Yadda ake kare majinyata daga samun kurajen kwanciya: Mu'ujiza daga Alƙur'ani

Kurajen kwanciya


Kurajen kwanciya, watau "pressure sore" ko kuma "bed sore" a turance, lahani ne ga fata zuwa tsoka sakamakon tsawaitar kwanciya, musamman a gadon baya, watau kwanciyar rigingine ko rairam. 

Kurajen kwanciya sun fi faruwa a sassan jiki da tudun ƙashi ya bayyana ko kuma inda ƙashi ya fi kusa da fata kamar bayan kwankwaso, bayan ƙeya, gwiwar hannu da dunduniya.

Tsawaitar kwanciya a kan sashe ko ɓangare ɗaya na jiki na sanya raguwar gudanar jini zuwa ga fatar da aka taushe. Raguwar gudanar jini da kuma nauyin kan sa tantanin halittun fata su fara mutuwa (necrosis) daga nan sai kuma fatar ta fashe. Idan matsalar ta ci gaba, kitsen ƙasan fata shi ma zai cinye har tsoka ta bayyana.

Idan ba'a shawo kan matsalar ba, a haka abin zai ci gaba da cinye tsokoki har ƙashi ya bayyana. Bayyanar ƙashi a fili na nuni da cewa ƙurji ko gyambon kwanciya ya kai matakin ƙarshe, watau mataki mafi tsanani.

Kurajen kwanciya suna samun majinyata ne da suka daɗe a kwance, musamman waɗanda ba sa iya juya jikin su da kan su, kamar majinyata da suke fama da ciwon sashe (stroke) ko kuma ciwon lakka.

Haka kuma, majinyata waɗanda ba sa cikin hayyacin su, masu fama da lalurorin ƙwalƙwalwa, su ma suna kan haɗarin samun kurajen kwanciya.

Meke kawo kurajen kwanciya

Sanadin kurajen kwanciya na da alaƙa da ƙaranci ko rashin gudanar jini a sashen jiki sakamakon matsi, nauyi ko kuma danniya daga kwanciya, kamar yadda dukan sassan jiki suka dogara da gudanar jini domin samun iskar oxygen da sinadarai.

Ƙaranci ko rashin gudanar jini a wani sashen jiki na 'yan sa'o'i zai sanya ƙwayoyin halittar jiki su fara mutuwa. Saboda haka ne, sai fata ta fara lalacewa har ta fara fashewa ko ma ta ruɓe.

Har wa yau, danshi a makwanci ko makwanci maras laushi ko tirjiya a makwanci na daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin samun kurajen kwanciya.

Fatar jiki ita ce garkuwar farko da ke fara yaƙar cututtuka a jikin ɗan Adam. Idan fata ta fashe, toh kamar kofar garkuwar jiki ta karye kenan, kowace irin ƙwayar cuta na iya shiga jiki cikin sauƙi ba tare da tirjiya ba. Saboda haka, bayan wahalar jinyar kurajen kwanciya, akwai mummunan haɗarin kamuwa daga ƙwayoyin cuta iri-iri daga kurajen kwanciya.

Sau da yawa, matsalar kamuwa da ƙwayoyin cuta daga kurajen kwanciya, ita ce ke lashe rayukan majinyata da suka daɗe suna jinya a kwance, saɓanin lalurar da ta fara kwantar da su.

Yadda ake kare majinyata daga samun kurajen kwanciya 

Kimiyyar lafiya ta bayyana hanyoyin kiyaye kamuwa daga kurajen kwanciya. Hanyoyin sun haɗa da: tsabtace jiki, kawar da danshi a makwancin mai jinya, amfani da katifar iska ga majinyata da ke dadewa a kwance da kuma jujjuya majinyaci duk bayan awa biyu. 

Wannan hikima ta jujjuya maras lafiya duk bayan awa biyu ita ce babbar hanyar da ake amfani da ita a asibiti domin kare majinyata daga samun kurajen kwanciya, hikimar ta bayyana ne a wajen karni na 20 a likitancin zamani.

Amma wannan hikima ta jujjuya majinyata da ke kwance, tuni Alƙur'ani Mai Tsarki ya yi bayanin ta kimanin shekara 1,400 da suka wuce.

A Suratul Kahfi da ke cikin juzu'i na 30, Allah Maɗaukakin sarki Ya ba da labarin mutanen kogo, waɗanda Allah ya sanya su yin bacci har na tsawon shekaru 309. A cikin wannan labarin Allah Maɗaukakin sarki Ya bayyyana wata hikima ta adana jikin su ba tare da sun lalace ba tsawon waɗannan shekarun da sukayi suna bacci.

A cikin Suratul Kahfi, a wani ɓangare na aya ta sha takwas (18), Allah ya ce:

 "وَنُـقَلِّبُهُمۡ ذَاتَ الۡيَمِيۡنِ وَ ذَاتَ الشِّمَالِ "

Ma'ana 

" ....kuma Munã jũjjaya su wajen dãma da wajen hagu,...."

Allah ya ce Shi Yake jujjuya su, saboda mai bacci yana jujjuyawa ba tare da sanin yadda ko a lokacin da yake juyawar ba. 

Duk da cewa Allah Mai Iko ne ya adana jikin su ba tare da jujjuya su ba. Amma saboda Ya nuna mana cewa jikin ɗan Adam ba zai zauna lafiya ƙalau a kwance diris har na tsawon lokaci ba tare da ana jujjuya shi ba.

Ta amfani da wannan hikima, likitoci da ma'aikatan jinya suke ba da shawarar jujjuya majinyaci duk bayan awa biyu, musamman wanda ke fama da lalurar da ba zai iya juya kansa ba.

Kammalawa 

Jujjuya majinyaci duk bayan awa biyu zuwa ɓangarorin jikin sa na hagu da na dama zai taimaka wajen:

  • Kiyaye kurajen kwanciya
  • Rage ciwon jiki da gaɓoɓi
  • Daskarewar jini a cikin jijiyoyin jini musamman jijiyoyin ƙafafu, da dai sauransu.

Daga ƙarshe, ga duk majinyacin da aka kwantar a asibiti, zai fi kyau ma'aikatan jinya ko yan'uwansa da ke jinyar sa a asibiti su kula da jujjuya shi, domin gujewa aukuwar waɗannan matsaloli.

Nassi: Physiotherapy Hausa.

Post a Comment

0 Comments