Yar uwa ko kina fama da ciwon ƙasan kafafu musamman da safe ko kuma a lokacin da cikin ki ya fara nauyi?
Ciwon "plantar fasciitis" rauni ne da ke samun rukunin tantanin halittun fata da ke shimfiɗe a ƙasan tafin kafafu. Wannan rukunin tantanin halittun yana aiki ne a matsayin "shock absorber", watau mai shanye shokin ko girgiza yayin tafiya ko gudu.
Wannan ciwon yana faruwa ne idan aka ɗame rukunin tantanin halittun fatar kafafu yayin tafiya ko gudu wanda hakan na iya kaiwa ga 'yar yagewa ko tsagewa da kumburi a cikin tafin kafafu, wanda ba za'a iya ganin sa ba, musamman a tushen kafau da suka taso daga ƙasan ƙashin dunduniya.
Ciwon tafin kafafu na plantar fascitis ya fi tsanani da safe yayin da aka fara tattakawa domin tafiya.
- Mutanen da ke da haÉ—arin samun wannan ciwo sun haÉ—a da:
- QMasu wasan tsere / masu gudu
- Mata masu juna biyu
- Masu shimfiÉ—aÉ—É—en tafin sawu (flat foot).
- Masu ƙiba / teɓa sosai.
- Masu sa takalmin choge ko takalman da ke da mashinfiÉ—i mai taushi ko tauri sosai.
- Wadanda suka samu sauyin salon rayuwar daga rashin motsa jiki zuwa motsa jiki da ya ƙunshi sassarfa ko gudu da dai sauransu.
Mene ne maganin ciwon tafin kafafu na plantar fascitis
Yayin da wannan ciwon ya dame ka ko ya dame ki, a nemi ƙanƙara a naɗe ta da zani ko tawul sai a ɗora a tafin sawu na tsawon mintuna 15 zuwa 20, sannan a cire. Wannan zai rage raɗaɗin ciwon. Sannan bayan an cire tafin sawun daga kan ƙanƙarar sai a garzaya asibiti domin gani likitan.
0 Comments