Matsalar kwacewar fitsari bayan ayyukan yunkuri ga mata

Maganin kwacewar fitsari

Shin ɗisowa ko ƙwacewar fitsari ce matsalarki ko matsalar ka?

Ɗisowar ko ƙwacewar fitsari ga maza da mata na daga cikin matsalolin da ke barazana ga ibadah, tsaftar jiki da kuma walwala.

Ɗisowa ko ƙwacewar fitsari musamman yayin ayyukan yunƙuri na nuni da raunin tsokokin shimfiɗar ƙugu a wajen riƙe bututun fitsari

Wannan matsalar tafi aukuwa ga mata saboda sun fi maza samun raunin tsokokin ƙashin ƙugu sanadiyyar samun ciki, nakuda da dai sauran su. Haku kuma bututun fitsarin mata ya na maza faɗi da kuma zama gajere.

Ayyukan yunƙuri da ke sanya fitsari ya ɗiso ko ya ƙwace wa mutum sun haɗa da: yin dariya, yin atishawa, yin hamma, yin tari, yin gudu ko yunƙurin ɗaga kayan nauyi.

Idan kana fama ko kina fama da ɗisowa ko ƙwacewar fitsari yayin waɗannan ayyukan da muka lissafa hakan na nuni da rauni ko rashin ƙwarin tsokokin shimfiɗar ƙugu.

Tsokokin shimfiɗar ƙugu suna ɗauke da tsokokin maɗaurin bututun fitsari (urinary sphincters). Saboda haka, raunin tsokokin shimfiɗar ƙugu na janyo tsokokin maɗaurin bututun fitsari su yi rauni.

Idan maɗaurin bututun fitsari ya yi rauni, hakan zai haddasa ɗisowa ko ƙwacewar fitsari yayin da aka takura jakar fitsari (bladder ) a lokacin yin ayyukan yunƙuri da aka ambata a sama.

Maganin kwacewar fitsari

Abubuwan da ke ƙara hadarin samun lalurar ɗisowar fitsari ƙwacewar fitsari sun haɗa da: goyon ciki, haihuwa, doguwar naƙuda, tangarɗar naƙuda, ƙiba ko taiɓa, matsanancin tari tsawon lokaci, buguwa ko rauni a ƙugu, matsalolin da ke biyo bayan tiyatar ƙugu da dai sauransu.

Idan kina ko kana da matsalar É—isowa ko Æ™wacewar fitsari, tuntuÉ“i likita a yau domin sanin yadda zaka yi maganin wannan lalurar 

Nassoshi 

1. Physiotherapy Hausa

Post a Comment

0 Comments