Cin zuma, wanda ake kira da yaren likitanci "dental flourosis" lalurar hakora ce da ke sauya launin hakora zuwa ruwan ƙasa-ƙasa.
Lalurar tana samun yara ne, musamman Æ´an kasa da shekara takwas, kamin hakoran girma na dim dim dim su fito masu.
Dalilin aukuwar cin zuma na da alaƙa da shan ruwa mai ɗauke da sinadarin flouride fiye da ƙima ko kuma wasu hanyoyi da yaran za su iya ci ko shan sinadarin "flouride" fiye da ƙima.
Sinadarin flouride ana amfani da shi wajen tsaftace ruwan sha, sai dai kasancewarsa fiye da ƙima a cikin ruwa na iya jefa ƴara cikin haɗarin samun cin zuma a hakoran su
Cin zuma lalurar haƙora ce da ke munana hasken hakoran kawai, amma ba ta da illah ga lafiyar hakoran, ma'ana ba ta da alaƙa da kawo ciwon hakori.
Manyan mutane waɗanda suka gama hakoran girma kuma ba su sha sinadarin flouride fiye da ƙima ba lokacin da hakoran su ke girma, to ba su da haɗarin kamuwa da cin zuma.
Lalurar cin zuma ba ta raunana hakora, a maimakon haka ma sai dai ta ƙarfafa hakoran. Saboda masu cin-zuma suna da ƙarin kariyar samun ramin haƙora.
Dalili kuwa shi ne sinadarin flouride na da muhimmanci ga lafiyar hakora. Kawai dai ba a so ya yi yawa ne fiye da ƙima lokacin girman ƴara domin kiyaye matsalar cin zuma.
Idan kana da yaro mai matsalar cin zuma ko kuma kana da damuwa kan launin hakoran ko kuma kana da ƙorafin ciwon hakori, tuntuɓi likitan hakori.
© Physiotherapy Hausa
0 Comments