Shawarwari Zuwa Ga Iyaye Da Malamai Game Da Rataya Jakar Makaranta Ga Dalibai

Jakar Makarantar Yara


Mene ne nauyin jakar da ya kamata yaro ya riƙa ratayawa domin kiyaye ciwon jiki da lafiyar gadon bayan sa?

Wannan amsa na nan cikin shawarwari takwas da zamu ba da ga iyaye da malamai game da rataya jakar makaranta ga daliban ilmi.

Duk da muhimmancin jakar makaranta ga ɗalibi, kulawa da lafiyarsa ma tafi muhimmancin gaske. Sau dayawa, ƙorafe-ƙorafen yara 'yan makaranta kan matsananciyar gajiya, ciwon baya, wuya ko kafaɗu na da alaƙa da ɗabi'ar nan ta rataya babbar jakar makaranta maƙare da littafai, kayan rubutu, abin ci ko abin sha, wani lokacin ma har da sauran kayayyakin da ba a buƙata a makaranta.

Bugu da ƙari, bincike ya nuna yadda rataya jaka mai matuƙar nauyi ke sauya lafiyar numfashi saboda yadda nauyin jakar ke takura haƙarƙari da huhun yaro.

Hakanan, masana lafiyar ƙashin gadon baya sun ja hankalin iyaye da malamai cewa lafta wa yara jakankuna masu nauyin gaske na da gagarumar illah ga lafiyar yara. A cikin wannan rubutun za mu ba da shawarwari takwas domin kiyayewa, kamar haka;

Jakar Makarantar Yara

1. A tabbatar da cewa nauyin jakar da yaro zai ɗora a baya ba ta wuce kaso goma zuwa sha biyar cikin ɗari (10 - 15%) na nauyin yaro ba. Nauyin jakar baya da ya wuce kaso goma zuwa sha biyar cikin ɗari (10 - 15%) na nauyin yaro zai riƙa rinjayar yaro a lokacin da yake tafiya wanda hakan kan sa yaro durƙusawa ko sunkuyawa gaba domin kar nauyin jakar ya rinjaye shi.

Misali, idan nauyin yaro ya kai kilogram talatin (30Kg) a kan ma'aunin nauyi; to nauyin jakar da ya kamata yaron ya ɗinga ratayawa zai yi daidai ne da kilogram uku zuwa uku da rabi (3 - 3.5Kg) ko kasa da haka, amma kar ya taɓa wuce haka.

2. A yayin da aka rataya jakar baya, ba a son ta sauko ko ta zarce fiye da farkon ƙashin ƙugun yaro, ko kuma sama da maɗaurin zariya kaɗan.

3. A zaɓi jaka mai aljihuna, a sanya abin da ke da tsini ko kaifi a aljihu mafi nesa da gadon baya. Sannan a sanya kayan da ke da nauyi a aljihu mafi kusa da gadon baya.

4. Lafta wa yara littattafai a cikin jakar makarantar su ta ratayawa ba dole ba ne. Girman jakar makaranta fiye da ƙima kan sanya yara ɗaukar kayayyaki masu nauyi da ba a buƙatar su a makaranta.

5. A umarci yaro ya rataya maratayan jakar biyu a kafaɗun sa na hagu da dama kowane lokaci, domin sanya maratayin jakar a kafaɗa ɗaya kawai zai kawo rinjayar nauyin zuwa ɓari ɗaya na jikin yaro; wanda hakan kan kawo ciwon wuya, ciwon kafaɗa, ciwon baya da kuma tasgaɗewar ƙashin gadon baya idan ana yi yau da gobe.

Jakar Makarantar Yara

6. A zaɓi maratayin jaka mai faɗi kuma mai laushi, domin siririn maratayin jaka na iya nutsewa a cikin kafaɗa har ya ci wa yaro jiki.

7. A zaɓi jakar makaranta mai maratayan da za'a iya ƙarawa ko ragewa daidai da tsayin yaro. Domin maratayan jakar da ba za'a iya ragewa ba na iya kawo zarce wa ko taruwar nauyin jakar zuwa inda ba'a buƙatar sa a gadon baya.

8. Idan jakar makarantar yaro ta yi nauyi sosai, a shawarci malaman sa domin rage littattafan da za'a iya barin su a makaranta domin rage nauyin dakon littattafan daga gida zuwa makaranta kullum.

A yayin da yaro ya fara ƙorafin matsananciyar gajiya, ciwon baya, wuya ko kafaɗu, tuntuɓi likitan fisiyo domin neman shawarwari da kuma magance ƙorafe-ƙorafen.

Nassoshi 

1. Physiotherapy Hausa

Post a Comment

0 Comments