Yadda Cutar Tarin Fuka Ke Shaƙe Laka Da Shanye Kafafu

Cutar tarin Fuka ko tarin TB


Cutar tarin fuka ko kuma Tarin TB, ta fi kama huhu a jikin É—an adam. Sai dai, cutar na iya kama kowane sashin jiki. Hakanan, cutar tana kama Ć™ashin baya. Idan ta kama Ć™ashin baya, ana iya ganin wani baĆ™on Ć™aramin doro mai kama da Ć™usumbi ko tudu a tsakiyar Ć™ashin bayan. 

Mafi yawan lokuta wannan doro ya fi bayyana a saman baya, musamman tsakanin allon kafaɗu. Sai dai, yana iya bayyana a ƙasan baya a wasu lokutan.

Bayan bincike da gwaje-gwaje sun tabbatar da cewa wannan doro daga cutar tarin TB ne, ana ɗora majinyaci a kan magani domin yaƙar ƙwayoyin cutar bakteriya wacce ke haddasa cutar TB, watau Mycobacterium tuberculosis. Ana kuma warkewa daga tarin TBn garau ba tare da wata matsala ba.

Lalurar laka ita ce matsalar da ke biyon bayan cutar tarin TB wadda ta kama ƙashin baya ko da majinyaci ya warke daga harbin ƙwayoyin cutar bakteriyar.

Ɗaya ko fiye da ɗaya daga cikin jerin ƙasusuwan ƙashin baya na kumbura, wani lokacin ma ya karye ko ya rushe. Hakan na iya danne ko shaƙe laka da ke cikin kororon ƙashin baya.

Idan aka shaĆ™e ko danne laka kuwa, matsalolin da ke biyo baya sun haÉ—a da: 

  • Shanyewar Ć™afafu / raunin kafafu
  • ĆŠaukewa / gushewar jin taÉ“i ko ciwon a fatar Ć™afafu
  • Gaza riĆ™e fitsari da bayan gida 
  • Da kuma rirriĆ™ewar gaÉ“oÉ“in Ć™afa.
  • Mijirya ko dindiris a Ć™afafu.

Game da waɗannan matsalolin, likitoci na amfani da ƙwarewa domin ceto majinyaci daga samun naƙasa.

Domin a kullum muna zaton cewa kowane tari daga mura ko sanyi ne, amma abun ba haka yake ba! Sau da yawa, tari daga tarin fuka ko tarin TB ne, musamman idan ya haɗu da rama da yawan zufa a lokacin dare, amma sai mutune su zaci na mura ko sanyi ne, duk da cewa tarin fuka yana zuwa da ƙarin alamu kamar tari mara majina, ramewa, zazzabi, gumin dare da sauransu.

Sai dai, ba kasafai tarin fuka ke nuna duka alamomi  kai tsaye tun da farko ba. Alamar farko dai ita ce tari mara majina da ya Ć™i chi ya Ć™i chanyewa.

Haka kuma, ko da mutum bai yi tari ba kuma ya ga bayyanar wani doro, bulli ko tudu a ƙashin baya, a garzaya asibiti domin gane abinda ke faruwa.

Daga ƙarshe, domin guje wa cutar tarin TB, garzaya asibiti da zarar tari ya wuce sati biyu domin a binciken abinda ya kawo maka tarin. Kuma ga wani albishir, gwajin tarin TB kyauta ne.

© Physiotherapy Hausa