Meke kawo shanyewar kafa bayan allura a duwawu?

Shanyewar kafa bayan allurar duwawu

Shanyewar ƙafa matsala ce da ke iya faruwa sakamakon lahani ga jijiyar laka da ake kira da 'sciatic nerve,' ita wannan jijiyar lakka ta sciatic nerve ita ce babbar jakadiyar ƙwaƙwalwa da ke kula da kafa, aikinta shi ne kai saƙonnin motsi daga ƙwaƙwalwa zuwa wasu tsokokin ƙafa da kuma karɓo saƙonnin taɓi daga fatar ƙafa zuwa ƙwaƙwalwa.

Wannan jijiyar lakka ta fito daga babbar lakka dake cikin ƙashin baya ne, sai ta biyo ta cikin ƙashin ƙugu sannan ta ratso ta cikin tsokokin duwawu a hanyarta ta zuwa ƙafa har tafin sawu.

Shanyewar kafa bayan allurar duwawu
Jijiyar lakkar sciatic nerve 

Wannan matsalar shanyewar kafa bayan anyi allurar duwawu yana faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura a kan jijiyar lakkar yayin allura a ɗuwawu, ko idan ruwan allurar ya taɓa jijiyar lakkar har ya tunzira jijiyar ta fara bijirewa ruwan alluran, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar lakar wanda hakan na iya danne ko shaƙe ta har aikinta ya samu cikas.

WaÉ—anda suke da haÉ—arin samun wannan matsalar shanyewar kafa bayan allurar duwawu sun haÉ—a da:

1) Yara ƙanana da mata masu fisge-fisge yayim da za'a yi musu allura, ko ma duk wanda bai bayar da haɗin kai ba yayin yin allura, musamman ƙananan yara da ma manyan masu tsoron allura.

2) Mai ƙaramin jiki ko rama sosai.

3) Faɗawa hannun wanda bai ƙware da yin allura ba.

4) Da kuma wanda tsautsayi ya faÉ—awa.

A lura cewa, daga cikin manyan matsalolin da ke sanya aukuwar shanyewar ƙafa bayan allura a duwawu, musamman ga yara ƙanana, akwai al'adar nan ta tsorata yara da yi musu allura idan suna rashin ji ko idan ana so su yi ko su bar wani abu.

Tsorata su da allura yana shiga tunaninsu cewa allura aba ce mai ciwo sosai. Saboda haka, duk lokacin da za a yi musu allura su ke tsorata har su fara fisge-fisge ba zasu taɓa bada haɗin kai ba. Wannan fisge-fisge da burususuwa ne kuma ke sa allura ta sauya hanyarta daga tsoka zuwa jijiyar lakka, ko kuma wanda zai yi alluran ya kauce hanya ya soka alluran akan jijiyar lakkar sciatic nerve.

Alamomin shanyewar kafa bayan allurar duwawu na bayyana ne a dukan rassan jijiyar lakkar a ƙafa nan take ko bayan wani ɗan lokaci.

Alamomin sun haÉ—a da:

1. Matsanancin ciwon kafa ga baki dayanta

2. Sagewa

3. Shanyewar tafin sawu

4. ÆŠaukewar tafin sawu zuwa sama

5. Bayyanar gurmanta bayan allura duwawu

6. Rauni ko rashin ƙwarin ƙafa

7. Rashin ji a fatar kafa idan aka taɓa

8. Wahalar tafiya da yin ɗingishi, jan ƙafa da sauransu.

Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, a gaggauta sanar da jami'in lafiyar da ya yi allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa sumul kamar ba a yi ba. Sai dai yin jinkirin zuwa asibiti na iya nakasa ƙafar ta shanye har abada.

Post a Comment

0 Comments