Gabatarwa:
Fitsarin kwance shi ne yin fitsari a lokacin bacci ba tare da sani ba bayan yaro ya wuce shekarun yin haka (shekaru bakwai). Mafi yawanci, yin fitsarin kwance kafin yaro ya cika shekaru bakwai ba matsala ba ce.
A lokacin da yaro ya cika shekaru bakwai ana tsammanin ya samu ingantaccen horon ƙwaƙwalwa da zai iya sarrafa uzurin fitsarin sa wanda zai bashi dama yayi fitsari a lokacin da ya ke buƙata kuma a wurin da ya kamata.
Yaushe ya kamata a ga likita idan yaro yana fitsarin kwance?
Mafi yawancin yara suna daina yin fitsarin kwance a lokacin da suke tsakanin shekaru biyar (5) zuwa shekaru bakwai (7). Wasu ƙalilan sukan daina yi kamin su kai shekara biyar, wasu kuma sukan wuce shekaru bakwai basu daina ba.
Akwai buƙatar iyayen yara su kai yaro asibiti domin ganin likita idan har:
- Yaro ya wuce shekaru bakwai (7) yana fitsarin kwance.
- Yaron da ya wuce shekaru biyar (5) ya dawo yana yin fitsarin kwance bayan yayi watanni da dainawa.
- Yaro yana fitsarin kwance tare da wasu alamu kamar jin ciwo yayin fitsari, yawan shan ruwa, yin fitsari mai duhu ko kalar ja, yawan hansari yayin bacci da dai sauransu
Abubuwan da ke kawo fitsarin kwance
Har ila wa yau babu wanda ya san tabbas haƙiƙanin abin da ke haifar da matsalar fitsarin kwance, amma masana sun tabbatar da abubuwa daban-daban waɗanda zamu ambata yanzu na iya taka rawa:
1. Karamar mafitsara
A cikin abubuwan da ake ɗorawa alhakin fitsarin kwance akwai ƙaramar mafitsara, idan yaro yana da ƙaramar mafitsara wannan yana nufin ba zai iya jure riƙe dukkanin fitsarin da ƙodar sa ke samar wa a cikin dare ba. Wannan yakan tilasta masa yin fitsari da dare domin zube fitsarin da ke cikin karamar mafitsarar.
2. Rashin iya gane mafitsara ta cika.
Wannan yana faruwa ne a lokacin da jakadun ƙwaƙwalwa masu sarrafa mafitsara suka samu jinkirin girma. Idan mafitsara ta cika da fitsari waɗannan jakadun su ke da alhakin aika saƙo zuwa ga ƙwaƙwalwa domin yaro yaji uzurin yin fitsari.
A lokacin da waɗannan jakadun suka samu jinkirin girma ba zasu iya aika isasshen signal zuwa ga ƙwaƙwalwa ba, saboda haka cikakken mafitsara bazai iya tayar da yaro daga bacci ba - musamman ma idan yaron ya kasance mai nauyin bacci.
3. Rashin daidaituwar sinadarin hormone na ADH
A lokacin ƙuruciya, wasu yara ba su samar da isasshen sinadarin hormone na anti-diuretic hormone (ADH). Wannan sinadarin hormone yana rage yawan fitsarin dare.
4. Ciwon magudanan fitsari
Kamuwa da wasu cututtukan fitsari na iya sa wa yaro wahalar sarrafa fitsari. Alamomin ciwon fitsari ga yara na iya haɗawa da fitsarin kwance, yawan fitsari, fitsari kalar ja ko ruwan ƙwai, jin zafi ko ciwo yayin fitsari da yawan kuka lokacin da yaro yake fitsari.
5. Cutar obstructive sleep apnea.
Wani lokaci fitsarin kwance alama ce ta cutar da ake kira Obstructive Sleep Apnea, wannan wata cuta ce da ke kawo sarƙewar numfashin yaro yayin da yake yin bacci. Mafi yawanci cutar tana faruwa ne saboda kumburi ko kara girman tonsils ko adenoids. Sauran alamun cutar na iya haɗawa da hansari yawan baccin rana da kuma yin bacci da baki buɗe.
6. Ciwon sugar
Ga yaron da baya yin fitsarin kwance a chan baya, fara yin fitsarin kwance kan iya zama alama ta farko da ciwon sugar zai nuna. Sauran alamomi na iya haɗawa da zubar da fitsari mai yawa a lokaci ɗaya, yawan jin ƙishirwa ko kuma yawan shan ruwa, yawan gajiya da rage nauyi duk da kyakkyawan cin abinci.
7. Dadewa ba tare da yin ban haya ba
Ana amfani da tsokoki iri É—aya don sarrafa fitsari da kuma ban haya. Rashin yin ban haya akai-akai ya kan iya sa waÉ—annan tsokoki suyi rauni, yin raunin waÉ—annan tsokoki yakan taimaka wajen raunin sarrafa fitsari da kuma yin fitsarin kwance yayin bacci.
8. Matsala a nervous system ko urinary system
Chan ba'a rasa ba, watarana matsalar fitsarin kwance tana samo asali ne daga matsala a ƙwaƙwalwar yaro ko kuma sashen fitsarin sa.
Yaran da ke kan haÉ—arin samun matsalar fitsarin kwance
Matsalar fitsarin kwance zata iya shafar kowa, amma ya fi shafuwar maza da ninki biyu sama da 'yan mata. Ana danganta abubuwa da yawa tare da ƙarin haɗarin fitsarin kwance, abubuwan sun haɗa da:
1. Gajiya da damuwa
Abubuwan da ke haddasa damuwa ga yaro - kamar zama babban É—a ko É—iya, fara sabuwar makaranta, ko yin bacci ba wurin da aka saba ba ko kuma idan yaro ya shiga wata damuwa - na iya sanya yaro yin fitsarin kwance.
2. Tarihin fitsarin kwance a cikin zuriya
Idan É—aya ko duka na iyayen yaro sun daÉ—e suna yin fitsarin kwance a lokacin da suke yara, toh É—ansu yana da babbar dama ta daÉ—ewa yana yin fitsarin kwance shi ma.
3. Yara masu cutar ADHD
Yara masu fama da cutar ADHD (attention deficit hyperactivity disorder) sunfi sauran yara samun matsalar fitsarin kwance.
Illolin fitsarin kwance
Ko da yake abin takaici ne, amma duk da haka yin fitsarin kwance baya haifar da wata illa ga lafiyar yaro idan har ana kula da tsarkake yaron da kuma makwancinsa a duk lokacin da yayi fitsarin.
Sai dai ga iyayen yaro fitsarin kwance kan iya zama matsala ko kuma wani abin takaici wanda zai iya haddasa musu damuwa ko kuma yayi tasiri akan zamantakewar su da sauran jama'a.
Haka zalika, idan yaro yakai wani mataki na mallakan hankalin kansa ba tare da ya daina fitsarin kwance ba, wannan na iya saka shi cikin halin damuwa kuma ya shafi mu'amalarsa da kuma dangantakar sa da mutane. Yakan iya fuskantar ƙalubale a cikin abokaninsa ko kuma a zamantakewar sa da sauran yara.
Bugu da ƙari, idan yaro mai fitsarin kwance baya samun kulawa da tsafta mai kyau, yawan fitsarin kwance kan iya haifar masa da ƙuraje a al'aurar sa da kewaye. Haka kuma zai kama warin fitsari a duk inda yake.
Kammalawa
A cikin wannan rubutu mun ga mene ne ake nufi da fitsarin kwance da abubuwan da ke kawo shi da kuma wasu daga cikin illolin fitsarin kwance. A rubutu na gaba da yardar Allah zamu ga hanyoyin da ake bi domin maganin fitsarin kwance a asibiti. Ku kasance tare damu.
Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3.
0 Comments