Matsalar Yawan Fitsari Ga Mace Mai Ciki

Yawan fitsari ga mai ciki


Yawan fitsari matsala ce da ke addabar mata masu ciki musamman waÉ—anda cikin su ya tsufa. Wannan lalurar ta yawan fitsari ga mai ciki ta na É—aya daga cikin abubuwan da ke sa mata masu tsohon ciki neman taimakon likita.

Meke kawo yawan fitsari ga mai ciki?

Akwai abubuwa da dama da ke iya musabbabin yawan fitsari ga mai ciki, amma za muyi tsokaci ga abubuwan da suka fi yawan kawo wannan lalurar ta yawan fitsari ga mata masu ciki.

1. Girman ciki

A lokacin da cikin mace ke girma, mahaifar mai ciki tana Æ™ara tasowa daga cikin marar ta zuwa cikin ciki, sakamakon Æ™ara girman jaririn da ke cikinta (fetus) da kuma Æ™arin ruwan faya (amniotic fluid). 

Wannan ƙarin girman mahaifa yana takura jakar ajiyar fitsari (urinary bladder) da kuma taushe ta. Wannan takura da tausa takan hanawa jakar fitsari iya riƙe kwatankwacin fitsarin da saba riƙewa kamin mace ta samu ciki.

Daga hakanan sai mai ciki ta ga yawan yin fitsarin ta kullum sai ƙaruwa yake, musamman idan cikin ya girma dayawa. Wannan kalar yawan fitsari ba ya da illah ga mai ciki, kima ba ya bukatar wani magani, daga zarar mace ta haihu za ta daina, fitsarin zai daidaita.

Yawan fitsari ga mai ciki


2. Cututtukan magudanan fitsari 

Mata masu ciki suna kan haÉ—arin samun cututtukan magudanan fitsari, saboda dalilai dayawa. Yawan fitsari ga mai ciki yana iya zama alamar farko da ke nuna kamuwa da cututtukan magudanan fitsari. 

Amma idan mace mai ciki ta kamu da cututtukan magudanan fitsari, takan samu wasu alamomi kamar jin zafi yayin fitsari, zazzaɓi, ciwon mara, zubar farin ruwa daga mafitsara tare da yawan jin fitsari.

Saboda haka idan har mace mai ciki ta luravda yawan yin fitsari da kuma wasu alamomi irin waÉ—anda muka ambata a sama sai ta garzaya asibiti domin ganin likita da gaggawa.

3. Ciwon sugar na masu ciki

Wasu mata masu ciki sukan samu ciwon sugar na wuccin gadi a lokacin da suke da cikin, wannan ciwon sugar yakan warke bayan mace ta haihu, amma kaÉ—an daga cikin matan da suka samu irin wannan ciwon sugar yakan ci gaba ya zama ciwon sugar na yau da kullum.

Yawan fitsari da irin wannan ciwon sugar yake kawowa shi ne, yana sanya mai ciki malala fitsari dayawa kuma mai kumfa da zaƙi, watarana ma sai aga kiyashi na bin fitsarin saboda zakin da yake da.

Mata masu ciwon sugar na masu ciki sukan haifi manyan yara, wadansu ma, ba zasu iya haihuwa da kansu ba sai anyi aiki an cire yaron.

Post a Comment

0 Comments