Meke kawo shanyewar tsintsiyar hannu? (Wrist drop)

 

Make kawo shanyewar tsintsiyar hannu

Shanyewar tsintsiyar hannu da ake cewa "wrist drop" a turance, matsala ce da ke faruwa sakamakon lahani ko rauni akan jijiyar lakka ta radial nerve (radial nerve palsy). Wannan jijiyar lakka ta radial nerve itace jakadiyar ƙwaƙwalwa da ke kai saƙo zuwa ga tsokoki masu kula da aikin ɗaga tafin hannu sama yayin da tafin hannun yake a kife. 

Yayin da wani rauni yayi wa jijiyar lakkar lahani ko ko yasa jijiyar ta tsinke, tsokokin ba za su iya karɓar umarnin aikin ɗaga hannu daga ƙwaƙwalwa ba. Saboda haka, gudanar da aikinsu na ɗaga tsintsiyar hannu ko tafin hannun a sama yayin da tafin hannun yake kife zai yi wahala.

Haka kuma hannun da raunin ya shafa yakan lanƙwashe ya kife a ƙasa saboda tsokokin da ke kula da kifar da hannun ƙasa sun rinjaye masu kula da ɗaga shi sama.

Shanyewar tsintsiyar hannu

Abubuwan da suke haddasa rauni akan jijiyar lakkar radial nerv sun haɗa da:

Karaya a tsakiyar damtse (saboda wannan jijiyar lakka ta biyo a wani koraro a tsakiyar damtse).

Lahani ko rauni sakamakon sara, suka ko yanka a wuya ko hannu.

Lahani ga jijiyar lakkar sakamakon kuskurewar allura a damtsen hannu.

Shaƙewar jijiyar lakar sakamakon ɗaurin karaya fiye da ƙima (wajen daurin gargajiya)

Ɗaure damatsa tamau da igiya tsawon lokaci na iya katse gudanar jini da kuma lahani ga wannan jijiyar lakka ta radial nerve.

Lahani ga tushen jijiyar lakar daga wuya sakamakon haɗuran ababen-hawa, faɗowa daga sama ko kuma raunukan ta'addanci.

Maƙalewar kafaɗar jariri a ƙugun mahaifiya yayin da aka samu tangarɗar naƙuda, wanda hakan na iya janyo lahani ga tushen jijiyar lakar a wuya. Wannan yafi faruwa ga yaran da ake haihuwa ba tare da suna kwance daidai a cikin ciki ba.

Shanyewar hannun jariri

Don haka, anan zanyi gargadi na musamman idan mace ta zo haihuwa aka ga hannun jariri ne ya fara fitowa maimakon kan sa, don Allah kar ayi kokarin yin wata dabara domin fitowa da jaririn ko kuma a ja hannun sa, waɗannan abubuwa ne da ke iya naƙasa jaririn har abada. A irin wannan yanayi abin da ya kamata ayi shi ne a tattara a ruga asibiti.

Shanyewar hannun jariri

Haka nan, masu larurar shanyewar ɓarin jiki kan iya samun wannan matsalar sakamakon shanyewar duka tsokokin hannu, sai dai, a wannan yanayin ba jijiyar lakar ce ke samun matsala ba face matsala ce daga ƙwaƙwalwa wadda ta shafi duka rabin jikin.

Likitan fisiyo na bin hanyoyin ƙwarewa na musamman domin yi wa jijiyar lakka ko tsokar da ta shanye atisaye da ƙara mata ƙaimi har ta dawo aiki yadda ya kamata.

Wannan matsala tana iya nakasa hannu, musamman idan ba a ɗauki matakin ganin likita a kan lokaci ba.

Post a Comment

0 Comments