Illolin Ciwon Sugar Ga Mace Mai Ciki: Shin Ciwon Sugar Na Hana Haihuwa?

Complications of diabetes in pregnancy

 

Assalam doctor ya aiki Allah ya ƙara basira, doctor ina da ciwon sugar ne (diabetes) to in nasami ciki sai ya lalace, to yanzu Bana samu din ma gaba daya. Doctor ko ciwon sugar diabetes hana Hana daukar ciki ?

Amma na karshen nan wani likita yace wai maganin da nake sha ne ya ke taba cikin wai allura ne ya kamata da ansamu ciki a koma yi. Don Allah ya abun yake?

Amsa 

Ciwon sugar yana iya yin mummunan tasiri sosai akan juna biyu ta hanyar haifar da Æ™alubale ga uwa da jaririnta. Idan ba'a kula da yawan sugar a cikin jini (blood sugar level) yadda ya kamata ba, to, hakan yana iya haÉ“aka haÉ—arin zubewar ciki (miscarriage), ko haihuwa kafin lokacin ta (preterm birth), da nakasar jariri (birth defects). 

Sugar mai yawa a cikin jini yana iya tasiri akan girman jariri, ta hanyar sanya jaririn ya zamo mai girma sosai fiye da Æ™ima (macrosomia), wanda zai iya haifar da matsaloli yayin haihuwa. 

A wajen uwa kuwa, tabbas ciwon sugar yana iya hana mace É—aukar ciki da kuma lalacewar cikin idan ta samu. Rashin kula da ciwon sugar yadda ya kamata yana iya Æ™ara tsananta wa mace yanayin hauhawar jininta wanda zai iya haifar mata da jijjiga (preeclampsia), ko matsalolin koda (kidney problems), ko matsalolin gani (vision problems). 

Haka kuma, zai iya shafar aikin mahaifarta, ta hanyar rage yawan iskar oxygen da abinci ga jariri. Bin shawarwarin likita, tare da auna yawan sugar a jini ga mai juna biyu da kuma ɗorata akan ka'idodin da suka dace na kula da ciwon sugar a lokacin juna biyu, yana da matuƙar muhimmanci don tabbatar da lafiyar cikinta da haihuwar ta lafiya.

Dangane da yin amfani da allurar insulin a lokacin da mace mai fama da ciwon sugar ta samu ciki, wannan haka ne, idan a chan baya tana amfani da magungunan ciwon sugar, toh idan ta samu ciki za ta daina shan magunguna ta koma yin allura. Dalili shi ne, mafi yawancin magungunan ciwon sugar suna kawo matsala ga lafiyar juna biyun.

Saboda haka, shawarar yin amfani da allurar insulin a gare ki ta dogara ne akan yanayin sugar ɗin ki da kuma matsayin lafiyar jikin ki gaba-daya. Idan har baki samu daukar ciki ba, ko kuma cikin yana lalacewa idan kika dauka, to, ya kamata ki nemi likitan da ya ƙware a wajen kula da ciwon sugar da haihuwa (endocrinologist ko obstetrician) don samun tsarin kula da ciwon sugar ɗin ki yadda ya kamata.

Post a Comment

0 Comments