Illolin Cin Goro Ga Masu Hawan Jini Da Ciwon Olsa

 

Amfani da illolin goro

Goro yana ɗaya daga cikin ya'yan itace da ake amfani da su domin chi a sassan duniya baki ɗaya. Haka kuma, ba da kyautar goro alama ce ta karrama baƙo yayin bukukuwa da sauran taron al'adun Hausawa, kamar wurin daurin aure ko naɗin sarauta, musamman a al'adun arewacin Najeriya da sauran ƙasashen Afrika ta Yamma. Bugu da ƙari, ana amfani da goro a wasu abubuwan sha domin ƙarin ɗanɗano.

Goro na ɗauke da sinadarai da dama da ake alaƙanta su da amfani ga jiki kamar:

  1. Karin ƙarfi da kuzari: Maciya goro na amfani da shi domin wartsakewa, ƙara kuzari da karfin jiki.
  2. Maganin hana bacci ko kasala:  Sinadarin kafin (caffeine) da ya'yan goro ke É—auke da shi yana iya rage magagin bacci ko kasala. Mutane da yawa na amfani da goro ta wannan hanyar, musamman direbobin mota ida zasuyi tuÆ™in dare, ko ma'aikata masu aikin dare.
  3. Maganin tashin zuciya: Ana amfani da goro domin magance matsalar jin amai tashin zuciya.
  4. Rage sha'awar abinci: Cin goro yayin jin yunwa na da tasirin rage sha'awar cin abinci ko daƙushe jin matsananciyar yunwa.
  5. Rage raÉ—aÉ—in ciwon kai, musamman irin wanda ke kama É“arin kai, wato 'migraine headache' a turance.
  6. Kashe ƙwayoyin cutuka a jiki.
  7. Taimaka wa masu ciwon Asama (asthma) wajen buÉ—e hanyoyin numfashi 
  8. Da dai sauransu

Sai dai, duk da irin waÉ—annan amfani da bincike ke alaÆ™anta goro da shi, bincike ya nuna cewa; ana iya samun cutar wa ta hanyar wasu daga cikin wadannan sinadaran, idan ana yawan cin goro. 

Misali, goro na É—auke da sinadarin kafin (caffeine) kaso biyu zuwa uku cikin É—ari (2 – 3%). Bincike yai nuna cewa za'a iya samun hauhawar jini bayan cin goro sakamakon sinadarin kafin da ke cikin goro. Sai dai hauhawar jinin ya fi Æ™arfi ga masu cin goron a karon farko, ko kuma masu ci jifa-jifa. Haka nan, hauhawar jinin zuwa na wani É—an lokaci ne da sinadarin kafin É—in zai Æ™are a cikin jini, sai kuma hauhawar jinin ya sake daidaita.

Amma waÉ—anda suka shafe shekara da shekaru suna cin goron har goro ya zame musu jiki, jinin su kan jure tasirin sinadarin kafin É—in da ke cikin goro, sakamakon yawan amfani da goro yau da gobe. Don haka, tasirin sinadarin kafin a kan hawan jini na raguwa ne da tsawon lokacin da aka daÉ—e ana amfani da shi.

Har ila yau, wani binciken ya sake nuna cewa, ga masu hawan jini, amfani da goro yayin da suke kan magungunan hawan jini yana da tasirin daƙushe aikin maganin hawan jini, musamman jinsin maganin hawan jini da ke rufe ƙofar sinadarin calcium a jijiyoyin jini, wato 'calcium channel blockers' wadanda aikin su shi ne taimakawa wajen buɗa jijiyoyin jini.

Bugu da ƙari, wannan sinadarin kafin da ke cikin goro, yana ta da ciwon olsa (peptic ulcer disease) ga waɗanda ke da ita.

Bayan goro, ana samun sinadarin kafin a cikin kofi (coffee), lemukan roba/gwangwani kamar irin su fearless da dukkan energy drinks da baƙin shayi, har da ma wasu magungunan ciwon kai, mura, da kasala da ake saye a kasuwa.

Daga ƙarshe, mafi kyawun al'amari game da cin goro shi ne yin amfani da shi sannu-sannu. Saboda wannan dalili, zai fi kyau a yi amfani da goro yayin buƙata kaɗai, amma kada ya zama ɗabi'ar mutum kullum. Haka shima namijin goro bayanan sa ya gabata a wani rubutu.

Sannan ga masu hawan jini, saboda hauhawar jini da sinadarin kafin ke kawowa, da kuma daƙushe tasirin jinsin waɗancan maganin hawan jini da muka ambata a baya, zai fi kyau su ƙaurace wa chin goro, da sauran abubuwan da ke ɗauke da sindarin kafin.

Idan kana fama da hawan jini, tattauna da likitan ka kafin cin goro ko shan abubuwa masu sinadarin kafin don neman shawarwari.


Post a Comment

0 Comments