Gidauniyar koda ta kasa-da-kasa a ƙarƙashin Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutune miliyan ɗari takwas da hamsin (850) ne ke fama da ciwon koda a faɗin duniya a yau.
- 1. Tace ko wanke jini daga guba da sauran gurɓatattun sinadarai da jiki yake samarwa.
- 2. Taimakawa wajen samar da ƙwayoyin halittun jini jajaye (Red Blood Cells)
- 3. Daidaita ruwan jiki da samar da fitsari.
- 4. Daidaita hawan jini, da dai sauran su.
- Daga cikin hanyoyin kariya daga ciwon koda sun haÉ—a da:
1. Shan Isasshen Ruwa
Masana kiwon lafiyar koda sun bayar da shawarar shan ruwa da zasu kai yawan aƙalla lita 2 zuwa 3 a kowacce rana. Shan isashshen ruwa na taimaka wa aikin koda wajen wanke ko tace jini da ruwan jiki daga guba da sauran gurbatattun sinadarai domin fitar da su zuwa cikin fitsari.
2. Chin Lafiyayyen Abinci
Chin lafiyayyen abinci kamar ganye, 'ya'yan itatuwa, kayan marmari, wake, hatsi, madara mai ƙarancin daskararren mai, da makamantansu. Haka kuma, akwai bukatar rage chin jan nama, sarrafaffen abinci, da kuma gishiri.
Sai dai, an lura cewa kaso uku cikin huɗu watau (3/4) na yawan gishirin da mutane ke ci ba sa sanin suna ci. Saboda ana zuba gishirin ne tun lokacin da ake sarrafa abin ci ko abin sha. Saboda haka, abu ne mai matuƙar wahala ka iya gane yawan gishirin da ka sha a kowacce rana.
- Maggi (musamman farin magi)
- Burodi
- Youghurt
- Lemun kwalba/gwangwani/roba
- Sarrafaffen abinci da ke zuwa ƙunshe a leda, gwangwani ko roba.
- Da dai sauransu.
3. Ƙauracewa Shan Tabar Sigari
Shan tabar sigari na iya daƙile aikin magungunan hawan jini da kuma ƙara tauri da matsewar jijiyoyin jini.
4. Ƙauracewa Shan Barasa/Giya
Shan barasa ko giya na kassara aikin ƙoda na wanke ko tace ruwan jiki da jini. Kuma shan barasa na da haɗarin kawo hawan jini da ciwon sugar.
5. Ƙauracewa Shan Magungunan Ciwon Jiki Jinsin NSAIDs
Magungunan kashe ciwon jiki kamar irin su diclofenac, ibuprofen, felden da sauransu. Saboda haka likitoci na kira da a gujewa shan irin wadannan magungunan barkatai saboda lahanin da suke iya yiwa koda, bayan cutar gyambon ciki (cutar ulcer) da yawan amfani da su na tsawon lokaci ke kawowa.
Har wa yau dai, hukumomin lafiya a Najeriya sun yi tsokaci a kan cewa shan magungunan gargajiya barkatai na kan gaba wajen janyo ciwon koda a Najeriya.
A maimakon hakan, tuntuɓi likita idan kana fama da ciwon jiki kamar ciwon baya, ciwon wuya, ciwon gwiwa da sauran ciwon jiki don kauce wa waɗancan matsalolin da muka ambata.
0 Comments