Abubuwan Da Ke Kawo Kumburin Ya'yan Maraina

Kumburin ya'yan maraina


Idan ya'yan marainan (testes) na yaro ko babban mutum suka kumbura, wannan na iya zama alamar wata matsalar lafiya. Ga wasu daga cikin dalilan da za su iya haifar da wannan kumburi:

1. Hydrocele (Gwaiwa)

Gwaiwa


Hydrocele ko kuma cutar gwaiwa tana faruwa ne idan ruwa ya taru a cikin jakar maraina (scrotum). Wannan matsala tana da yawa a jarirai maza kuma yawanci bata da haÉ—ari sosai, sai dai idan ta yi tsanani. Sai dai idan ba'a yi magani da sauri ba, ruwan zai cigaba da taruwa har jakar marina ta cika.

2. Inguinal Hernia

Wannan yana faruwa idan wani sashi na hanji ya shiga cikin jakar maraina (scrotum) ta hanyar da bai dace ba. Wannan matsala tana buƙatar kulawar likita.

3. Testicular Torsion (Murdewar ya'yan maraina)

Wannan na faruwa ne idan ya'yan marainan jariri, ko na yaro ko na babba ma suka murɗe. Murɗewar ya'yan maraina yana katse jini daga isa gare su. Wannan matsala ce mai tsananin ciwo da ke buƙatar kulawar gaggawa a asibiti, saboda za ta iya hanawa yaro haihuwa a nan gaba.

4. Epididymo-orchitis (Ciwon Infection Na Maraina)

Epididymitis ko orchitis suna iya haifar da kumburi, wanda yawanci yana tare da zazzabi ko ciwon ya'yan maraina. Yana iya zama saboda dalilan kamuwa da kwayoyin cutar bacteria ko virus, kamar wanda ke haifar da ciwon mumps (ciwon hangum).

5. Trauma Ga Ya'yan Maraina (Rauni)

Idan jaririn ko babban mutum ya samu rauni a wurin, wannan na iya jawo kumburi da ja a wurin ya'yan maraina.

6. Tumor (Kumburin Sankara ko Kansa):

Ko da yake yana da wuya a jarirai da ƙananan yara, kumburi a golaye na iya kasancewa alamar ciwon sanƙara.

Abin Da Ya Kamata Yi:

1. Kai Jariri ko Yaro Asibiti: Kumburi a ya'yan maraina matsala ce da ke buƙatar kulawar gaggawa daga likita, musamman idan akwai:

  1. Ciwo mai tsanani.
  2. Zazzabi.
  3. Wurin ya yi ja ko ya yi zafi.

2. A Guje Wasa da Wurin: Kada a dinga matsawa ko taɓa wurin don kada a ƙara tsananta matsalar.

3. Likita Zai Yi Gwaje-Gwaje: Ana iya buƙatar duba jaririn ta amfani da gwajin jini, gwajin fitsari, ko hoton ultrasound don gane ainihin abinda ya kawo matsalar.

Kammalawa

Wannan ba matsala ce da za a yi sakaci da ita ba, saboda wannan matsalar ta kan iya hana haihuwa a nan gaba. Likita ne kawai zai iya gano tushen matsalar da bada magani.


Rubutu Masu Alaqa

1. Ire-iren Azzakari Da Sahihan Bayanai Akan Azzakarin Namiji

2. Jarababben Namiji: Fadakarwa Akan Alamomin Rashin Lafiyar Namiji

3. Abubuwan 18 da ke kawo rashin haihuwa ga maza: 18 Common causes of male infertility in Nigeria

4. Alamomi, abubuwan dake haddasawa da kuma maganin saurin inzali (Premature ejaculation)

Post a Comment

0 Comments