Ire-iren Azzakari Da Sahihan Bayanai Akan Azzakarin Namiji

 Azzakarin Namiji

1. Ba abin damuwa ba ne idan azzakarin namiji ko ince mazakutar namiji ta zamanto a karkace ko tai lanƙwashe a gefen hagu ko dama, ko tai sama ko tayi curve ƙasa, hakan ba matsala ba ne. 

Hasali ma, binkicen masana a fannin saduwa ya nuna azzakarin namiji wanda yake a karkacen yafi taɓa sashin dake gigita mace da ƙara nishaɗin saduwa ga abokiyar tarayyar, abinda wasu kan kira da G-Spot. 

Karka yarda wani ɗan damfara yace ai yana da maganin miƙar da ita kawai saboda ta ɗan karkace, wannan ƙarya ne, zai cinye maka kuddi ne kawai. Munyi bayanin karkacewar ko lankwashewar azzakarin namiji kwattahilla, ayi searching rubutan a cikin wannan shafin.

2. Ba abin mamaki bane watarana don namiji ya samu kan sa azzakarin sa yayi sanyi, ta yadda ya kasa samun miƙewarta currr yadda ya saba, yanayi ko weather din gari na da tasiri a kan azzakarin namiji, musamman idan ana saduwa a ƙasan fankar sama sanda take juyawa da gudu. Don haka watarana wannan kan iya faruwa, ba matsala ba ne kar ayi gaggawa fara ɗeɓe-ɗeben maganin karfin maza

Kurum rashin miƙewar na fara zama matsala ne in hakan ya zarce tsawon wata shida, yana mai cigaba da faruwa ko yaushe, ta yadda sai anyi ta girgiza azzakarin namiji kamar wata tsohuwar tochila kafin ya miƙe, ko kuma azzakarin na yawan kwanciya bayan nasarar miƙewar sa ba tare da namiji ya kawo ruwan maniyyi ba, ko kuma ba tare da namiji ya daina sha'awar saduwa ba.

3. Ba'a yanke hukunci kan girma da tsayin azzakarin namiji, ta abin da ake iya gani da ido, musamman wanda bai taɓa aure ba ko wanda bai ma taɓa keɓewa da mace ba. Domin game da girma azzakarin namiji kala biyu ne; 

  • Akwai maza da azzakarin su baya kara girman tsayi a lokacin da sha'awar su ta motsa, sai dai ta ƙara ƙarfi ta cika, ta tsaya cak ba tare da ƙara tsayi ba har sai sun gama biyan buƙatar su sai ta kwanta.
  • Akwai kuma mazan da azzakarin su ya kan ƙara girma, tsayi, ya miƙe ya cika a duk lokacin da sha'awar su ta motsa, bayan sun biya buƙatar su sai ya koma kwantawa ya lahe kamar na wani ƙaramin yaro.

Waɗannan duka ba matsala bane, duk da cewa anfi samun maza masu yanayin azzakari na biyu.

Azzakarin namiji

4. Karamin azzakarin namiji ba ya nuna namiji  ba zai taɓa iya gamsar da mace a wajen saduwa ba, babban abin da ya dace kurum namiji yayi ƙoƙarin gane buƙatun matarsa a lokacin saduwa

Duk da cewa, wani lokaci ƙanƙancewar azzakarin namiji tare da rashin girma yana da dalili, domin daga cikin dalilan dake jawo haka akwai shaye-shaye! Saboda yadda tasirin sinadaran dattin dake cikin kayan maye, kamar irinsu tabar wiwi ke sanƙamar da jijiyoyin jinin azzakarin namiji in ya ɗau lokaci cikin harkar.

Sai kuma dalilin rashin amfani da azzakarin, wannan ma na rage masa tsawon centimeters 1 zuwa 2, kun ga ko 2cm ai da yawa yake. Azzakarin namiji yana ƙunshe da tsokoki ne, sannan ita tsoka tana ƙara girma ne a lokacin da ake yawan amfani da ita. Wannan shi yasa yan wasanni da yan dambe su kan yawaita yin atisaye domin ƙara girman tsokokin jikin su.

Anan rashin aure kenan yana taka rawa. Shi yasa in an sami dama ayi aure yafi, in ba hali toh a dinga cin abinci mai gina jiki tare da motsa jiki domin a sami sinadaran testosterone da nitric oxide su riƙa farkar da azzakarin (erection) akai-akai don dawwamar dashi a cikin ƙoshin lafiya. Wannan shi yasa galibi in kun farko da safe ku ke jin ta tsaye cak wannan abu ne mai kyau.

Mata ma na jin kansu a jiƙe duk da ba su yi komai ba, kurum suji danshi da santsi wannan ma normal ne tasirin sinadaran sex hormones ne, kuma suna ƙara nuna lafiyar mace.

5. Kamar yadda akan sami karayar ƙashi a hannu ko cinya ace sun karye, haka ma, tabbas azzakarin namiji yana karyewa shi ma! Duk da cewa tsoka ce me gautsi babu ƙashi a jikin azzakari amma kamar yadda in ka samu robar lemun kwalba irinsu Coca-Cola ka lanƙwasa ta za kaga wurin da ta karye yai wani fari yadda ko kaso ta miqe sak ba zata iya komawa daidai ba.

Toh shi ma azzakarin namiji haka karayar take. Abubuwan da kan iya kawo kariyar azzakarin sun haɗa da, faɗuwar abu mai nauyi kan azzakarin a yayin da yake tsaye cak bayan samun erection me ƙarfi, ko namiji ya cika sanya ƙarfi yayin artabun saduwa musamman irin salon nan na goho a shimfiɗa, ko ace abokiyar mu'amalar ita za ta koma sama tayi irin aikin namiji kai kuma namiji kana a ƙasa. 

Toh a irin wannan yanayi idan ta cika sa maka azzakari a cikin farji da ƙarfi ko sauri musamman in tanada nauyi sosai, zata iya ma illah ta karya maka zarmalulu. Kuma warakar ka sai an ji jiki don a shekara 2 ma ba lallai ka dawo aiki ba.

6. Sam babu wata matsala don 'yan daƙiƙu kaɗan bayan kayi kawowa ko inzali (releasing) kaji duk jikin ka ya saki, sha'awa ta tafi ko da ace baka so kawowa ba. Wannan ba matsala ba ne, Haka abin ya kamata ya kasance dama. Sai a jira wani ɗan lokaci kaɗan da ake kira refractory period da turanci, sannan sai abin ya ƙara tashi.

Azzakarin Namiji


Mene ne refractory period a yayin saduwa mace da namiji?

Wannan wani zango ne da kowanne namiji ko mace kan ɗauka kamin sha'awar saduwa ta koma dawo masa  bayan yayi zuwan kai ko inzali, watau kawowa (Releasing). Wato sai an jira wannan ɗan lokacin kamin a iya ɗaukar sabon chaji aji sabuwar sha'awa don komawa fagen daga. 

Sai dai shi wannan lokacin ya bambanta daga wani mutum zuwa wani mutum, wani mutum na iya jin sabuwar sha'awa ta taso masa ya koma bayan mintuna 15, ko mintuna 20, wani kuma sai bayan minti 30, 40, ko bayan awanni 2, ko huɗu 4 kamin ya iya komawa saduwa, kai wani ma shikenan sai gobe, wani kuma sai bayan kwana 3 ko sati sannan zai iya jin wata sabuwar sha'awa.

Wannan lokaci na refractory period yafi zama ƙanƙani ga samari da yan mata masu jini a jika sama da tsofaffi da mutane waɗanda suka fara manyanta. Amma komi ƙuruciyar mutum aƙalla sai an samu mintuna 15 shi ne mafi ƙarancin refractory period, wannan saduwar na novel ko ko irin saduwar da ake nunawa a finafinan batsa, yana kawowa ya koma juya ta duk ƙarya ne.

Ana dai iya kawowa aji azzakarin namiji ba ya kwanta ba amma duk da haka, ba za ya moru ba har sai ta koma default tukuna, idan mutum yayi ƙoƙarin cigaba da saduwa a irin wannan lokaci na refractory period toh zai dinga jin ciwo ne ko zafi a maimakon jin dadin saduwa. Sai dai idan sha'awar ta sake dawowa bayan shuɗewar refractory period toh, zango na biyu dama kan fi na farko tsayi.

8. Yanayin shigar abokiyar mu'amala/matarka ko sakin jikin ta da sakin fuskar ta yafi tasiri da amfani wajen ƙwazon da ɗa namiji zai samu yayin saduwa fiye da duk wani maganin matsi da take sha, galibi rashin shiga ko yin salo mai ɗaukar hankali, ko rashin wasannin motsa sha'awa kan sa namiji ya fuskanci rauni wajen saduwa. 

Yayin da kuma ya zaman a fusace namiji yake kamin ki aminta dashi, toh tausayin ki kan fice masa saboda ɓata masa rai da kika yi, hakan kan iya sa ya jima bai yi inzali ba, kukan ki ma ƙara masa ƙarfi yake, ƙarshe abu ya ƙara lalace muku ya barki da ɓacin rai da gashe-gashe, kizo ko yaushe ana mu'amala kina takaici kamar ki mutu. Don haka anaso a kasance cikin nishaɗi da jindaɗi kuma ayi saduwa domin soyayya, farantawa juna rai da jindaɗin kowa ba don kawai mutum ɗaya naso ayi ba.

Hoton azzakarin namiji

Yadda ake tsotse azzakarin namiji

09. Ga mata masu son tsotse azzakarin namiji ko kuma maza masu son matan su dinga totse musu azzakarin, akwai ɓangaren da yafi jin taɓi wato sensation a jikin halittar azzakarin namiji wanda yawan tsotsa gun kan sa namiji saurin inzali nan da nan. 

Don haka in anaso a ɗan jima ana shan azzakarin namiji to a kaucewa yawan tsotsa wannan sashin. Ɓangaren da yafi jin taɓin shi ne kan azzakari, saboda haka yawan tsotsa kan azzakarin namiji yana sa namiji ya cika miki baki taff da ruwan maniyyi nan take, amma ƙasan azzakarin ta daga layin da ya raba kan da gangar jiki har zuwa jakar ƴaƴan marina, a nan ne zaki himmatu wajen tsotsewa in baki so ya kawo da wuri.

Yadda ake shan azzakarin namiji

Miye amfanin shan ruwan maniyyin namiji ga mace?

10. Ba wata matsala ta lafiya a cikin haɗiye wa ko shan ruwan maniyyin namiji ga masu yin saduwa ta baki ko "oral sex". Matukar dai namijin ya kasance mai tsafta, kuma ba ya da ciwon sanyin mara ko mafitsara, baya fitar da farin ruwa mai wari, kuma ba yada abokan saduwa barkatai.

Sai dai kuma shan ruwan maniyyin namiji bai ƙarawa mace komai a jiki kamar yadda wasu ke zaton yana yi. Saboda kawai, ance ruwan maniyyi yana ƙunshe da sinadarai irin su; Calcium , Citrate, Fructose, Glucose, Protein da sauransu, adadin wannan sinadaran a cikin maniyyi baya da yawan da zai iya samar da wani muhimmin tasiri a jikin mace. 

A ƙalla kamin shan ruwan maniyyin namiji ya ba mace wani muhimmin abu a jiki sai ta sha ruwan maniyyi wanda ya kai 25 to 50 liters watau kwatankwacin wanda zai cika irin ƙatuwar baƙar jarka da masu kura ke turawa guda biyu, wanda ba abu ne mai yiwuwa ba. Haka kuma babu tabbacin yana gyara fuska don an shafa.

11. Adadin ruwan da kowanne namiji ke fitarwa yayin inzali ya bambanta tsakanin maza, wannan kuma ba matsala bane, ƙarancin ruwan da kake samarwa bashi ke nuna ba zaka iya yiwa mace ciki ba.

12. Hakanan kuma, ruwan maniyyin namiji ba yada ɗanɗano na bai ɗaya, kowa da kalar taste ɗin nasa, sau tari, ɗanɗanon ruwan maniyyi ya danganta da tsaftar mutum, abincin da yake ci, ko abin da yake sha. Domin abubuwa irinsu; tafarnuwa, albasa, coffee, kabeji, tabar sigari duk suna iya canja taste din ruwan maniyyin namiji.

13. Bugu da ƙari, a cikin ruwan maniyyin namiji akwai sinadarin melatonin dake sarrafa tsarin bacci, don haka duk da saduwa shi kansa motsa jiki ne amma wannan ruwan maniyyi daga namiji zuwa jikin mace saboda yana ɗauke da melatonin lokuta da yawa shi kesa gajiya a gareta bayan gama saduwa, ko in ta haɗiye sa.

14. Saduwa na mintuna 7 komi da komi, kamar yin wasannin motsa sha'awa mintuna 5, sanya azzakari a cikin farji mintuna 2 ba matsala ba ne, matukar kowa ya gamsu da juna shikenan, haka bai zama matsala. Duk saduwar nan na novel ko finafinan batsa (BF) ba fa gaskiya ba ne ina ƙara maimaitawa. 

Shin akwai maganin istimna'i ko masturbation na gaskiya?

Ku sani ƙarya ne babu wani abu wai maganin masturbation ko maganin istimna'i na gaskiya. Maganin istimna'i kawai shi ne ka ji tsoron Allah ka daina kurum in kaso dainawa, in kuma ka daina shikenan ba ka  buƙatar shan wani maganin komi, babu wani abu da ake buƙatar kasha, kai dai ka dage da motsa jiki da cin abinci mai kyau.

15. Yawan saduwa da namiji bai sa budewar gaban mace. Da yawa mutane kan yaɗa cewa yawan saduwa na sa mace buɗewa, amma sam wannan ba gaskiya ba ne, daga shekarun mace sai haihuwa su ne kaɗai ke tasiri wajen budewar gaban mace

16. Shan abarba bai ƙara wa mace zaƙin komai ko daɗi wajen saduwar aure, ko ya sa gaban mace irin ƙamshin abarba. Babu wani binkicen ilimi da ya tabbatar da hakan na faruwa.

17. Ba duk farin ruwa ne don an ga yana fita daga gaban mace ba za'a ce ciwon sanyin mara ko infection ba ne. Akwai lokuta da ruwa fari tas kan riƙa fita wanda yake healthy ne, akwai kuma zubar ruwan ni'ima da ke sa mace danshi da hana bushewar gaban mace, akwai kuma zubar ruwa mai yauƙi dake faruwa wanda yana cikin alamomin ovulation

Haka kuma, wani lokaci yayin saduwa za'a iya ganin farin ruwa mai kauri na fitowa duk gefe da gefe har ya jiƙa jikin azzakarin namijin kamar ya shafa farin cream ko kindirmo, wannan baya nuna vaginal infections, matuƙar ba ɗoyi sosai a kaji yana yi ba haɗe da jin zafi yayin saduwa.

18. Ba rashin tsafta ba ne don wani lokaci zuwa lokaci mace na jin gaban ta na ɗan yin hamami ko wari kaɗan, musamman idan mace ta san tana kula da tsaftace wurin daidai gwargwado. Haka kuma bayan gama jinin al'ada mace za ta iya jin gaban ta yana wani ƙarni kamar na jini, shi ma wannan ba matsala ba ne.

19. Maza ya dace ku san cewa ba'a taɓa iya ƙara tsayi ko kaurin azzakarin namiji. Don haka ku daina wahalar banza tare da asarar kuɗin ku a banza 'yan damfara na karbewa, galibi daga shekara 19  zuwa 21 shikenan tsayin azzakarin namiji ya kammala. Sai dai ma ya ƙanƙance amma ba dai ka ƙara ma sa girma ba. 

Da yawan mazaje kan dami kan su bisa jin ana cewa dole azzakarin namiji ya zamo ma girma kamin mace ta iya samun gamsuwa ta saduwa. Amma wannan ma ba gaskiya bane a haƙiƙanin magana, girman azzakari ba ya wajaba kamin mace ta gamsu da namiji. Galibi gamsuwar mace ya ta'allaka ne da ƙwarewar namiji wajen tattaɓa macen da kuma fahimtar abubuwan da take so ayi mata masu gigita mace yayin saduwa.

20. Jiƙa lemun tsami, kanwa ko jiƙa gishirin andir a sha bayan kammala saduwa, ko yin fitsari daga zarar an ƙare saduwa duk ba ya taɓa hana shigar ciki. Sai dai idan dama ba kwanakin shigar cikin ba ne, ko kuma ba'a dace da shigar ciki ba.

21. Wasu na cewa idan har namiji bai yi inzali a can cikin ƙarshen farjin mace ba dab da mahaifar ta wai ciki ba zai shiga ba. Amma wannan ba gaskiya ba ne, saboda tantanin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi suna da jela da suke amfani da ita suyi gudu zuwa cikin mahaifa a duk inda aka zuba su a farjin mace.

Post a Comment

0 Comments