba ciki ba goyo.
Akwai matsaloli masu yawa waÉ—anda su ke haddasa hauhawar wannan sinadarin hormone, kamar haka:
1. Rashin daidaituwar sinadaran hormones a jinin mace (Hormonal Imbalance)
Almost ko wace mace ta kan samu matsalar rashin daidaituwar sinadaran hormones a wani lokaci na rayuwar ta, rashin daidaituwar sinadaran yana nufin hauhawar wasu sinadarai fiye da ƙima da kuma ƙarancin wasu sinadaran.
Wannan matsalar tafi aukuwa ga mata masu tashen balaga da kuma manyan mata da suka kusa daina yin al'ada. Haka kuma mata masu wasu cututtuka kama cutar polycystic ovarian syndrome su na yawan samun rashin daidaituwar sinadaran hormones.
Hauhawar sinadarin hormone na prolactin, sakamakon wannan rashin daidaituwar hormones ya kan sa mace ta fara ganin zubar ruwan nono ba gaira ba dalili, haka kuma yakan iya kawo mata É—aukewar al'ada ko kuma rikicin jinin haila.
2. Tsotsar nono da yawan shafa nono
Tsotsar nono da yawan shafa shi yana sanya ƙwaƙwalwa fahimtar cewa ana son shan ruwan nono, don haka ƙwaƙwalwa za tayi umurni da samar da ruwan nono idan ana yawan tsotsa shi ko shafa shi, musamman kan nono.
3. Ciwon sankara na jakar pituitary (pituitary adenoma).
Jakar pituitary ko kuma pituitary gland wani muhimmin gland ne da ke ƙarƙashin ƙwaƙwalwa yana samar da wasu muhimman sinadaran hormones domin sarrafa ayyukan jiki. Sashen jakar pituitary na gaba, shi ne keda alhakin samar da wannan sinadarin hormone ma prolactin.
Ciwon sankara ko ciwon dajin jakar pituitary yana sanya wannan jakar ta ƙara girma ta kama fitar da wannan hormone na prolactin fiye da ƙima, wannan zai sanya hauhawar wannan hormone a cikin jini da kuma zubar ruwan nono.
Bugu da kari, ciwon dajin jakar pituitary yana sanya matsanancin ciwon kai, gani dushi-dushi, ganin juwa, yawan amai tunda safe da kuma rikicewar al'ada.
4. Rashin yin ayyukan jakar hypothalamus yadda ya kamata (hypothalamic dysfunction).
Ita jakar tana cikin ƙwaƙwalwa ne, kuma ita ce cibiyar daidaita ayyukan jiki (body functions coordinating center). Ita ce ke da alhakin kula da jakar pituitary.
5. Karancin sinadarin thyroid a cikin jiki (hypothyroidism).
Ƙarancin sinadarin hormone na thyroid wanda jakar thyroid da ke ƙarƙashin wuya take samarwa shi ma yana sanya zubar ruwan nono ba dalili. Sinadarin hormone na thyroid yana da muhimmanci wajen sarrafa ayyukan jiki da girman jiki. Ƙarancin sa kan iya kawo maƙoƙo a wuya, rashin kuzari da kuma zubar ruwan nono.
6. Laulayin amfani da magunguna (medication side effects)
Wasu magunguna, kamar iri magungunan bada tazarar haihuwa suna iya sanya zubar ruwan nono ba ciki ba goyo. Sauran magungunan da kan iya kawo zubar ruwan nono, sun haÉ—a da:
- Magungunan da ake amfani dasu wajen magance cutar hauka (antipsychotics)
- Magungunan cutar damuwa (antidepressants)
- Maganin olsa na cimetidine
- Maganin hawan jini na Aldomet
- Da dai sauran su
7. Cututtuka
Cututtuka misali ciwon koda, ciwon hanta da ciwon farfaÉ—iya duk suna iya sa mace zubar ruwan nono ba dalilin komai.
Yadda Ake Maganin Zubar Ruwan Nono
Ana magance matsalar zubar ruwan nono ne bisa ga la'akari da abubuwan da su ka haddasa shi. Idan anyi gwaji an tabbatar da lallai akwai hauhawar sinadarin hormone na prolactin, toh, babban maganin sa shi ne yin amfani da rukunin magunguna waÉ—anda ake kiran su a jimlace "dopamine antagonist". Kamar su bromicriptine da cabergoline, waÉ—annan magunguna suna da tasiri wajen rage prolactin da kuma tsayar da zubar ruwan nonon.
Mai yiwuwa ne idan likita ya ɗora mace a kan magungunan tsayar da zubar ruwan nono ta ga an ɗauki tsawon lokaci bai tsaya ba. Toh, sai tayi haƙuri ta cigaba da bin umurnin likitan. Amma idan duk magungunan da aka ɗorata a kansu ba suyi tasirin da ake buƙata ba, zaɓin da ya rage ga likita yayi amfani dasu sune:
1. Kara yawan magungunan da ya ɗorata akansu (dosage adjustment). Misali, idan da yace tasha 2.5 mg (kwaya daya) kenan na bromicriptine, toh yanzu yana iya cewa tasha 5 mg (kwaya biyu). Dalili shi ne yana yiwuwa ƙwayoyin sankara waɗanda suka haddasa ciwon 2.5 mg bazai iya yin tasiri akansu ba sai an kara zuwa 5 mg. Ko kuma ya kara mata adadin lokacin shan magani. Misali, idan da yace tasha sau ɗaya ne a rana, to, yanzu yana iya cewa tasha sau biyu a rana.
2. Canja mata maganin (switching medications). Akwai magunguna masu yawa waÉ—anda ake yin amfani dasu wajen magance matsalar zubar ruwan nono, kuma tsarin aikinsu (line of action) yana da bambanci. Domin haka, likitan zai iya canjawa mace maganin wanda yake da tsarin aiki na daban. Zai yiwu a dace.
3. Yin haÉ—akar magunguna (combining drugs), ta hanyar game magunguna waÉ—anda tsarin aikinsu ya bambanta. Misali, likita yana iya haÉ—awa da magungunan ciwon nono na matan da suka kai shekarun daina al'ada (menopause) wadanda ake kira "aromatase inhibitors", kamar letrozol.
4. Yin tiyata (surgery) domin cire karin sankarar pituitary da ya haddasa cutar zubar ruwan nonon. Amma wannan shi ne matakin ƙarshe, domin ba'a yinsa sai dukkan magunguna sun gagara aikin da ake so.
5. Yin amfani da haske (radiosurgery) a haska ƙwayoyin cutar da suke haddasa ciwon domin a kashe su.
6. Likita ya shawarci mace da ta canja tsarin rayuwar ta, ta hanyar daina yawan motsa kan nonon ta (nipple stimulation) wanda take yi ita da kanta ko kuma lokacin mu'amalar aure. Sannan ta kaucewa cin kayan da zasu sanya ta ƙiba kamar kayan zaki, da maiƙo, da kayan gwangwani, da sauransu.
Zubar ruwan nonon da mace zata gani kuma ta É—auke shi a matsayin hauhawar sinadarin prolactin ne ya kawo zai iya zamowa da daya daga cikin wadannan siffofin.
Kammala
Daga karshe, kada wata member mai matsalar zubar ruwan nono tace zata dora kanta a magani. A tafi asibiti.
0 Comments